Barcelona ta ce 'yansanda sun yi amfani da karfi kan magoya bayanta
Rikicin Crystal Palace da Mateta na kara dagulewa
Arbeloa da Alonso abokan juna da za su fafata a Premier
Rahoto kai-tsaye
Muhammad Buhari Fagge
Labarai da dumi-dumi, Fulham 1-3 Chelsea, Kwallo ta uku a ragar Fulham... 49
Asalin hoton, Getty Images
Cole Palmer ya kara sa kungiyarsa ta Chelsea a gaba 1-3.
Mene ne ya ragewa Fulham da Arbeloa?
Yanzu haka nake rubutu game da yadda Cole Palmer ya yi wani gagarumin kokari inda ya shige wa 'yan wasan Fulham hudu kafin daga bisani ya buga kwallon da ta wuce gefe da raga.
Amma a wannan karon, ya yi wani gudu mai kyau ya zagaye Joao Pedro kafin ya zura kwallon ta tsakanin kafafun mai tsaron gida Bernd Leno.
Wannan ƙarewa ce mai kayatarwa daga Palmer, wanda ya nuna nutsuwa da ƙwarewa wajen cin ƙwallon, yayin da Chelsea ta ci gaba da nuna hatsari a harinta.
Bayan nasarar da Barcelona ta samu da ci 5-0 a wajen Elche ranar Lahadi, an tambayi Hansi Flick ko kungiyar za ta sayi sabon ɗan gaba.
Ya amsa da cewa: "Za mu yi magana bayan wannan wasan. Mun riga mun bayyana hakan, saboda ni da Deco daraktan wasanni na Barcelona muna tattaunawa akai-akai kan abin da za mu iya yi da kuma abin da yake da muhimmanci. Haka ma za mu ci gaba da yi a mako mai zuwa.
"Saboda haka, za mu jira mu gani. "Muna matuƙar farin ciki da wannan nasarar da ci 5-0 da kuma maki uku, domin wannan fara gasa ne da ƙafar dama a gare mu. Wannan shi ne abin da muke so. Haka kuma ya ba mu kwarin gwiwar da muke bukata domin wasanni na gaba."
Maganar Flick ta nuna cewa Barcelona na ci gaba da duba yiwuwar ƙara sabon ɗan gaba a tawagar, amma har yanzu ba a yanke hukunci na ƙarshe ba yayin da tattaunawa ke gudana tsakanin shi da Deco.
Morgan Rogers ya gama nuna kansa
Dan wasan da Chelsea ta sayo daga Aston Villa kan kuɗi fam miliyan 117, Morgan Rogers, ya taka rawar gani sosai a wasan.
Ya matsa lamba yadda ya kamata, ya kasance barazana ga abokan hamayya idan yana da ƙwallo, sannan motsinsa a cikin yankin bugun yadi na 18 ya kasance abin a yaba. Yanzu kuma ya samu ƙwallon farko da zai nuna irin gudunmawar da ya bayar.
Sabon ɗan wasa Maxence Lacroix ne ya ba shi damar cin ƙwallon, inda ya aika da ƙwallon ga Rogers ya tura cikin raga a sandar baya ba tare da wata matsala ba.
Magoya bayan Chelsea da suka yi tafiya zuwa filin wasan ma sun riga sun ƙirƙiro wa Rogers waƙar ƙarfafawa ta musamman.
Har yanzu wasan bai ka kare ba, amma sababbin 'yan wasan da aka saya sun kasance daga cikin fitattun waɗanda suka haskaka a ƙungiyar Xabi Alonso.
Hutun rabin lokaci, Fulham 1-2 Chelsea
Asalin hoton, Getty Images
An tafi hutun rabin lokaci, Chelsea na kan gaba a wasan da ci 1-2.
Dole Filham ta sake zage dantse domin ganin ta yi abin da ya kamata a mintina 45 na biyu.
