Yadda za ku kare kanku daga ƴan damfara a intanet

.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Yayin da sabbin masu amfani da internet waɗanda ba su da ƙwarewa ke ƙaruwa a duniya, ko waɗanne hanyoyi za su bi wajen kare kansu daga ƴan damfara?

A shekarar 2022, Anicet Etekpo wani jami'in tsaro a ƙasar Benin ya karbi gayyatar abota da wani ya aika masa ta shafin facebook .

"Lamarin da ya shigar da ni wani shafin internet na bogi inda aka buƙaci in shigar da bayanan asusun ajiyata na banki'' kamar yadda ya shaidawa BBC.

Etekpo ya yi asarar makudan kuɗaɗe daga yana ya fara damuwa game da tsaron bayanan sirrinsa.

A lokacin da lamarin ya faru, shekaru kaɗan ne kawai ya kwashe yana amfani da intanet. Yayin da damar amfani da intanet ke ci gaba da yaɗuwa a yankuna irin su Afirka ta Yamma, miliyoyin mutane za su fara fuskantar irin haɗurran da ke tattare da amfani da intanet, kamar waɗanda Etekpo ya fuskanta. To, ta yaya za a kare bayanan sirri?

An kiyasta cewa mutane biliyan 2.6, wato kusan kashi ɗaya bisa uku na al'ummar duniya, har yanzu ba su da damar amfani da intanet. Idan aka ci gaba da faɗaɗa damar amfani da intanet a irin wannan yanayai, ana sa ran ƙarin mutane kusan biliyan biyu za su samu damar fara amfani da intanet nan da shekara ta 2030.

Ga yawancin sabbin masu amfani da intanet, hakan na nufin za su fara fuskantar abubuwa kamar saƙonnin marrassa amfani watau (spam) da manhajoji masu cutarwa da ke neman kuɗin fansa kafin a dawo da bayanan da aka kulle (ransomware) da kuma shafukan internet na bogi da aka ƙirƙira domin yaudarar mutane.

Wannan yanayi na samarwa masu aikata laifukan intanet sabbin damarmaki na samun kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya, lamarin da za a iya bayyana shi da cewa "tsarin tara dukiya ta hanyar aikata laifukan intanet".

Sai dai matakan da aka tsara domin kare sabbin masu amfani da intanet tun daga horas da su kan yadda za su yi amfani da fasahar zamani cikin aminci zuwa matakan kariya daga ƴan damfara na da wahalar fahimta ga sabbin masu amfani da internet.

"Wani sabon tsarin aikata laifukan intanet ne ke kunno kai," in ji Zeki Turedi, babban jami'in fasaha na kamfanin CrowdStrike wanda ya ƙware a fannin tsaron intanet da kuma bibiyar masu satar bayanai.

"Ko da yake babban abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne taimakawa kamfanoni waɗannan matakan kariya suna da tasiri mai kyau ga ɗaiɗaikun mutane.

.
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu aikata laifukan intanet na amfani da fasahohin sarrafa bayanai na kai tsaye da kuma amfani da ƙirƙirarriyar basira watau (AI), da kuma dabarun amfani da tunanin ɗan Adam wajen yaudarar mutane.

Sai dai Turedi ya ce, ga mutanen da ke fuskantar irin waɗannan barazanar a karon farko, sauye-sauyen da ake samu a duniyar intanet na iya ƙara wahalar gano irin waɗannan barazanar.

"A gefe guda sabon mai amfani da intanet a yanzu yana samun damar bayanai, ayyuka da damarmaki waɗanda za su iya sauya rayuwarsa.

A halin yanzu, masu aikata laifukan intanet na iya ƙirƙirar saƙonnin damfara da suka dace da al'adu ko harshen yankin da suke son kai wa hari, domin kwaikwayon bankunan cikin gida, suna kuma yiwa mutane tayin tallafin gwamnati na bogi, ko kuma tallata manhajojin wayar hannu da suke kama da na gaskiya, a zahiri suna ɗauke da manhajojin leƙen asiri da za su iya bibiyar ayyukan masu amfani da su.

