Ƴan fashin daji biyar da suka fi addabar arewacin Najeriya

Bindiga
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Yayin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu ke tunkarar ƙarshen wa'adi na farko, matsalar ƴan bindiga, wadda ta yi ƙamari a gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari, na ci gaba da addabar al'ummar arewa maso yammacin Najeriya.

Ƴan bindiga waɗanda suka shafe kimanin shekara 15 suna addabar jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Sokoto, Kebbi da Neja, na agrkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kisan mutane da kuma tarwatsa ƙauyuka.

Lamarin da ya jefa al'umma cikin garari da durƙusar da tattalin arziƙin al'ummar yankin, waɗanda akasarin su sun dogara ne a kan noma.

Dubban mutane sun rasa rayukansu, wasu sun rasa muhallansu, suna gudun hijira, yayin da har yanzu akwai ɗaruruwan mutane da ke hannun ƴan bindiga a wannan lokaci.

Duk da ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi na daƙile ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, wasu daga cikin manyan jagororinsu na ci gaba da zama barazana ga zaman lafiyar ƙasar.

A ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu an kashe da dama daga cikin shugabannin ƴan bindigar, sai dai duk da haka wasu na ci gaba da tasowa suna addabar yankunan, waɗanda yanzu haka wasu daga cikinsu na daga cikin waɗanda jami'an tsaron Najeriya ke nema ruwa-a-jallo.

Bincike kan ayyukan ƴanbindiga a Arewa maso Yamma ya nuna cewa akwai jagorori da dama da ke da nasu sansanonin da mayaƙa, yayin da wasu ke ƙulla ƙawance ko fafatawa da juna domin faɗaɗa ikonsu.

Mai bincike kan harkokin tsaro da rikicin ƴanbindiga, Yusuf Anka, ya ce fahimtar tarihin waɗannan shugabanni na taimakawa wajen fahimtar yadda matsalar ta samo asali da kuma yadda take ci gaba da canjawa.

"Wadannan mutane ba su fito lokaci guda ba. Kowane lokaci yana da shugabanninsa, kuma akwai alaka tsakanin tsoffin shugabanni da wadanda suka gaje su," in ji Yusuf Anka.

Ado Aleiro: Ɗan bindiga mai tasiri

A cewar Yusuf Anka, Ado Aleiro na ɗaya daga cikin fitattun shugabannin ƴanbindiga masu dogon tarihi a yankin.

"Ado Aleiro an haife shi ne a yankin Yankuzo da ke ƙaramar hukumar Tsafe. Ana hasashen ya haura shekara 50 a duniya," in ji shi.

Ya bayyana cewa ƙungiyar Aleiro tana da sansanoni a yankunan Tsafe kuma tana gudanar da hare-hare daga Tsafe zuwa Gusau, musamman a kan hanyar Gusau zuwa Funtua.

"Ayyukansu ba Zamfara kaɗai suka tsaya ba. Suna shiga yankunan Jibia da Ɗanmusa a Katsina, wato dukkan ƙananan hukumomi masu iyaka da Zamfara ne ayyukansu ke shafa."

Yusuf Anka ya ƙara da cewa Ado Aleiro ya yi suna ne a ƙarƙashin wani tsohon shugaban ƴanbindiga.

"Ya fara ne a ƙarƙashin Hassan Ɗan Tawaye, wanda shi ma ya taso ƙarƙashin Buhari Daji. A yau ana kallon Ado Aleiro a matsayin ɗaya daga cikin manyan shugabannin da suka fi tasiri a yankin."

Bello Turji: Sunan da ya fi ɗaukar hankali

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga cikin shugabannin da suka fi jan hankali a shekarun nan a yanzu a harkar ƴanbindiga akwai Bello Turji.

A cewar Yusuf Anka, "Bello Turji matashi ne da aka haifa a ƙauyen Fakai da ke ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara."

Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa Turji bai samu ilimin boko ko na addini sosai ba, kuma ya taso ne cikin rayuwar Fulani ta noma da kiwo.

