Chelsea na harin Boubacar Kamara, Liverpool na son Ronald Araujo

Asalin hoton, Getty Image
Chelsea, da Inter Milan da Al-Hilal na zawarcin ɗan wasan Aston Villa Boubacar Kamara, bayan da ya koma taka leda daga raunin da ya samu. (Fussball News - in German)
Liverpool da ɗan wasan aro ɗan Uruguay Ronald Araujo na shirin jiran zuwa ƙarshen kaka wasanni, sannan ya yanke shawararsa na komawa Barcelona a matsayin ɗan wasa na Din-din-din, kan fam miliyan 47. (Sport - in Spanish)
Manchester United za ta iya biyan maƙuden kuɗaɗe wajen ɗauko ɗan wasan Nottingham Forest Murillo, a kakkar wasanni. (Football Insider)
Idan Manchester United ta sallami Michael Carrick,akwai yiwuwar tsohon mai horar da Newcastle United Eddie Howe, da takwaransa da ya horarar da ƴan wasan Bayern Munich, sai kuma RB Leipzig Julian Nagelsmann, na daga cikin mutum biyun farko da za su iya maye gurbinsa. (Manchester Evening News)
Sai dai kuma , mai horar da ƴan wasan Amurka Mauricio Pochettino, da ya taba kula da Tottenham da Chelsea, shi ne wanda ake ganin ka iya zama sabo mai horar da yan wasan kungiyar. (Standard)
Brentford, da Chelsea, da Manchester City, da Newcastle United da Tottenham na cikin ƙungiyoyin da ke bibiyar ɗan wasn Faransa Ismaelo Ganiou, da ke taka leda a Lens. (Teamtalk)
Everton sun shiga gaban Sunderland da Coventry City waje siyen Abdoulaye Doumbia daga BK Hacken. (Football Insider)
Liverpool, da Manchester United da Chelsea na kan gaba wajen bibiyar ɗan wasan AC Milan Koni de Winter. (Caught Offside)
Everton na harin Kelvin Yeboah - wato da ga tsohon ɗan wasan Leeds United Tony, kuna sun akan kamala shiga yarjejejniya a watan Janairu, bayan da ɗan wasan ya zura ƙollaye 18 a wasanni 32 da ya baugawa ƙungiyarsa ta Minnesota United. (The Hard Tackle)
Sai dai Crystal Palace da Ipswich Town za su shiga zawarcin Yeboah tare da Everton. (Football Insider)
Everton, da Chelsea, da Manchester United da Tottenham sun tuntuɓi wakilan tsohon ɗan wasan Barcelona Vitor Roque, inda farashin ɗan wasan ya kai fam miliyan 42 a wajen Palmeiras. (Bolavip via Teamtalk)
Manchester United ta tunkari ɗan wasan Manchester City Rayan Ait-Nouri, a kakar wasanni, a yunƙurinsu na ɗuko dan asalin Algeriyar a watan Janairu. (Football Insider)



