Turedi ya ƙara da cewa: "Muna sa ran wannan yanayi zai ƙara ta'azzara yayin da masu aikata laifukan ke inganta dabarunsu, ta hanyar amfani da abubuwan da aka samar da basirar na'ura mai kwakwalwa (AI) da kuma fasahar 'deepfake', wadda ke ƙirƙirar sauti ko bidiyo na bogi da ke kwaikwayon ainihin mutane."

Sau da yawa waɗannan masu aikata laifuka suna tsara shirye-shiryensu ne ta hanyar shafukan sadarwa a internet watau (dark web), inda ake amfani da fasahar ɓoye bayanan sadarwa domin tabbatar da sirrinta.

Hukumomin tabbatar da bin doka a ƙasashen duniya sun yi gargaɗin cewa laifukan intanet na ƙara girma da samun tagomashi, kuma ana gudanar da su ta hanyar da ta yi kama da harkokin kasuwanci.

Misali, wani rahoto da Ƙungiyar Sadarwa ta Duniya (ITU) ta fitar kan Ma'aunin Tsaron Intanet na Duniya (Global Cybersecurity Index), ya yi nuni da haɗurran da ke fuskantar sabbin masu amfani da intanet, ciki har da damfara, satar bayanai ta hanyar saƙonnin yaudara (phishing), da kuma ƙaruwar hare-haren manhajojin kwamfuta masu garkame bayanai tare da neman kuɗin fansa (ransomware).

Ga Etekpo, illolin irin wannan damfara sun kasance na zahiri.

"Na ji kamar ba ni da kariya, kuma ina cikin wani yanayi mai matuƙar haɗari," in ji shi.

Ya yi imanin cewa raunin da mutane da dama ke fuskanta ba ya da nasaba sosai da rashin ilimin fasaha, sai dai matsalar amincewa da mutane.

"Mutane da dama suna amincewa da waɗanda suke hulɗa da su a intanet, kuma suna ɗaukar mataki cikin gaggawa ba tare da fara tantance ko saƙon da suka karɓa na gaskiya ne ba," in ji shi.

Wannan haɗari ya fi kamari musamman a Afirka. Duk da cewa nahiyar na daga cikin yankunan da ke da mafi saurin bunƙasar amfani da intanet a duniya, Afirka ce nahiyar da ke da mafi ƙarancin yawan mutanen da ke da damar amfani da intanet.

Wani bincike da aka gudanar kwanan nan ya kuma bayyana cewa akwai babban bambanci tsakanin matakan samun damar amfani da intanet a yankuna daban-daban na nahiyar.

.

A ƙasashe irin su Benin da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango, wadda ke da yawan al'umma akwai adadi mai yawa na mutanen da har yanzu ba su da damar amfani da intanet.

Ayyukan intanet da ke amfani da tauraron ɗan Adam suna da tsada, yayin da kayayyakin more rayuwar intanet ta layin waya ke da ƙaranci, kuma galibi ba sa aiki yadda ya kamata. Bugu da ƙari, rashin ingantattun tsare-tsaren tsaro na barin mutanen da suka samu damar shiga intanet cikin haɗarin fuskantar damfara.

Duba da hasashen cewa adadin masu amfani da intanet a Afirka zai ƙaru da fiye da miliyan 280 cikin shekaru huɗu masu zuwa, akwai buƙatar gaggawa ta aiwatar da dabaru mafi inganci domin dakile laifukan intanet.

A cewar Ƙungiyar 'Yan Sandan Ƙasa da Ƙasa (Interpol), asarar kuɗaɗen da ake samu sakamakon laifukan intanet a Afirka ta ninka fiye da sau biyu tun daga shekarar 2024, inda ta tashi daga dala miliyan 192 zuwa dala miliyan 484.

Ko da yake an riga an samar da wasu matakan kare masu amfani da intanet, masana na ganin akwai buƙatar ƙara ƙarfafa su.

Matakan sun haɗa da shirye-shiryen ilimantarwa a makarantu kan yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira cikin aminci, da kuma ƙarfafa kariyar masu amfani da kayayyaki da ayyuka daga ƴan damfarar intanet.

Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi da laifuka (UNODC) ya samar da fasahohin zamani domin gano barazanar da ke intanet, tare da tsare-tsaren tsaro da aka gina cikin na'urori da tsarin kwamfuta, kamar matakan kula da damar shiga bayanai da kuma gano manhajojin kwamfuta masu cutarwa, a wani ɓangare na ƙoƙarinsa na yaƙi da laifukan intanet.

A halin da ake ciki kuma, Hukumar Binciken Laifuka ta Tarayya ta Amurka (FBI) na da ƙungiyoyi na musamman da jami'ai da aka horar domin yaƙi da laifukan intanet a kowane ofishinta na shiyya.

A Birtaniya kuwa, Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Ƙasa (NCA) ta jagoranci wasu bincike na ƙasa da ƙasa da suka yi nasara, waɗanda aka gudanar domin murƙushe ƙungiyoyin masu aikata laifukan intanet.

Sai dai da dama daga cikin waɗannan matakan sun fi mayar da hankali ne kan binciken laifukan intanet bayan an riga an aikata su, maimakon magance haɗurran da sabbin masu amfani da intanet ke fuskanta.

"Batun tsaron intanet babban ƙalubale ne," in ji Robert Anderson, wanda ya kafa ƙungiyar Telecom4Good, wata ƙungiya mai zaman kanta da ke samar da ayyukan fasahar sadarwa ga sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu a faɗin duniya, waɗanda da dama daga cikinsu suke Afirka, domin taimaka musu samun ingantattun ayyukan intanet masu sauƙi.

Kamfanin CrowdStrike na shawartar ƙungiyoyi da kada su ɗauki batun tsaron intanet a matsayin jerin ayyukan da za a gudanar a sau ɗaya tak, sai dai su ɗauke shi a matsayin wani tsari da ake ci gaba da aiwatarwa domin inganta hanyoyin kariya.

Ana sa ran waɗannan haɗurra za su ƙaru yayin da tsarin ƙirƙirarriyar basira ke ci gaba da faɗaɗa. Bisa ƙididdigar masana'antar fasaha, ana hasashen cewa yawan na'urorin da ke da alaƙa da intanet a faɗin duniya, tun daga kayayyakin samar da wutar lantarki da na'urorin da ake dasawa a zuciya domin taimaka mata bugawa, zuwa motocin da ke tafiya ba tare da direba ba, zai haura biliyan 38 nan da shekarar 2030.

Yayin da yawan na'urorin da ke da alaƙa da intanet ke ƙaruwa, haka nan ma giɓin tsaro da masu kutse za su iya amfani da su wajen kai hare-haren intanet ke ƙaruwa.

Gwamnatoci da hukumomin tabbatar da bin doka na ƙoƙarin gano tare da gwada hanyoyi daban-daban na magance wannan matsala. Wasu gwamnatoci sun yi ƙoƙarin kafa dokoki da ke ayyana wasu nau'o'in laifukan intanet a matsayin laifuffuka da doka ta haramta.

Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta ayyana tsaron intanet a matsayin ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da take ba fifiko a ƙarƙashin shirinta na "Agenda 2063".

A halin da ake ciki, Ƙungiyar Ƴan Sandan Ƙasa da Ƙasa (Interpol) na taimakawa rundunonin ƴan sanda a faɗin Afirka wajen hana aikata laifukan intanet da kuma gudanar da bincike a kansu.

Ƙoƙarin ya haɗa da horas da masu ƙananan sana'o'i kan yadda za su kare kansu daga ƴan damfarar intanet.

A Myanmar, inda amfani da intanet ya ƙaru cikin sauri a shekarun 2010 zuwa 2019, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ɗauki nauyin wani shirin wayar da kan jama'a da aka tsara domin sabbin masu amfani da intanet.

A shekarar 2024, Najeriya ta yi wa dokarta ta yaƙi da laifukan intanet kwaskwarima, inda ta haɗa da matakan kare masu amfani da intanet a sabbin kasuwannin ƙirƙirarriyar basira.

A Indiya kuwa, gwamnati ta kafa wata lambar waya ta musamman ta ƙasa da waɗanda aka damfara za su iya amfani da ita domin kai rahoton lamarin nan take, tare da hana fitar da kuɗaɗen da aka sace ta bankuna da manhajojin biyan kuɗi