Me ya sa INEC ta cire sunayen mutum sama da miliyan 1.6 daga kundinta?

Asalin hoton, Inec/X
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta ce ta cire bayanan masu rajistar zaɓe guda miliyan 1.6 da ta bayyana a matsayin marasa inganci daga rijistar masu zaɓe, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Hukumar ta ce ta gudanar da wannan aikin ne bayan sake tantance bayanan da aka tattara a lokacin rajistar masu zaɓe tsakanin shekarun 2025 zuwa 2026.
Kakakin INEC, Mohammed Kudu Haruna, ya ce an cire bayanan ne bayan binciken zarge-zargen cewa akwai wasu hotunan masu zaɓe da aka yi amfani da AI wajen samar da su.
Hakan kuma ya zo ne bayan wasu 'yan Najeriya sun yi ta wallafawa a kafafen sada zumunta cewa rajistar masu zaɓen da INEC ta fitar a watan Oktoban 2026 na ɗauke da hotunan da aka samar ta hanyar AI.
Wasu kuma sun yi iƙirarin cewa akwai sunayen mutane da suka ɓace daga rajistar, yayin da wasu suka ce an maimaita sunayensu fiye da sau ɗaya.
A lokacin, INEC ta bayyana cewa rajistar da ta wallafa a intanet ranar 26 ga Oktoba 2026 ita ce irin rajistar wucin-gadi da ta riga ta wallafa a cibiyoyin rajista a faɗin ƙasar daga ranar 9 zuwa 15 ga Oktoba 2026 domin jama'a su duba su kuma gabatar da korafe-korafensu.
Yanzu haka, hukumar ta ce ta cire jimillar bayanan masu zaɓe miliyan 1,609,553 daga rijistar masu zaɓen ƙasar bayan tantancewar da ta yi.
An samu bayanan masu zaɓe marasa inganci da mutum 873 da suka mutu
Shugaban hukumar zaɓen ta Najeriya, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa cikin bayanan masu zaɓe da aka cire sun haɗa da guda miliyan 1,608,660 marasa inganci da kuma 873 waɗanda mutanen suka riga suka mutu.
INEC ta ce ta karɓi bayanai mutanen miliyan 11,088,238 a tsarin ci gaba da rajistar masu zaɓe zango uku da aka yi, sannan na'urorinsu sun nuna musu cewa akwai buƙatar yin ƙarin bincike kan bayanan yatsun mutum miliyan 1,545,052 .
Shugaban na Inec ya ce bayanan da ke buƙatar ƙarin bincike ba yana nufin cewa ba su inganci ba ne nan take, amma jami'ai za su yi bincike a kansu da kuma yanke shawara.
Tun da farko, Inec ta ce ta cire bayanan masu zaɓe marasa inganci miliyan 1,277,052.
"Bayan ƙorafe-ƙorafe daga jama'a, za mu sake yin duba kan bayanan mutum 268,000. A cikinsu, mun tabbatar da cewa 217,722 ba su da inganci, ga sauran 50,278 kuma an tantance su tare da mayar da su cikin rajista."
Ya ƙara da cewa daga bisani sun gano wasu ƙarin mutum 113,886 da suka yi rajista ba bisa ka'ida ba, kuma tuni aka cire su daga kundin masu rajistar zaɓe.
'Mun samu bayanan da aka yi amfani da AI wajen saka su'
A kan batun amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen samar da hotuna, shugaban na Inec ya ce hukumar ta gano hanyoyi da aka bi wajen saka su a shafinta.
"Mun samu bayanan da aka yi amfani da AI wajen saka su, wani ne ya samu dama wajen aikata wannan lamari," in ji Amupitan.
INEC ta bayyana cewa an yi amfani da wasu jami'anta ne wajen saka bayanan masu zaɓe da AI.
Ya ce matsalar ita ce saboda suna amfani da wasu na'urori, amma yanzu za su sauya su zuwa manhajoji.
"Mun riga mun umarci daraktan sashen sadarwar zamani na hukumar mu cewa ba za a sake amfani da waɗannan na'urori ba. Maimakon haka, za a koma amfani da manhaja. Wannan manhajar ce za ta ɗauki hoton mutane," in ji Amupitan.
