Labaran wasannin BBC Hausa

Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da kasuwar 'yan wasanni ta duniya daga nan BBC Hausa daga 24 zuwa 30 ga watan Agusta

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Tottenhma ta shiga kasuwar saye da sayerwa da karfinta

    Ga jerin 'yan wasan da Tottenham ta dauko zuwa yanzu a wannan kasuwar musayar 'yan wasa:

    • Savinho (Manchester City zuwa Tottenham) – £75m
    • Sandro Tonali (Newcastle United zuwa Tottenham) – £100m
    • Mateus Fernandes (West Ham United zuwa Tottenham) – £85m
    • Jan Paul van Hecke (Brighton zuwa Tottenham) – £52m
    • Marcos Senesi (Bournemouth zuwa Tottenham) – Kyauta
    • Andrew Robertson (Liverpool zuwa Tottenham) – Kyauta
    • Martin Dubravka (Burnley zuwa Tottenham) – Kyauta

    Wannan na nuna cewa Tottenham ta kashe kuɗi masu yawa a wannan bazarar, inda ta zuba aƙalla fam miliyan 312 kan manyan saye uku da huɗu, ba tare da ƙididdige kuɗaɗen kari da sauran tanade-tanaden da ke cikin kwantiragi ba.

    Zuwa yanzu, sayen Sandro Tonali kan £100m shi ne mafi tsada, sai Mateus Fernandes (£85m) da kuma Savinho (£75m). Haka kuma, ƙungiyar ta ƙara ƙarfafa tsaro da gogewa ta hanyar ɗaukar Marcos Senesi, Andrew Robertson da Martin Dubravka ba tare da biyan kuɗin saye ba.

    Idan har Tottenham ta kammala sayen Omar Marmoush daga Manchester City, kuɗin da ta kashe a wannan bazarar zai ƙara tashi sosai, lamarin da ke nuna aniyarta ta gina ƙungiya mai ƙarfin lashe manyan kofuna a kakar wasa mai zuwa.

    ,
  2. Ina batun Marmoush da Tottenham?

    ,

    Savinho ya bayyana Roberto De Zerbi a matsayin ɗaya daga cikin "fitattun masu horarwa a duniya" bayan ɗan wasan gaba ya kammala komawarsa daga Manchester City zuwa Tottenham Hotspur.

    Da yake magana da shafin yanar gizon Tottenham bayan sanya hannu a kungiyar da ta lashe Europa League ta 2025, tauraron na Brazil ya ce:

    "An ɗauki lokaci kafin komai ya kammala amma ina matuƙar farin cikin kasancewa a nan.

    Wannan babbar dama ce a wata ƙungiya mai girma tare da ɗaya daga cikin mafi kyawun masu horarwa a duniya.

    Da zarar na yi magana da kocin, nan take na san cewa dole ne in zo. Ya gaya mini cewa yana son taimaka mini wajen kaiwa mataki mafi girma, kuma na yi imanin za mu iya cimma hakan tare, a matsayin ƙungiya."

  3. Ethiopia na neman ɗaukar nauyin AFCON 2028

    ,

    Habasha ta miƙa buƙatarta a hukumance domin karɓar baƙuncin gasar Kofin Nahiyar Afirka AFCON ta shekarar 2028, wanda zai zama karo na farko da ƙasar za ta shirya gasar cikin fiye da rabin ƙarni.

    Hukumar Kwallon Kafar Habasha ta tabbatar da gabatar da takarar a wani saƙo da ta wallafa a shafin X a daren Litinin.

    A karo na ƙarshe da Habasha ta karɓi bakuncin gasar shi ne a shekarar 1976.

    Habasha ita ce ƙasa ta biyu mafi yawan jama'a a Afirka, inda ake hasashen tana da mutane kusan miliyan 130.

    Bugu da ƙari, babban birninta Addis Ababa ne hedkwatar Tarayyar Afirka (AU). Haka kuma, Addis Ababa ne babban birnin ƙasa mafi tsayi da ke kan tudu a Afirka, tana da tsayin mita 2,300 daga matakin teku.

    Sai dai takarar na fuskantar ƙalubale da dama, ciki har da tashe-tashen hankula da har yanzu suke gudana a jihohin Amhara da Oromia, waɗanda su ne jihohi mafiya yawan jama'a a ƙasar.

    Har ila yau, akwai fargabar sake barkewar yakin basasa tsakanin gwamnatin tarayya da yankin Tigray da ke arewacin ƙasar.

