Yadda ƴanbindiga suka kashe mutum 13 ƴangida ɗaya a Zamfara

Asalin hoton, Dauda Lawan/FB
Rundunar yansandan jihar Zamfara ta yi ƙarin haske kan kisan wasu mutum 13 ƴan gida ɗaya da ƴanbindiga suka yi a jihar a ƙarshen mako.
A ƙarshen mako ne wasu mahara suka auka wani gida a ƙauyen Gidan Taba da ke ƙaramar hukumar Maradun tare da kashe wani magidanci da duka iyalansa.
Lamarin mai matuƙar sosa zuciya, ya razana mazauna ƙauyen, waɗanda suka jima suna fuskantar barazanar hare-haren ƴanbindiga.
Ƴansandan sun ce lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare lokacin da mutane barci.
Ya lamarin ya faru?
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, DSP Yazid Abubakar ya shaida wa BBC cewa maharan sun shiga ƙauyen ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka zagaye gidan mutumin.
''Dama gidansa suka nufo, ba wani wuri ba, ba su da niyyar kai hari kan kowa, gidansa kawai suka nufo'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa bayan da maharan suka isa gidan mutumin sun kashe shi tare da duka iyalansa, sannan suka cinna masa wuta.
''Abin ya tayar da hankali, sun kashe shi tare da matansa da yaransa jimilla mutum 13, sannan suka ƙona su'' kamar yadda DSP Yazid ya bayyana cikin alhini.
Mutum nawa aka kashe?
Rahotonnin kafofin yaɗa labarai da dama sun ce mutum 12 ne suka mutu a lokacin harin.
To sai dai DSP Yazid ya ce adadin mutanen da aka kashe 13 ne.
'"Shi mutumin ne da sauran mutum 10 da suka haɗa da matansa da kuma ƴaƴansa'', in ji kakakin ƴansandan jihar.
Ya ƙara da cewa mutumin jajirtacen ɗan sa kai ne, wanda ya jima yana taimaka wa jami'an tsaro wajen yaƙi da ƴanbindiga a yankin.
Jami'in ƴansandan ya ce tuni aka yi jana'aizar duka mutanen da suka mutu.
Wane ɗauki jami'an tsaro suka kai?
DSP Yazid Abubakar ya ce a lokacin da ƴanbindigar ke kai harin jami'an ƴansanda sun samu rahoto kuma sun kai ɗauki.
''Sai dai kafin jami'anmu su isa ƙauyen, tuni ƴanbindigar sun tsere bayan aikata laifin'', in ji shi.
Ya ci gaba da da cewa yanzu haka rundunar ƴansandan jihar ta zuba jami'anta a ƙauyen domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al'ummar ƙauyen.
'Mutumin shi ne garkuwan ƙauyensu'
DSP Yazid Abubakar ya ce mutumin ya kasance garkuwa ga mutanen ƙauyensu daga hare-haren ƴanbindiga.
''Ɗan sa kai mai matuƙar ƙoƙari da ya shahara wajen aiki da jami'an tsaron a yaƙin da suka yi da ƴanbindiga a yankin'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa dama ƴanbindiga sun jima suna jin haushinsa, saboda yadda yake taimaka wa jami'an tsaro.
''Hakan ne ya sa suka fito musamman saboda sun jima suna jin haushinsa'', in ji DSP Yazid.
''Mutum ne jajirtacce da ke kare ƙauyensu daga hare-haren ƴanbindiga, hakan ne ma ya sa yanzu ƴanƙauyen nasu suka razana'', in ji shi.
To amma ya ce tuni rundunar yansandan jihar Zamfara suka samar da jami'an tsaron don taimaka wa kauyen da tsaro.

