Abin burgewa, Fulham 1-2 Chelsea
Asalin hoton, Getty Images
Kwallon da Morgan Rogers ya ci kwallo a wasansa na farko na Premier a matsayin ɗan wasan Chelsea zai rage masa matsin lamba sosai.
Yanzu ya samu ƙwarin guiwa bayan buɗe asusun zura ƙwallaye tun da wuri, kuma hakan zai sa rayuwarsa ta fi sauƙi a sabon kulob ɗinsa.
Matsin lambar ya ragu... aƙalla a yanzu.
Pedro ya kafa tarihi, Fulham 1-2 Chelsea
Asalin hoton, Getty Images
31 - Da aka auna a daƙiƙa 31 kacal, João Pedro ya zura ƙwallo mafi sauri da aka taɓa ci a ranar farko ta kakar Premier League.
Wannan na nufin babu wani ɗan wasa da ya taɓa zura ƙwallo cikin sauri haka a wasan farko na kakar Premier League tun bayan kafa gasar.
Ƙwallon da João Pedro ya ci cikin daƙiƙa 31 ya kafa sabon tarihi a matsayin ƙwallo mafi sauri da aka ci a ranar buɗe kakar Premier League.
Fulham 1-2 Chelsea, Kwallo a raga
Chelsea ta kara ta hannun sabon dan wasanta Morgan Rogers a minti na 40
, Fulham 1-1 Chelsea
Minti 40 da sa wasa, saura mintina 5 a kammala wasa.
Fulham 1-1 Chelsea, Josh King (23 mins)
Robert Sanchez bai taɓa nuna cikakken kwanciyar hankali a wannan wasan ba, kuma hakan ya janyo wa Chelsea matsala yayin da Josh King ya buga wata ƙwallo kai tsaye ta tsakiyar raga, amma ta wuce hannun mai tsaron gidan Chelsea.
Wannan babban kuskure ne daga Sanchez, amma magoya bayan Fulham ko kaɗan ba su damu da yadda aka ci ƙwallon ba, domin sun yi murnar ganin ƙungiyarsu ta ƙara cin gaba.
Abin da ake yiwa Vinicius ya wuce gona da iri - Mourinho
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Real Madrid, Jose Mourinho, ya ce Vinicius Jr yana buƙatar nuna "ƙarfin sarrafa kansa" bayan ya yi ikirarin cewa ana muzanta ɗan wasan a filin wasa.
Kalaman Mourinho mai shekaru 63 sun zo ne bayan da ɗan wasan na Brazil ya samu katin gargadi da bai kamata ba a wasan da Real Madrid ta doke Espanyol da ci 2-1 a farkon kakar La Liga, sakamakon wata gardama da ya shiga da ɗan wasan tsakiya Cala a mintina 45 na farko.
Vinicius Jr ya fara fuskantar cin zarafi a tsawon shekaru takwas da ya yi yana taka leda a Real Madrid, ciki har da lokacin da Mourinho ke zaune a kujerar horar da Benfica lokacin da aka zargi Gianluca Prestianni da yi wa ɗan wasan na Brazil kalaman wariyar launin fata, zargin da ɗan ƙasar Argentina ya musanta.
Mourinho ya ce: "Ina iya fuskantar haɗarin ku koma baya ku fito da kalaman da na yi watanni da suka gabata lokacin da nake abokin hamayyar Vini Jr."
Ya ƙara da cewa: "Yanzu Vini Jr ɗan wasana ne. Vini Jr ba mala'ika ba ne, amma abin da ake yi masa ya wuce gona da iri."
Mourinho ya jaddada cewa duk da cewa Vinicius Jr yana da nasa kura-kuran, yana ganin yadda ake mu'amala da shi a wasu lokuta a filin wasa ya yi yawa, kuma hakan na sa ya buƙaci ƙarin haƙuri da sarrafa ɓacin ransa.