"Turji ya fito ne a mataki na uku na ƴanbindiga. Kafin zuwansa akwai zamanin su Buharin Daji, sannan akwai zamanin su Halilu Sububu, kafin a zo zamaninsu na yanzu."

A cewarsa, sansanonin Turji na yankin Shinkafi ne, amma tasirinsa ya wuce iyakokin Zamfara.

"Dabarsa tana kai hare-hare a Sabon Birni da Isa a jihar Sokoto, sannan suna tsallakawa zuwa Jamhuriyar Nijar."

Dangane da ayyukan da suke yi a Nijar, Yusuf Anka ya ce: "Abin da suke yi a Najeriya kusan shi suke yi a Nijar. Akwai satar mutane domin neman kuɗin fansa, kai hare-hare kan jami'an tsaro da sauran ayyukan ta'addanci."

Dogo Giɗe: Wanda ya fi hulɗa da ƙungiyoyin jihadi

Dogo Giɗe na daga cikin sunayen da jami'an tsaro da masu bincike suka fi mayar da hankali a kansa.

Sai dai har yanzu akwai saɓani kan asalin inda ya fito. "Wasu suna cewa ɗan asalin Faskari ne a Katsina, wasu kuma suna cewa ɗan Maru ne a Zamfara," in ji Yusuf Anka.

Ya ce Dogo Giɗe na cikin mutanen farko da tsohon jagoran ƴanbindiga Buhari Daji ya ba makamai.

Yusuf Anka ya ce daga baya Dogo Giɗe ya ware baya kashe Buhari Daji, sannan ya fara gina dabarsa.

"Saboda ƙarfinsa ya sa ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi suka fara neman alaƙa da shi," in ji Anka.

Mai binciken ya ƙara da cewa ƙungiyar Ansaru ce ta fara tuntubarsa. "Shi kansa yana iƙirarin babu ƙungiyar jihadi da bai taɓa mu'amala da ita ba."

A cewarsa, wasu masana tsaro na ganin irin waɗannan alaƙa ne suka ƙara masa ƙarfi da tasiri a yankin.

A yanzu, Yusuf Anka ya ce Dogo Giɗe ya koma yankin jihar Neja da zama.

Mati Sububu: Magajin Halilu Sububu

Bayan mutuwar Halilu Sububu, wani daga cikin fitattun shugabannin ƴanbindiga a Arewa maso Yamma, sai hankali ya koma kan magajinsa.

"Wasu suna cewa Mati Sububu ƙani ne ga Halilu Sububu, wasu kuma suna cewa ɗan uwansa ne kawai," in ji Yusuf Anka.

Ya bayyana Halilu Sububu a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da suka fi tara makamai da dukiya kafin mutuwarsa.

"Kafin rasuwarsa, mutane da dama suna kallonsa a matsayin wanda ya fi tasiri da iko a yankin."

Bayan rasuwar Halilu, Yusuf Anka ya ce Mati ne ya karɓi ragamar dabar. "A yau shi ne ke jagorantar hare-hare a yankin Anka, har ma suna shiga wasu yankuna na Jihar Kebbi."

Ya ƙara da cewa dabar ta fara karkata zuwa harkokin haƙar ma'adanai tun kafin rasuwar Halilu.

"Bayan mutuwarsa, Mati ya ci gaba da amfani da ƙarfi wajen sarrafa wuraren haƙar ma'adinai, duk da cewa har yanzu suna ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna," in ji Anka.

Gwaska Ɗan Ƙarami: Matashin da ya gaji mahaifinsa

Wani sunan da ke cikin jerin shugabannin da suka fi tasiri a yanzu akwai Gwaska Ɗan Ƙarami.

A cewar Yusuf Anka, asalinsa ya sha bamban da mafi yawan shugabannin ƴanbindiga.

"Bincike ya nuna cewa iyayensa da kakanninsa ba Fulani ba ne. Wasu na cewa Gobirawa ne, wasu kuma na cewa Hausawa ne."

