Labaran wasannin BBC Hausa

Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da kasuwar 'yan wasanni ta duniya daga nan BBC Hausa daga 24 zuwa 30 ga watan Agusta

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Muna cikin hidimar ɗaukar 'yan wasa ne - Moyes

    ,

    Kocin Everton, David Moyes, kan tambayar da aka yi masa game da Jack Grealish “Har yanzu ba mu yanke wani hukunci na ƙarshe kan hakan ba, amma a yanzu muna aiki ne wajen neman sabbin ‘yan wasa, kuma muna duba ko za mu iya kawo wasu idan hakan ya yiwu.

    “Babu wata tabbas a kan hakan, kuma ba daidai ba ne in ambaci mutum guda kawai.”

  2. 'Ba gaggawa muke ba domin sayar da manyan 'yan wasanmu'

    ,

    Kocin Everton David Moyes kan rade-radin yiwuwar Iliman Ndiaye ya bar kungiyar "Ba zan yi magana kan 'yan wasan wasu kungiyoyi daban ba. Jack [Grealish] ba dan wasanmu ba ne yanzu. Ya yi abin kirki sosai a gare mu, yaro ne nagari, amma bai dace in yi magana a kansa ba idan yana wata kungiyar.

    "Tabbas ba ma gaggawar sayar da mafi kyawun 'yan wasanmu, wannan kuwa babu shakka.

    "Gwargwadon abin da na sani, babu wani abu da zai sa mu damu. Ba mu samu wata magana daga kowace kungiya ba. Wani ya gaya min cewa mun yi hulda da Al-Hilal a lokacin bazara, amma ba mu samu komai daga gare su ba.

    "Akwai labarai da yawa da ke yawo wadanda ba koyaushe suke zama gaskiya ba. Wata kila wannan gaskiya ne, amma tabbas abubuwan da aka fada a baya ba gaskiya ba ne."

  3. 'Ina farin ciki da tawagarmu'

    Kocin Brighton and Hove Albion, Fabian Hurzeler, kan yiwuwar kawo sababbin ‘yan wasa: “Mu jira mu ga abin da zai faru.”

    Da aka tambaye shi ko zai gamsu da ƙungiyarsa idan kasuwar musayar ‘yan wasa ta rufe a yau, ya ce: “Eh. Akwai wasu ƙananan matsaloli na raunika, amma ba na zo nan ba ne don yin korafi. Ina nan ne domin nemo mafita tare da tawagata, kuma abin da muke ƙoƙarin yi kenan tun daga ranar farko. Don haka, eh, ina farin ciki da ƙungiyar da muke da ita.”

  4. Mene shirin Moyes a bana?

    g

    Everton za ta je filin Bournemouth ranar Asabar bayan ta fara kakar wasa cikin yanayi mai kyau.

    Toffees ta lallasa Preston da ci 4-0 a gasar League Cup, sannan ta fara yakin neman kambun Premier League da nasara 2-0 a kan Crystal Palace.

    Sai dai da alama hankalin mutane zai fi karkata kan batun canja wurin 'yan wasa a yau, inda sunayen Jack Grealish da Iliman Ndiaye suka mamaye kanun labarai.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC Sport cewa burin Grealish shi ne komawa Merseyside, inda yake son komawa Everton ta dindindin daga Manchester City bayan an dakatar da zaman aron da ya ke yi a kungiyar sakamakon raunin kafa da ya samu a watan Janairu.

    A gefe guda kuma, Manchester City na kokarin daukar Iliman Ndiaye bayan dan wasan tawagar Senegal din ya yi watsi da tayin sabunta kwantiragi da dama da aka gabatar masa a Merseyside.

  5. David Moyes ya isa taron manema labarai

    Da yake magana kan rade-radin cinikayyar da ke danganta ɗan wasan gefe na Everton, Iliman Ndiaye, da wasu ƙungiyoyi, Moyes ya ce “Tabbas ba mu da wani gaggawar sayar da fitattun ‘yan wasanmu.”

    Ndiaye ya zura ƙwallaye shida kuma ya bayar da taimakon ƙwallo uku a gasar Premier League a kakar da ta gabata.

  6. 'Delap ɗan wasa ne da ya dace da mu'

    ,

    “Mun yi tattaunawa a kwanaki da dama, idan zan faɗi gaskiya. Mun yi ƙoƙarin shawo kansa, kuma a ƙarshe mun samu nasarar gamsar da Liam cewa Nottingham Forest ita ce ƙungiyar da ta dace da shi a wannan lokaci na rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.