Ya ce wannan sabon tsarin ba zai bai wa ma'aikata damar shigo da hotuna daga wajen tsarin ba, domin hana su amfani da kowace irin tsarin intanet wajen saka hotuna.
Dangane da batun amfani da fasahar AI, INEC ta ce ba ta da wata ɓoyayyiyar manufa, kuma za ta kasance mai gaskiya da bayyana yadda take amfani da fasahar AI.

Asalin hoton, STEFAN HEUNIS / AFP) (Photo by STEFAN HEUNIS/AFP via Getty Images)
An samu jami'an Inec 54 da aikata ba daidai ba
Hukumar Zaɓen Najeriyar ta ce ta samu wasu ma'aikata 54 daga jihohi 10 bisa zargin hannu a aikata ba daidai ba kan wannan lamari.
Hukumar ta ce bincikenta ya nuna cewa wasu jami'anta masu yin rajista sun tafka kurarai, lamarin da ya janyo yi wa wasu rajista sau biyu, saka hotunan bogi da kuma sunayen mutanen da suka mutu da har yanzu suke cikin rijistar zaɓe.
INEC ta ce za ta ɗauki matakin ladabtarwa tare da yiwuwar gurfanar da waɗanda aka samu da hannu a lamarin, sannan za ta ƙara ƙarfafa tantance bayanan masu rajista ta hanyar amfani da yatsun hannu, tare da ci gaba da tantance sabbi da tsofaffin rijistocin masu zaɓe kafin zaɓen 2027.
Hukumar ta kuma ce ta riga ta gano tare da nazartar bayanan mutanen da abin ya shafa, yayin da ake ci gaba da bincike kan ma'aikatan da ake zargi da hannu a lamarin.
Amupitan ya ce ba za a sake samun irin wannan matsala ba, domin hukumar za ta ƙara tsaurara matakan rajista ta hanyar inganta tsarin ɗaukar bayanan yatsu, tabbatar da sahihanci da kuma ƙarfafa matakai wajen tantance masu rajista.
Abin da hakan ke nufi ga zaɓen 2027
Tsohon kwamishina a hukumar zaɓe ta Najeriya INEC, Festus Okoye, ya ce bayan zaɓen 2027, ya kamata a soke kundin rajistar masu kaɗa ƙuri'a gaba ɗaya, sannan a fara sabon rajista daga tushe.
A tattaunawarsa da BBC Pidgin, Okoye ya ce a wasu al'ummomi ana samun mutum ɗaya ya yi rajista fiye da sau ɗaya, don haka ya zama wajibi a samar da tsarin rajista da zai yi amfani da yatsu tun daga farko domin hana yin rajista sau da yawa.
Ya kuma ce kundin masu zaɓe da ake da shi a Najeriya a yanzu ba ya nuna ainihin yadda al'ummar ƙasar ke shiga zaɓe.
A cewarsa, wannan na iya buɗe ƙofa ga maguɗi a zaɓen 2027 saboda kundin rajistar ba ya da tsari yadda ya kamata.
"Na jagoranci kwamitin ƙungiyar lauyoyin Najeriya, kuma na ga yawan mutanen da suka fito domin kaɗa ƙuri'a. Mun ga cewa ƙasa da rabin waɗanda suka fito ne ke cikin rajistar masu zaɓe. Wannan yana nuna akwai babban giɓi a kundin rajistar."
Dangane da ma'aikatan INEC da ake zargi da hannu a wasu kura-kurai da suka faru a zaɓe, Okoye ya ce hakan ya samu ne saboda hukumar ba ta ɗauki tsattsauran matakai a baya ba cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci.
Ya buƙaci INEC ta miƙa ma'aikata 54 da ake zargi ga rundunar 'yan sanda domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su a kotu idan aka same su da laifi.
Okoye ya ce ya kamata a binciki mutanen da suka ɗauki waɗannan ma'aikata aiki ko suka sa su yin abin da suka aikata.
"Akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin amfani da giɓin da ke cikin tsarin zaɓe. Burinsu shi ne su ƙauce wa tsarin na'urar BVAS, sannan su riƙa rubuta sakamakon zaɓe ba bisa ƙa'ida ba," in ji shi.