    Tawagar ƙwallon ƙafar Habasha tana matsayi na 143 cikin ƙasashe 211 a jadawalin FIFA.

    Haka kuma, karo na ƙarshe da ta buga gasar AFCON shi ne a shekarar 2022, inda aka fitar da ita tun daga matakin rukuni.

    ,
  4. Man City da Tottenham na rige-rigen ɗaukar Cody Gakpo

    ,

    Manchester City ta shiga cikin jerin kungiyoyin da ke neman daukar ɗan wasan gaba na Liverpool da ƙasar Netherlands, Cody Gakpo mai shekaru 27, yayin da Tottenham Hotspur ma ke ci gaba da kokarin kulla yarjejeniya da shi.

  5. Manchester City ta amince da sayen Allan Elias daga Palmeiras

    ,

    Manchester City ta cimma yarjejeniya da Palmeiras kan ɗaukar ɗan wasan gefe na Brazil Allan Elias a wani ciniki da zai iya kaiwa har fam miliyan 34.2.

    An shirya Allan Elias mai shekaru 22 ya maye gurbin ɗan uwansa ɗan ƙasar Brazil Savinho, wanda ake sa ran zai koma Tottenham Hotspur.

    City za ta biya kuɗin farko na fam miliyan 32, sannan a ƙara wasu fam miliyan 2.2 a matsayin ƙarin kuɗaɗen da suka danganci wasu sharudda. Ana kuma sa ran ɗan wasan zai yi gwajin lafiya cikin kwanaki masu zuwa.

    A gefe guda kuma, City na ci gaba da tattaunawa kan sayar da ɗan wasan gaba na Masar Omar Marmoush zuwa Tottenham.

    Majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun ce akwai "kyakkyawar dama" yarjejeniyar za ta kammala kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar 1 ga Satumba.

    Har yanzu dai tattaunawa na ci gaba tsakanin kulob ɗin biyu, duk da cewa akwai wasu bayanai da sharudda da ba a kammala daidaitawa a kansu ba.

    Haka kuma, ɗan wasan tsakiya Nico Gonzalez na iya barin filin wasa na Etihad kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa, inda Newcastle United ke nuna sha'awa wajen ɗaukar ɗan wasan na Spain.

  6. Me ake ciki ne kan cinikin Watkins

    a

    Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya, wadda ta bayar da tayin kusan fam miliyan 40, har yanzu ba ta kai farashin da Aston Villa ke nema domin sayar da Ollie Watkins ba.

    Yayin da ranar rufe kasuwar musayar 'yan wasa ta kusa a ranar Talata mai zuwa, Villa na da niyyar tsayawa tsayin daka kan dan wasan da ya fi kowa zura mata ƙwallaye a tarihin Premier League.

    Har yanzu ana ganin akwai tazara mai yawa kafin a cimma yarjejeniya, duk da cewa kocin Aston Villa, Unai Emery, ya bayyana a makon da ya gabata cewa mai yiwuwa Watkins ya bar kungiyar.

    Al-Hilal, wadda ta dauki Crysencio Summerville daga West Ham a watan Yuli, na iya bukatar ta sallami ko kuma ta fitar da daya daga cikin 'yan wasanta na ketare domin samun gurbin rajistar Watkins. Ko da yake ta tura Darwin Nunez aro zuwa Diriyah a makon da ya gabata, har yanzu akwai wasu batutuwa da dole a warware kafin yarjejeniyar ta kammala.

    Watkins yana atisaye shi kadai bayan ya dawo daga karin hutun da ya samu sakamakon buga Gasar Kofin Duniya, kuma rahotanni sun nuna cewa ya riga ya bayyana wa shugabannin Aston Villa ra'ayinsa na son barin ƙungiyar.

    Duk da cewa Watkins ko wakilansa ba su yi wata magana a bainar jama'a ba, an fahimci cewa dan wasan a shirye yake ya saurari tayin komawa Saudiyya.

  7. Akwai buƙatar a riƙa jin tsoron Manchester United - Rooney

    ,

    Babban kocin Manchester United, Michael Carrick, ya yi wasu muhimman bayanai guda biyu yayin taron manema labarai bayan rashin nasarar da ƙungiyarsa ta yi da ci 2-0 a hannun sabuwar ƙungiyar da ta hawo Gasar Premier, Hull City, a wasan farko na kakar bana.

    Ya ce "Mun yi abubuwa masu kyau da yawa a yau. Na san mutane za su manta da hakan saboda sakamakon wasan, amma a gare mu ba za mu manta da su ba."