    “Har ma ina ganin kafin ya zaɓi Chelsea, kusan kowace ƙungiya a Premier League tana son Liam bayan kakar ban mamaki da ya yi a Ipswich.

    Da muka ji cewa akwai yiwuwar a ɗauke shi, kuma muna neman ɗan gaba mai ƙarfi a jiki, mai sauri kuma mai iya yin gudun kutsawa cikin masu tsaron baya. Muna da wasu nau’ikan ‘yan wasa daban, tare da fitaccen ɗan gaba Chris Wood wanda ya tabbatar da kansa a Premier League a matsayin mai zura ƙwallaye.

    Yanzu muna taka leda sosai da mai lamba tara, tare da Igor Jesus. Muna neman irin wannan nau’in ɗan wasa, kuma Liam ya dace da abin da muke nema. Mu ne cikakkiyar ƙungiyar da ta dace da shi, kuma na gamsu cewa shi ma cikakken ɗan wasan da ya dace da mu ne.”

  7. Glasner kan halin da ‘yan wasansa ke ciki

    ,

    “Eh, Morgan [Gibbs-White] yana shirye ya buga wasa, haka kuma Ryan Yates yana shirye. Wannan shi ne labari mai daɗi.

    “Ibrahim Sangare ya samu ƙaramin rauni a tsokar maraƙinsa yayin atisayen ranar Laraba, don haka ba zai buga wasan gobe ba.

    “Amma sauran ‘yan wasan biyu za su dawo su buga wasan.”

  8. Glasner zai yi magana da manema labarai

    ,

    Nottingham Forest za ta kara da Liverpool a ranar Asabar a wasanta na biyu na gasar Premier League a wannan kakar.

    Forest ta fara kakar 2026-2027 da rashin nasara 1-0 a hannun Leeds United a filin City Ground.

    An buga irin wannan wasan ne a ranar Talata a zagaye na biyu na Gasar League Cup. Forest ta sha kashi da ci 2-0, inda Leeds ta tsallaka zuwa zagaye na gaba.

    Tawagar Glasner za ta yi fatan samun sakamako mafi kyau a karawar da za ta yi da Liverpool.

    A taron manema labarai da ya gudanar ranar Alhamis, sabon kocin Liverpool Andoni Iraola ya yabawa tawagar Glasner, yana cewa: "Za ka iya gani nan take yadda suke taka leda cikin tsari, kuma ba sa bai wa abokan hamayya damar samun damammaki masu yawa."

  9. 'Yankuba Minteh na tare da Brighton'

    b

    "Shi ɗan wasan Brighton ne, kuma a halin yanzu babu wani abu da zan ƙara faɗi. Ina yaba masa saboda idan kasuwar musayar 'yan wasa ta rufe, zai kasance gaba ɗaya ya mayar da hankali kan wannan ƙungiya."

    "Tabbas, 'yan wasa suna da mafarkai da burace-burace, amma a ƙarshe dole ne mu duba abin da ya fi alheri ga ƙungiyar.

    Saboda haka mun tattauna da shi, kuma a halin yanzu tabbas ɗan wasan Brighton ne. Ba zan iya cewa fiye da haka ba, don haka mu jira mu ga abin da zai faru."

  10. Ba za mu ce komai kan Munoz ba - Glasner

    ,

    Kocin Nottingham Forest, Oliver Glasner, kan yiwuwar ɗaukar Daniel Munoz daga Crystal Palace:

    “Ba zan yi tsokaci kan sunayen wasu ‘yan wasa ba. Idan komai ya kammala kuma an sanya hannu kan takardu, za a sanar da ku.”

    Kan tambayar ko Forest na dab da kulla yarjejeniya da wani sabon ɗan wasa:

    “Eh, abin da na ji kenan.”

  11. Brighton ta doke Tromso ta samu tikitin Conference

    ,

    Brighton ta tabbatar da samun gurbinta na buga kwallon Turai karo na farko cikin shekaru uku bayan ta lallasa kungiyar Tromso ta Norway da ci 4-0, wanda ya ba ta tikitin shiga gasar Conference League.