Ya ce mahaifinsa, Alhaji Kundu, shi ma ɗanbindiga ne wanda ya yi aiki tare da Buhari Daji.

"Daga baya jami'an tsaro suka kashe shi a yankin Dumburum da ke ƙaramar hukumar Zurmi."

Yusuf Anka ya ce bayan mutuwar mahaifinsa ne Gwaska ya karɓi ragamar jagorancin dabar.

Sai dai ya ce Gwaska na fama da saɓani mai tsanani da wasu shugabannin ƴanbindiga.

"Akwai rikici tsakaninsa da Bello Turji. Wasu suna danganta hakan da bambancin ƙabila, wasu kuma suna ganin rikici ne na neman iko da sarrafa albarkatu kamar yadda aka sabi gani a tsakanin ƴanbindiga."

A cewar Yusuf Anka, abin da ya fi ɗaukar hankali a yanzu shi ne yadda wasu ƙungiyoyin ƴanbindiga suka fara karkata daga dogaro da kuɗin fansa kawai zuwa haƙar albarkatun ƙasa, musamman zinare da sauran ma'adanai.

Abubuwan da suka sa aka kasa magance matsalar

Wani rahoto da kamfanin nazari kan harkar tsaro a yankin Sahel na Afirka, Beacon Security and Intelligence Limited ya fitar a watan Yunin 2026 ya yi gargaɗi tare da nuna ƙaruwar matsalolin tsaro a Najeriya musamman a jihohin Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi.

Rahoton ya nuna cewa abubuwa ne da dama ke janyo ƙaruwar matsalar ta tsaro a waɗanann jihohi, kamar yadda shugaban kamfanin Kabiru Adamu ya ƙara bayani.

Ya bayyana abubuwan da nazari ya nuna cewa su ne suka sanya aka gaza magance matsalar:

Rashin haɗin kai:

Sau da dama masana tsaro sun sha nanata cewa haɗin kai tsakanin waɗannan jihohi a ƙoƙarin magance matsalar zai taka rawa sosai, kasancewar ƴan fashin na zirga-zirga ne tsakanin jihohi.

A tattaunawarsa da BBC, Kabiru Adamu ya ce "Abin da ke da ban mamaki shi ne yadda babu wata alaƙa mai ƙarfi tsakanin gwamnonin nan.''

Rashin mayar da hankali:

A lokuta da dama an sha zargin hukumomi da mayar da hankali kan yaƙi da matsalar, kasancewa ana ganin ƴan bindigar suna zirga-zirgar su a cikin daji ba tare da wani tarnaƙi ba.

Adamu ya ce ''ƴanbindigan nan suna da dama ta walwala har dai a kan babura, daga wuri zuwa wuri, babu mataki guda ɗaya tilo wanda aka ɗauka na mamaye dazukan, a hana ƴanbindigan walwala".

Iyaka da ƙasashen ƙetare:

Najeriya na iyaka mai tsawo da Jamhuriyar Nijar wadda ta kai tsawon kilomita 1,497, kuma jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara duk suna daga cikin wadanda ke kan wannan iyaka.

Kabiru Adamu ya ce wata matsalar da ke yin tarnaƙi ga samar da tsaron shi ne: "jihohin nan duka suna da iyaka da kasashen waje har dai ma kasar Nijar".

Me ya kamata a yi?

Dangane da abin ya kamata a yi a jihohin, Dakta Adamu ya ce, sun dade suna ba gwamnonin jihohin shawara kan abubuwan da ya kamata su yi amma ba a yi.

''To amma yanzu abin ya kai lokacin da buƙatar mu fito fili mu ƙara magana saboda burin da muke da shi na ƙoƙarin taimaka wa jihohin nan''.

''Har kullum abin da muke kara jaddadawa shi ne samun hadin kai tsakanin gwamnonin nan ta yadda jama'a waɗanda ake mulka za su ga tasirin abin da suke yi musamman a kan harkar tsaro,'' in ji shi.