Ceferin ya ce ya janye daga neman takarar shugabancin Fifa
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban UEFA, Aleksander Ceferin, ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar maye gurbin Gianni Infantino ba, amma ya ce yana sa ran wani ɗan takara zai kalubalanci shugaban na FIFA a watan Maris.
Infantino ya fuskanci kiraye-kirayen yin murabus bayan da ya yi watsi da wani shiri mai cike da ce-ce-ku-ce na sayar da hannun jari a gasar FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu, bayan adawa mai ƙarfi daga sassa daban-daban.
UEFA ce ta jagoranci adawar ga wannan shiri, inda membobinta suka kada kuri'ar kaurace wa gasannin Kofin Duniya idan ba a soke shirin ba. Hukumar ƙwallon ƙafan Turai ta kuma bayyana cewa ta dawo daga rakiyar jagorancin Infantino.
Ceferin, mai shekaru 57, an daɗe ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za su iya kalubalantar Infantino. Sai dai ya ce ba ya da niyyar tsayawa takarar shugabancin FIFA a taron FIFA Congress da za a gudanar a watan Maris na shekarar 2027.
Da yake magana a shirin Rest is Politics Podcast, Ceferin ya ce: "Ba na sha'awar wannan muƙami saboda dalilai biyu. Na farko, ina son UEFA kuma ina son aikin da nake yi a nan. Kuma ina ganin akwai lokacin da ya kamata mutum ya fara more rayuwa."
Ya ƙara da cewa: "Dalili na biyu shi ne, amincina da ƙimata sun fi ƙaruwa sosai idan ba na neman wannan muƙamin."
Ceferin ya ce yana ganin ko dai Infantino mai shekaru 56, ɗan ƙasar Switzerland, zai sauka daga muƙaminsa saboda rashin cikakken goyon baya, ko kuma wani ɗan takara zai fito ya kalubalanci matsayinsa a zaɓen shugaban FIFA mai zuwa.
Ina makomar Mykhailo Mudryk a Chelsea
Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta daina kallon Leeds United a matsayin wurin da za ta tura Mykhailo Mudryk a matsayin aro a halin yanzu.
Leeds na ci gaba da nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gefe, bayan da Chelsea ta yi watsi da tayin farko da kulob ɗin ya gabatar domin karɓarsa aro.
Sai dai Leeds ba ta da niyyar yin gaggawar kulla yarjejeniya kan sharuddan da take ganin ba su yi mata daɗi ba.
Mudryk kuma na samun tayi daga wasu ƙungiyoyin Premier League da kuma kulob-kulob a Turai, ciki har da Strasbourg, wanda ke cikin ƙungiyoyin da abokan hulɗar Chelsea ne.
Kasuwar musayar 'yan wasa ta Premier League za ta rufe ranar Talata, 1 ga Satumba.
Ferran Torres ya fara wasa a PSG da ƙafar dama
Asalin hoton, Getty Images
Gwarzon dan wasan Kofin Duniya Ferran Torres ya farke wa PSG ƙwallaye biyu da aka ci ta 2-0, inda ya taimaka mata ta tashi canjaras da Rennes a wasan farko na Ligue 1.
Torres mai shekaru 26, wanda ya ci ƙwallon nasara lokacin da Spain ta doke Argentina a wasan ƙarshe na Kofin Duniya, ya koma PSG daga Barcelona kan kuɗi kimanin fam miliyan 42.7 a ranar 15 ga Agusta.
Kocin PSG, Luis Enrique, ya sanya Torres cikin wasa a mintina 45 na biyu bayan ƙungiyarsa ta shiga hutun rabin lokaci tana fuskantar barazanar shan kaye.
Tsohon ɗan wasan Manchester City ya maye gurbin wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or, Ousmane Dembele, kuma nan take ya zama gwarzon PSG bayan ya ci ƙwallaye a mintuna na 71 da 82, wanda ya taimaka wa zakarun Faransa kauce wa abin kunya.