    Bayan kunnen doki 0-0 da suka yi a wasan farko a makon da ya gabata, Seagulls ta fara wasa da karfi inda Charalampos Kostoulas, Maxim de Cuyper da Mats Wieffer suka ci mata kwallaye uku a rabin farko.

    Kwallon da Oliver Boscagli ya zura a minti na 86 ta tabbatar da gagarumar nasarar Brighton, bayan da aka soke wata kwallarsa ta farko saboda satar gida.

    Kocin Brighton Fabian Hurzeler ya bayyana wasan a matsayin na “rayuwa ko mutuwa” kafin a fara, kuma tabbas zai yi farin ciki da samun nasara ta biyu da ci 4-0 cikin kwanaki biyar kacal, bayan sun doke Aston Villa da irin wannan sakamakon a wasan farko na Premier League.

    Tromso ba ta iya maimaita bajintar da ta nuna a wasan farko ba, kuma ta kammala wasan ba tare da kai ko hari ɗaya.

    Yanzu kungiyar Hurzeler za ta buga gasar Turai karo na biyu a tarihinta, bayan da ta kai zagayen ‘yan 16 na Europa League a shekarar 2024.

    Jack Hinshelwood da Georginio Rutter duk sun kasance ba a cikin tawagar wasan na biyu ba bayan sun taka leda a wasan da Aston Villa.

  12. Ipswich ta ɗauki Palacios na Argentina

    ,

    Dan wasan tsakiyar Argentina Exequiel Palacios ya zama gwarzon Kofin Duniya na farko da ya sanya hannu a kungiyar Ipswich Town, bayan komawarsa daga Bayer Leverkusen.

    Palacios, mai shekaru 27, ya bar kungiyar ta Bundesliga kan kudi da ba a bayyana ba, kuma ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu da sabuwar kungiyar Premier League din.

    Ya kasance cikin tawagar Argentina da ta lashe Kofin Duniya a 2022, sannan ta kai wasan karshe a wannan bazarar. Haka kuma ya lashe Copa America sau biyu tare da kasarsa.

    Palacios ya ce:

    "Wannan kungiya ce mai babban buri kuma ina farin cikin buga kwallo a Ingila da kuma fafatawa da wasu daga cikin mafi kyawun kungiyoyi da 'yan wasa a duniya."

    Palacios, wanda shi ne dan wasa na 11 da Ipswich ta dauka a wannan kasuwar cinikin 'yan wasa, ya fara wasa a nasarar da Argentina ta yi da ci 3-1 a kan Jordan, wacce ke buga Kofin Duniya karo na farko, a matakin rukuni. Wannan ne kadai bayyanarsa a gasar ta 2026.

    Kocin Ipswich, Gary O'Neil, ya kara da cewa:

    "Dan wasa ne da ya samu gagarumar nasara a matakin koli na kwallon kafa, inda ya lashe babbar kambu mafi girma, wato Kofin Duniya, tare da manyan kofuna a matakin kulob."

    "Wannan kwarewar za ta kasance mai matukar muhimmanci a gare mu yayin da muke ci gaba da kokarin inganta tawagar a wannan bazarar."

  13. Hurzeler zai tattauna da manema labarai

    ,

    Ana sa ran kocin Brighton Fabian Hurzeler zai kasance cikin farin ciki idan ya zauna domin yin magana da kafafen yada labarai.

    Brighton ta tabbatar da samun gurbi a gasar Uefa Conference League, sannan kuma tana saman teburin Premier League yayin da kakar wasa ke shiga mako na biyu.

    Dan wasan tsakiya Jack Hinshelwood ne ke kan gaba a jadawalin masu yawan kwallaye a gasar bayan ya ci kwallaye biyu a wasan farko da suka doke Aston Villa.

    Sai dai akwai shakku kan ko Hinshelwood zai buga wasan da Brighton za ta yi da Chelsea a Stamford Bridge ranar Lahadi, bayan dan wasan mai shekaru 21 ya samu karamar matsala yayin atisaye a ranar Laraba.

    Saboda haka bai buga wasa na biyu da Brighton ta yi da Tromso a daren jiya ba.

    Ana sa ran Hurzeler zai ba da sabbin bayanai kan halin da kungiyar Brighton ke ciki nan ba da jimawa ba, amma da farko mu duba abin da ya faru a filin Amex a daren jiya.

