Dalilan da ke haddasa katsewar wutar lantarki a Najeriya?

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ɗora alhakin yawan katsewar lantarki da ake fama da ita a wasu sassan ƙasar kan aikin gyaran da ake yi a tashar samar da wutar lantarki ta Egbin, da ƙarancin gas, da kuma lalata layukan wutar lantarki da ake yi.
Tashar samar da wutar lantarki ta Egbin ita ce mafi girma a Najeriya cikin tashoshin da ke amfani da iskar gas wajen samar da lantarki, kuma tana samar da kusan kashi 16 cikin 100 na wutar da ake rarraba wa a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya fitar a ranar Asabar, ya ce: "Ina sane da cewa ana samun katsewar lantarki a halin yanzu kuma ta jefa iyalai da 'yan kasuwa cikin matsi a jihohi huɗu da abin ya shafa, ciki har da Legas da Babban Birnin Tarayya, Abuja."
Sai dai ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za a samu ingancin samar da lantarkin nan da sa'o'i 48 zuwa 72 masu zuwa, inda gwamnati ta fara ɗaukar matakan magance matsalolin da suka haddasa katsewar wutar.
Haka kuma "muna aiki tare da masu ruwa da tsakki a harkar makamashi domin inganta samar da iskar gas da kuma hanzarta gyaran kayayyakin da suka lalace."
Me ke haddasa katsewar lantarki a Najeriya?

Asalin hoton, Joseph Tegbe/X
Wasu sassan Legas sun shafe makonni ba tare da samun lantarki ba, yayin da mutanen da ke samun wutar ma ke cewa an samu raguwar yadda suke samun ta.
Hakan ya sa 'yan Najeriya suka fara tambayar abin da ke haddasa matsalar katsewar lantarkin, musamman yayin da tsananin zafi ke ƙara tsananta.
Sai dai ministan wutar lantarki ya ce sauran abubuwan da suka jawo matsalar sun haɗa da ƙarancin iskar gas da ake bai wa wasu tashoshin samar da lantarki da ke amfani da ita, lamarin da ya rage yawan wutar da ake rarrabawa a ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya kuma ce lalata layukan wutar lantarki ne ya haddasa raguwar samar da lantarki a wasu yankuna, musamman a Legas.
Tegbe ya ce ma'aikatarsa na aiki domin mayar da na'urorin samar da lantarkin da abin ya shafa tare da inganta samar da iskar gas ga tashoshin lantarki.
A ranar 4 ga Nuwamba, ministan wutar lantarki ya umarci Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) da Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki Mai Zaman Kanta ta Najeriya (NISO) da kamfanonin rarraba lantarki (DisCos) da su magance matsalolin aiki da suke haddasa raguwar samar da lantarki da ake gani a baya-bayan nan.
A wata sanarwa, NISO ta danganta matsalar ƙarancin lantarkin sakamakon ƙarancin iskar gas da ake bai wa tashoshin lantarki masu amfani da ita, da kuma raguwar ruwan da ke shiga madatsun ruwa da ake amfani da su wajen samar da lantarki.
"Karancin iskar gas ya rage ƙarfin wasu tashoshin lantarki masu amfani da ita wajen samar da wuta, yayin da ƙarancin ruwa a madatsun ruwa kuma ya shafi yawan wutar da tashoshin samar da lantarki ta ruwa za su iya samarwa.
Shi ma kamfanin TCN ya yi tsokaci kan matsalar bayan ɗaya daga cikin kamfanonin rarraba lantarki ya ɗora alhakin katsewar lantarki a kansa.
A ranar Juma'a, kamfanin ya ce zargin da Ikeja Electric (IKEDC) ya yi cewa "matsalar rashin daidaiton tsarin rabon lantarki" ce ta haddasa wasu daga cikin katsewar wutar da aka samu kwanan nan ba daidai ba ne.
TCN ya ce NISO ce kawai ke da hurumin bayyana ainihin musabbabin matsalolin da suka shafi babban tsarin lantarki na ƙasa, kuma tuni NISO ta bayyana cewa manyan matsalolin sun haɗa da ƙarancin iskar gas ga wasu tashoshin samar da lantarki da kuma ƙarancin ruwa a madatsun samar da lantarki ta ruwa.
Saboda haka ta shawarci IKEDC da sauran kamfanonin rarraba lantarki da su rika amfani da ingantattun bayanai daga NISO yayin bayyana matsalolin samar da lantarki ga kwastomominsu.
Abin da gwamnati ta ce ta yi kan matsalar lantarki a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta ce ta ɗauki matakai da dama domin magance matsalolin da suka addabi fannin lantarki a ƙasar.
Daya daga cikin matakan shi ne sanya hannu kan Dokar Lantarki ta 2023 a ranar 9 ga watan Yuni. Dokar ta bai wa jihohi da sauran ƙananan hukumomin gwamnati damar shiga harkar samarwa, rarrabawa da kuma sufurin lantarki, bayan an cire fannin daga jerin abubuwan da gwamnatin tarayya kaɗai ke da ikon gudanarwa.
Jihohin Legas da Enugu da Abia da Ekiti da Oyo da Kaduna da Neja na daga cikin waɗanda suka fara cin gajiyar wannan sauyi.
Gwamnatin ta kuma ce Shugaba Bola Tinubu ya gaji bashin da ya haura tiriliyan shida da aka tara tsakanin shekarun 2015 zuwa 2025 a fannin lantarki.
Haka kuma ta ƙaddamar da Shirin Samar da Mita domin magance rashin mita da ya haura mutum miliyan bakwai a faɗin ƙasar.
Ministan albarkatun ƙasa da ma'adinai, Dele Alake, ya ce a cikin shekara uku da suka gabata an samar wa fiye da kwastomomi miliyan 1.5 mita ta hanyar shirin.
Kazalika, Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara ta ce ta haɗa wa jami'o'i da asibitoci da kuma al'ummomin karkara tsarin samar da lantarki ta hasken rana.
Gwamnatin ta kuma samar da shirin lamuni na naira tiriliyan huɗu domin biyan basussukan da aka tantance na kamfanonin samar da lantarki 21 da kuma kamfanonin samar da iskar gas.
Ta ce har yanzu tana ci gaba da gyaran fannin lantarki da kuma fannin samar da wuta, tana mai jaddada cewa Shugaba Tinubu bai ja da baya daga alƙawarinsa na inganta harkar lantarki ba.
Sai dai duk da waɗannan matakai, 'yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsaloli wajen samun lantarki.
A wasu jihohi da yankuna ana samun lantarki fiye da wasu, yayin da wasu wuraren ke fama da ƙarancin wuta ko rashin wutar gaba ɗaya.



