PSG ta buga wasa mara armashi a mintina 45 na farko, inda Sebastian Szymanski ya ci wa Rennes kwallon farko a minti na tara. Daga baya Esteban Lepaul ya ƙara ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Sai dai Rennes, wadda ta kammala kakar wasan da ta gabata a matsayi na shida, ta kasa riƙe wannan nasara yayin da Luis Enrique ya yi amfani da ƙwararrun 'yan wasan da ke kan bencin PSG.
Tun farko dai an shirya PSG ta fara kare kambunta ne a gida a birnin Paris, amma an sauya filin wasan zuwa Brittany saboda matsananciyar zafi da kuma lalacewar da filin wasan PSG ya yi.
PSG na neman lashe kofin Ligue 1 karo na shida a jere a wannan kakar, tare da burin lashe kofin Champions League karo na uku a jere.
Barcelona ta ce 'yansanda sun yi amfani da karfi kan magoya bayanta
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta zargi 'yan sanda da yin amfani da karfin da ya wuce kima kan magoya bayanta a lokacin wasan da ta doke Elche da ci 5-0 a ranar Lahadi.
An ga bidiyoyi a shafukan sada zumunta da ke nuna rikici tsakanin 'yan sanda da magoya bayan yayin da suke kokarin shiga filin wasa na Estadio Martinez Valero da ke Elche.
Barcelona ta bayyana cewa, babu wata hujjar daukar matakin yin amfani da karfi wajen kama daya daga cikin magoya bayanta.
Haka kuma Barcelona ta zargi 'yan sanda da kwace tutocin 'Estelada' daga hannun magoya baya; tutocin da masu goyon bayan samun 'yancin yankin Catalonia ke amfani da su, kuma galibi magoya bayan kungiyar ta Barca ke dagawa.
Rikicin Crystal Palace da Mateta na kara dagulewa
Asalin hoton, Getty Images
Sabon salo a rikicin da ke tsakanin Jean-Philippe Mateta da Crystal Palace, wanda a 'yan kwanakin nan ya kasance tamkar tafiyar jirgin ƙasa mai cike da sauye-sauye, ya sake jefa makomar ɗan wasan a kulob ɗin cikin tambaya.
Bayyanawar da BBC Sport ta yi ranar Asabar cewa Mateta na jayayya cewa shekarar ƙarshe da ke cikin kwantiraginsa da Palace ba ta da inganci, tare da matakin da ya ɗauka na kai ƙarar gaban wata kotun sulhu mai zaman kanta ta Premier League da kuma sauraron ƙara a Fifa, ya ƙara sanya lamarin ya zama mai jan hankali yayin da kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ke gab da rufewa.
Duk da cewa Mateta da mashawartansa suna kalubalantar cewa shekarar ƙarshe da ke cikin yarjejeniyarsa ba ta da ɗaurewa a doka, saboda ƙarin shekarar wata zaɓi ce da kulob ɗin ya amince daga cikin ainihin kwantiraginsa na shekaru huɗu da rabi, har yanzu ɗan wasan na ƙasar Faransa yana ƙarƙashin kwantiragi da Crystal Palace.
Kwanaki kaɗan kafin ya fara wasan farko na Palace a Premier League da Everton, Fifa ta yanke hukunci cewa batun ba ya cikin huruminta.
Kuma ko da yake ba a bayyana sakamakon hukuncin kotun sulhu mai zaman kanta ta Premier League da aka yi a kakar wasan da ta gabata ba, kasancewar Mateta har yanzu yana ƙarƙashin kwantiragi da Palace na nuna cewa hukuncin bai zai yi masa dadi ba.
Arbeloa da Alonso abokan juna da za su fafata a Premier
Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da aka tambayi tsohon kocin Liverpool, Rafael Benitez, ko ya taɓa tsammanin tsoffin 'yan wasansa Xabi Alonso da Alvaro Arbeloa za su zama masu horarwa, amsarsa ta kasance kai tsaye ba tare da ɓoye komai ba.