  14. UEFA na son daukar matakin shari'a kan shugaban FIFA Gianni Infantino

    ,

    UEFA na shirya gurfanar da shugaban FIFA, Gianni Infantino, a gaban kotu bisa wani shiri da yanzu aka yi watsi da shi na sayar da hannun jari a gasar Kofin Duniya da sauran manyan gasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu.

    Takardun da BBC Sport ta gani sun nuna cewa hukumar kwallon kafa ta Turai ta nemi damar samun hujjoji da takardu domin amfani da su wajen gudanar da shari'a a Switzerland. UEFA na zargin Infantino da aikata abin da ta kira "mummunan rashin kula da harkokin gudanarwa".

    UEFA ta kuma bayyana cewa tana nazarin yiwuwar daukar matakin shari'a a kan wasu jami'an FIFA.

    Jim kadan bayan gasar Kofin Duniya ta bana, Infantino ya gabatar da shawarar kafa wani sabon kamfani mai suna FIFA Forward Enterprise (FFE).

    A karkashin shirin, za a sayar da wani bangare na mallakar manyan gasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu. Amma daga baya an yi watsi da shirin bayan fuskantar suka da adawa daga bangarori da dama a harkar kwallon kafa.

    A cikin bukatar da ta gabatar domin samun hujjoji, UEFA ta yi ikirarin cewa "A zahiri, wannan wata hanya ce da Infantino da karamin rukunin mutanensa za su samu ikon mallakar dindindin a kan muhimman kadarorin FIFA tare da cin gajiyar su, abin da zai cutar da FIFA, mambobinta da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa."

    UEFA ta ci gaba da zargin cewa Infantino ya tilasta amincewa da shirin cikin gaggawa ta hanyoyin cikin gida na FIFA.a ba.

  15. Wasannin Premier ƙarshen mako

    ,

    Juma'a

    Crystal Palace v Manchester City, 20:00

    Asabar

    Liverpool v Nottingham Forest, 12:30

    Bournemouth v Everton, 15:00

    Coventry City v Hull City, 15:00

    Tottenham Hotspur v Newcastle, 17:30

    Lahadi

    Chelsea v Brighton, 14:00

    Leeds v Brentford, 14:00

    Sunderland v Fulham, 14:00

    Manchester United v Ipswich, 16:30

    Litinin

    Aston Villa v Arsenal, 20:00

  16. Welbeck ya ci kwallo a wasansa na farko a Chelsea

    ,

    Danny Welbeck ya ci kwallo a wasansa ta farko yayin da aka ki sa Enzo Fernandez cikin tawagar Chelsea da ta doke Luton Town da ci 2-0 a zagaye na biyu na Gasar Carabao Cup.

    Dan wasan mai shekaru 35, wanda ya koma kungiyar daga Brighton a wannan bazarar, ya zura kwallo da kai daga kusa da raga a mintina 45 na biyu, kafin daga baya Hakeem Odoffin ya ci gida a kokarinsa na ciro kwallon da Estevao Willian ya buga masa.

    Fernandez, wanda wakilansa suka tattauna da Manchester City, ba a sanya shi cikin tawagar wasan an sa shi daga benci a wasan da Chelsea ta yi nasara da ci 3-2 a kan Fulham ranar Litinin a Premier League.

    Hakan ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni daga Argentina suka bayyana cewa ya nemi a bar shi daga cikin tawagar yayin da yake kokarin kammala komawa Etihad Stadium.

  17. Chelsea za ta biya fam miliyan 7.5 kan Martinez na Aston Villa

    f

    Chelsea ta amince da biyan fam miliyan 7.5 domin daukar mai tsaron ragar Aston Villa Emiliano Martinez.

    Dan wasan tawagar Argentina mai shekaru 33 zai yi gwajin lafiya a birnin Landan kafin ya kammala komawa Stamford Bridge, inda zai kara karfi a bangaren masu tsaron gida na Chelsea.

    Wannan matakin ya biyo bayan damuwar da aka nuna kan yadda Robert Sanchez ke taka leda, musamman bayan nasarar da Chelsea ta samu da ci 3-2 a kan Fulham ranar Litinin.

    Sanchez, wanda ya kasance mai tsaron gida na farko na Chelsea tun shekarar 2023, ya yi kuskure a wasan lokacin da harbin Josh King ya subuce masa ta kusa da sanda. Daga baya kuma ya sake zubar da kwallo a wuri mai hadari, lamarin da ya bai wa Gonzalo Garcia damar zura kwallo.