    Bayan wasu tambayoyi kaɗan, Carrick ya sake cewa "Don kawai mun yi rashin nasara a yau ba yana nufin sai an warware ko a sake nazarin komai da ya shafi ƙungiyar ba."

    Sai dai galibin masu sharhi da masu bibiyar wasan suna ganin Manchester United ta rasa zafin fafatawa da kuzarin matsawa abokan hamayya.

    Ko da ma tsohon ɗan wasan United kuma babban abokin Carrick, Wayne Rooney, ya bayyana hakan a shirin Match of the Day.

    Rooney ya ce: "Idan Manchester United na son ɗorawa kan abin da ta cimma a kakar da ta gabata, dole ne ta zama ƙungiyar da sauran ƙungiyoyi ke jin tsoronta."

    Ya ƙara da cewa: "Ya kamata a samu ƙarin kuzari wajen matsa wa abokan hamayya lamba. Sun yi wasa cikin sanyin jiki da yawa."

    Sai dai Carrick bai amince da wannan ra'ayi ba. Ya ce "Don kawai an doke ku ba yana nufin kun yi wasa cikin sanyin jiki ba."

    "Wasa ɗaya ne kawai. Irin waɗannan sakamako na iya faruwa a ƙwallon ƙafa. Dukanmu mun san hakan. Ba abin farin ciki ba ne idan ya faru, amma yana faruwa."

    Wannan martani dai ya dace da halin Carrick, wanda aka fi sani da natsuwa da kwanciyar hankali. Duk da haka, ya amince cewa yadda ya fito a bainar jama'a bayan wasan ya bambanta da yadda yake ji a zuciyarsa bayan shan kaye.

    Carrick ya shafe kusan shekaru 20 yana da alaƙa da Manchester United, a matsayin ɗan wasa, koci, babban koci da kuma magoyi baya.

  8. Ana daf da cimma matsaya tsakanin Arsenal da Al Hilal kan Martinelli

    a

    Arsenal na ci gaba da tattaunawa da kulob din Al-Hilal na Saudiyya kan sayar da Gabriel Martinelli kan kuɗi fam miliyan 50.

    Dan wasan na Brazil mai shekaru 25 na da 'yancin barin Arsenal a wannan bazara, bayan da kociyan kungiyar Mikel Arteta ya bayyana cewa ɗan wasan gaban ba ya cikin tsare-tsarensa na gaba.

    Tattaunawar tsakanin kungiyoyin biyu ta ƙara ƙarfi a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kuma yanzu yarjejeniya ta kusa kammaluwa.

    Idan aka cimma matsaya ta ƙarshe, Martinelli ne zai yanke hukunci kan ko yana son komawa taka leda a gasar Saudi Pro League, bayan da a baya ya ƙi tayin komawa Galatasaray ta Turkiyya.

    Rahotanni sun ce albashin da Al-Hilal ke tayin baiwa Martinelli ya fi fam 180,000 a mako da yake karɓa a Arsenal.

    Martinelli ya koma Arsenal daga kulob din Ituano na Brazil a shekarar 2019, kuma saura watanni 12 kacal a kwantiraginsa na Emirates.

    A kakar wasan da ta gabata, ya buga wasanni 53 a dukkan gasa, inda ya ci ƙwallaye 11 yayin da Arsenal ta lashe kambun Premier.

    Sai dai ba a saka shi cikin tawagar Arsenal ba a wasan farko na gasar da Coventry ranar Juma'a, wanda Gunners ta yi nasara da ci 3-0.

    Tsohon dan wasan gaba na Arsenal, Ian Wright, ya soki matakin da Arteta ya dauka na cire Martinelli daga tawagar, tare da yadda kulob din ke mu'amala da shi.

  9. Tottenham ta kammala sayen Savinho daga Man City

    ,

    Tottenham ta kammala ɗaukar ɗan wasan gefe na Brazil, Savinho, daga Manchester City kan kuɗi fam miliyan 75.

    Matashin mai shekara 22 ya sanya hannu kan kwantiragi na dogon lokaci da Spurs, yayin da ƙungiyar Roberto de Zerbi za ta iya biyan ƙarin fam miliyan 10 (£10m) idan wasu sharuɗɗan cikin sun cika.

    Komawar Savinho zuwa arewacin Landan ta daɗe tana kan hanyar kammalu wa, domin Spurs ta yi ƙoƙarin sayensa tun bazarar bara amma ba ta yi nasara ba.