"Alonso, eh. Arbeloa kuwa, ba sosai ba," in ji shi. "A gare ni, Arbeloa ya ba ni mamaki."
Kusan shekaru 20 bayan da Benitez ya haɗa su a Anfield, yanzu su biyun za su fafata a matsayin masu horarwa, yayin da Fulham da Arbeloa ke jagoranta za ta karɓi baƙuncin Chelsea ta Alonso a yau Litinin.
Su biyun sun lashe Kofin Duniya na 2010 tare da Spain, da kuma Kofin Kasashen Turai sau biyu. Haka kuma sun samu nasarori a gasar lig da kofuna na cikin gida bayan sun koma Real Madrid daga Liverpool.
Sun buga wasa tare har tsawon shekaru bakwai a matakin kulob, kuma sun yi wasa a fili guda sau 262 a matakin kulob da ƙasa. Tun bayan sun daina buga wasa, hanyoyin aikinsu sun ci gaba da kasancewa a haɗe.
An ɗaga darajar Arbeloa daga Real Madrid B Castilla zuwa babban ƙungiyar Real Madrid domin maye gurbin Alonso bayan da aka sallame shi daga jagorancin katafaren kulob ɗin na Spain a watan Janairun bara.
An sayar da kwallon da Maradona ya ci da hannu £2.5m
Asalin hoton, Getty Images
Ƙwallon da Diego Maradona ya zura shahararren ƙwallonsa na Hand of God a gasar cin kofin duniya ta 1986 ya samu mai siya a gwanjo kan kuɗi fam miliyan 2.5.
Maradona ya yi fice bayan da ya zura ƙwallon da hannu ta wuce mai tsaron raga Peter Shilton a wasan da Argentina ta doke Ingila da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da na ƙarshe.
Bayan wasan, ya shaida wa manema labarai cewa ya zura ƙwallon ne da kan Maradona, ɗan kuma da hannun uabngiji".
Daga baya Maradona ya sake zura abin da aka fi sani da "ƙwallon ƙarni" (Goal of the Century) a wannan wasa, inda ya yi yanka 'yan wasan Ingila biyar kafin ya sanya ƙwallon a raga ta hannun Shilton.
Ko da yake an sayar da ƙwallon kan dala miliyan 3.3, kwatankwacin fam miliyan 2.5 (£2.5m), a wajen bajakolin Heritage da ke Amurka a ranar Asabar, ana sa ran za ta kai kusan dala miliyan 10, wato fam miliyan 7.3.
Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters kafin gwanjon, Mike Provenzale, wani ƙwararren mai gudanar da gwanjo a Heritage, ya ce: "Wannan abu ne na musamman da babu irinsa. Ana iya cewa shi ne mafi muhimmancin abin tunawa da ya shafi ƙwallon ƙafa da ake da shi a duniya."
Ali Bin Nasser ɗan ƙasar Tunisiya, wanda shi ne alkalin wasan a 1986, ya karɓi ƙwallon Adidas Azteca bayan kammala wasan kuma ya adana ta fiye da shekaru 30.
A shekarar 2023, ya rattaba hannu a wata takarda da ta tabbatar da cewa ita ce kaɗai ƙwallon da aka yi amfani da ita a duk wasan, kuma wasu masu bincike da ke zaman kansu sun sake tabbatar da sahihancinta.
Bin Nasser ya sayar da ƙwallon a shekarar 2022 kan dala miliyan 2.37, kwatankwacin fam miliyan 1.74.
Sabon mamallakin ya sake fitar da ita gwanjo a shekarar 2023, amma ba a sayar da ita ba saboda tayin da aka yi ba su kai ƙimar mafi ƙaranci da aka tsara ba.
Rigar da Maradona ya sanya a wannan wasa ita ma an sayar da ita a gwanjo a shekarar 2022 kan fam miliyan 7.1.