    Komawar Chelsea domin neman Martinez na nuna babban sauyi a ra'ayin shugabannin kulob din. A baya sun nuna cikakken goyon baya ga Sanchez, amma yanzu sun yanke shawarar daukar Martinez kwanaki kadan kafin rufe kasuwar cinikin 'yan wasa.

    Chelsea tana kuma da matashin mai tsaron gida Mike Penders, wanda ta saya daga Genk kan kusan fam miliyan 17. Ana sa ran zai fara buga wa kungiyar wasa a karawar Carabao Cup da Luton Town ranar Alhamis.

    A bangaren Aston Villa kuwa, kungiyar ta kasance a shirye ta sayar da Martinez tun bayan da ta dauko mai tsaron ragar Japan Zion Suzuki daga Parma kan kimanin fam miliyan 30 a farkon wannan wata.

    Wannan ciniki shi ne na baya-bayan nan cikin jerin mu'amaloli da aka yi tsakanin Chelsea da Aston Villa a 'yan lokutan nan.

  18. Ipswich na tattaunawa domin daukar aron Abraham daga Aston Villa

    n

    Ana sa ran dan wasan gaba zai bar Villa Park, yayin da dan wasan Chelsea Nicolas Jackson ke gab da kammala komawa Aston Villa a wata yarjejeniya da ta kai kusan fam miliyan 65 (£65m).

    Wannan kuma na nufin ana tsammanin Ollie Watkins zai koma kungiyar Al-Hilal kan kusan fam miliyan 51 (£51m), yayin da Villa ke sake gina gaba daya layin harinta.

    Aston Villa ta kasance a shirye ta bar Abraham ya tafi duk da cewa kungiyar ta saya shi daga Besiktas a watan Janairu kan fam miliyan 18.25 (£18.25m).

    Abraham yana jin dadin rayuwa a Villa kuma ya kasance yana shirin fafutukar neman matsayinsa a kungiyar, amma yanzu akwai yiwuwar ya koma Portman Road, filin wasan Ipswich Town.

    Ana sa ran yarjejeniyar za ta kasance ta aro kai tsaye, ba tare da zabin saye ko tilas na saye ba ga Ipswich kan dan wasan mai shekaru 28.

    Abraham ya ci kwallaye uku a wasanni 17 da ya buga wa Aston Villa. A baya ma ya taba buga wa Villa a matsayin aro, inda ya taimaka musu samun daukaka zuwa Premier League a kakar wasa ta 2018-19.

    Ipswich ta kashe kusan fam miliyan 150 (£150m) wajen sayen sababbin 'yan wasa 12 a wannan bazarar, bayan dawowarta gasar Premier League.

  19. Za a yi wasan ƙarshe na bana a Madrid

    b

    Za a buga wasan karshe na UEFA Champions League na wannan kakar a filin wasa na Estadio Metropolitano, gidan kungiyar Atletico Madrid.

    Filin wasan mai daukar mutane kusan 70,000 zai karbi bakuncin babban wasan ƙwallon ƙafa na nahiyar Turai bayan UEFA ta ba shi damar shirya wasan karshe.

    Tun da farko, an bai wa San Siro na birnin Milan damar karbar bakuncin wasan na 2025, amma daga baya aka kwace wannan damar saboda damuwa kan shirye-shiryen gyaran filin wasan. Hakan ya sa UEFA ta sake bude tsarin neman wadanda za su shirya wasan, kuma a karshe aka zabi Madrid a matsayin mai masaukin baki.

    Wannan ba shi ne karo na farko da Estadio Metropolitano zai karbi bakuncin wasan karshe na Champions League ba. A shekarar 2019, an buga wasan karshe a filin, inda Liverpool ta doke Tottenham Hotspur da ci 2-0 domin lashe kofin.

    Yanzu dai akwai yiwuwar Atletico Madrid za ta yi fatan kaiwa wasan karshe da za a buga a gidanta, abin da zai ba magoya bayanta babban buri yayin da gasar Champions League ta 2026-27 ke ci gaba da daukar hankali.

  20. LASK ta kara da:

    • Liverpool (a gida)
    • Real Madrid (a waje)
    • Porto (a gida)
    • Sporting CP (a waje)
    • Fenerbahce (a gida)
    • Bodo/Glimt (a waje)
    • Slovan Bratislava (a gida)
    • AEK Athens (a waje)