    A lokacin, Savinho ya zaɓi ci gaba da zama a filin wasa na Etihad, amma bai samu buga wasa sosai ba a ƙarƙashin Pep Guardiola a kakar da ta gabata, inda ya fara wasa sau bakwai kacal a gasar Premier League.

    Da yake magana bayan kammala canjin, Savinho ya ce: "An ɗauki lokaci mai tsawo kafin a kammala komai, amma ina farin cikin kasancewa a nan."

    "Wannan babbar dama ce a wani babban kulob da ke da ɗaya daga cikin mafi kyawun masu horarwa a duniya."

    "Da zarar na yi magana da kocin, na san dole ne in zo. Ya gaya min cewa yana son taimaka mini in kai mataki mafi girma, kuma na yi imanin za mu iya cimma hakan tare a matsayin ƙungiya."

    Savinho ya koma Manchester City daga kulob ɗin Troyes na Faransa a shekara ta 2024 kan kuɗi fam miliyan 30.8.

    A tsawon zamansa da City, ya buga wasanni 84 a dukkan gasa, inda ya ci ƙwallaye bakwai tare da bayar da taimakon ƙwallaye 16.

  10. Chelsea ta doke Fulham 2-3 har gida

    a

    Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Chelsea ta samu nasarar doke abokiyar burminta Fulham har gida da ci 2-3 a wasan hammayar Landan.

    Tun a daƙiƙa ta 31 da sa wasam kan a kai minti ɗaya João Pedro dan wasan gaban Chelsea ya zura kwallo ta farko.

    31 - Da aka auna a daƙiƙa 31 kacal, João Pedro ya zura ƙwallo mafi sauri da aka taɓa ci a ranar farko ta kakar Premier League.

    Wannan na nufin babu wani ɗan wasa da ya taɓa zura ƙwallo cikin sauri haka a wasan farko na kakar Premier League tun bayan kafa gasar.

    Ƙwallon da João Pedro ya ci cikin daƙiƙa 31 ya kafa sabon tarihi a matsayin ƙwallo mafi sauri da aka ci a ranar buɗe kakar Premier League.

    A mintina na 23 J. King ya dawo da Fulham cikin wasan, wani abu da ya bata karsashi da kwarin gwiwa.

    Sai dai gabanin a juya hutun rabin lokaci ɗan wasan da Chelsea ta saya daga Aston Villa mafi tsada Morgan Rogers ya zira kwallo ta biyu a wasan, ta farko da ya ci a sabuwar ƙungiyarsa a wasan farko.

    Wannan zai rage matsin lamba kan ɗan wasan da aka saya fam miliyan 117 mafi tsada a wannan kakar baki ɗaya.

    Bayan da matsi ya ƙaru ga Chelsea sai a mintina na 49 Cole Palmer ya ƙara kwallo ta uku wadda da ita ce kuma Chelsea ta tsira a wasan.

    Cin kwallon bai kashewa Fulham gwiwa ba, ta ci gaba da matsawa na ganin ta farke kwallayenta, inda dan wasan da ta ɗauko daga Real Madrid Gonzalo García ya ci tasa shi ma a wasansa na farko a mintina na 54.

    A haka aka ƙare wasan Chelsea na gaba 2-3.

    Sai abin birgewar shi ne yadda matasan 'yan kwallon Fulham suka buga wasansu ba tare da jin fargaba ko tsoro ba, kuma ba su tare a baya ba domin nuna kariya.

  11. , Fulham 2-3 Chelsea

    Ina ganin Xabi Alonso zai duba sosai yadda aka tsara da kuma yadda layin baya na mutum biyar ɗin nasa ya kasance.

    A zahiri, Chelsea na iya lashe wannan wasa cikin sauƙi da tazara mai kyau da ba don kuskure ɗaya ko biyu da suka yi a tsaron baya ba.

    Duk lokacin da suka kai hari sun nuna haɗari kuma sun samar da damammaki masu yawa, amma gazawar tsaron ta ba Fulham damar ci gaba da kasancewa cikin wasa.

    Alonso zai ji daɗin yadda ƙungiyarsa ta ƙirƙiri damammaki da harin da ta kai, amma babu shakka zai damu da yadda suka bari aka ci musu ƙwallaye daga kuskuren da za a iya kauce wa.

  12. Ƙarin lokaci, Fulham 2-3 Chelsea

    Alƙalin wasa ya ƙara mintina huɗu domin kammala wannan karawa

  13. Labarai da dumi-dumi, Fulham 2-4 Chelsea

    Pedro ya kara amma mai taimakawa alkalin wasa ya daga tuta

  14. , Fulham 2-3 Chelsea

    Fulham ta yi matuƙar ƙoƙari wajen ci gaba da kasancewa cikin wasan. A wasu lokuta, Chelsea ta nuna bambanci sosai, inda ta fi abokiyar karawarta a kusan kowane bangare na wasa.

    Sai dai Fulham ba ta karaya ba. Duk da matsin lambar da Chelsea ta yi, ta nuna jajircewa da ƙwazo, inda ta samu damar dawowa cikin wasan har sau biyu.

    Wannan alama ce ta ƙwarewa da ƙarfin hali daga Fulham, wadda ta ƙi yarda a raba ta da wasan duk da irin ƙarfin da Chelsea ta nuna a wasu lokuta.

  15. , Fulham 2-3 Chelsea

    Kasa da minti biyar ne ya rage a wasan Chelsea na kan gaba da ci 2-3...

    Idan har ta yi nasara za ta zama abar nunawa ga kungiyar ta Xabi Alonso

  16. , Fulham 2-3 Chelsea

    a

    Enzo Fernandez ba ya kauce wa neman ƙwallo, kuma tun bayan da ya shigo wasan yana samun damar mu'amala da ita sosai.

    Dan wasan tsakiyar na Argentina na ta ƙoƙarin karɓar ƙwallo da kuma haɗa wasa, yana ba Chelsea wata hanya ta samun nutsuwa da riƙe ƙwallo a tsakiyar fili.

    Zai iya ba Chelsea ƙarin iko damamaye wasa fiye da yadda Romeo Lavia ya bayar a wannan wasan, musamman wajen rarraba ƙwallaye da kuma rage matsin lambar da Fulham ke yi.

    A wannan matakin na wasan, Chelsea na buƙatar wanda zai kwantar da hankali a tsakiyar fili, kuma Enzo na nuna cewa zai iya taka wannan rawa.

  17. Chelsea ta yi canji, Fulham 2-3 Chelsea

    Za a sako Enzo Fernandez da Pep Chavarria su maye gurbin Romeo Lavia da Jorrel Hato.

  18. , Fulham 2-3 Chelsea

    Yanzu Fulham ce ke matsa wa Chelsea lamba sosai a rabin filinta.

    Waccan ƙwallon da suka ci ta ba su sabon ƙwarin gwiwa kuma ta sa sun sake yarda cewa za su iya samun wani sakamako mai kyau daga wasan.

    Chelsea na fama da wahala wajen fita da ƙwallo daga baya, yayin da Fulham ke ci gaba da kai hare-hare da kuma matsa musu a ko'ina cikin fili.

    Da alama muna fuskantar mintuna 30 na ƙarshe masu matuƙar kayatarwa, domin wasan ya buɗe kuma dukkan ɓangarorin na nuna aniyar neman ƙarin ƙwallaye.

    a
  19. , Fulham 2-3 Chelsea

    a

    Wannan ya kasance mummunan wasan a baya ƙwarai. Ya kamata an kawar da ƙwallon tun farko, amma Sanchez ya sake buga ta ya mayar da ita cikin yankin haɗari. Wani kuskure ne kuma daga mai tsaron ragar.

    Garcia bai san abubuwa da yawa game da yadda ƙwallon ta zo masa ba, amma yana wurin da ya dace, kuma hakan ya ba shi damar kai mata da kai ya zura ƙwallon.

  20. Labarai da dumi-dumi, Fulham 2-3 Chelsea, Kwallo a raga......

    Gonzalo Garcia ya farke wa Fulham yanzu wasa ya koma Fulham 2-3 Chelsea.

    Wannan kuskure ne daga Levi Colwill, wanda ya kasa hasashen hanyar da ƙwallon za ta bi a cikin yadi na 18, lamarin da ya bai wa Timothy Castagne damar kai hari tare da tilasta wa Robert Sanchez yin ceto.

    Sai dai ceto ɗin na Sanchez bai yi kyau ba, domin ya murɗe ƙwallon kai tsaye zuwa gaban Gonzalo Garcia.

    Garcia ya yi saurin mayar da martani, inda ya buga ƙwallon da kai cikin raga.

    Babban kuskure ne daga Chelsea a matakin tsaro, kuma Fulham ta yi amfani da damar ba tare da ɓata lokaci ba.

    a