Abin da addinai suka ce kan ranar tashin duniya

Ranar tashin duniya
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

In har kana karanta wannan labari, to lallai kana raye kuma duniya ba ta tashi ba.

Mutane da dama sun yi ta tsammanin wannan rana ta 13 ga watan Nuwamba, ba za mu shaida ta ba, sakamakon yadda wani bincike ya nuna cewar wataƙila "duniya za ta tashi".

Manyan addinai biyu na Musulunci da Kirista na da matsaya mabambanta kan yaushe ne za a yi tashin duniya.

Amma masu bincike uku ne suka rubuta wani bincike, kuma an wallafa shi a mujallar kimiyya ta Amurka mai suna Science a ranar 4 ga Nuwamba, 1960.

Taken binciken shi ne: "Doomsday: Friday, November 13".

Masu binciken sun bayyana cewa idan yawan mutanen duniya ya ci gaba da ƙaruwa da irin saurin da bayanan da suka nazarta na kusan shekara 2,000 suka nuna, to bisa ga hasashensu, yawan al'ummar duniya zai kai matakin da ba za su iya rayuwa a duniyar ba zuwa watan Nuwamba na shekarar 2026.

Dama dai Musulmai suna da masaniya daga nassi daban-daban cewa za a yi tashin duniya ne a ranar Juma'a ne, sai ga shi kuma ranar 13 ta faɗo daidai da wannan rana ta Juma'a, amma dai babu tabbas a kai.

To amma mece ce mahangar addinan nan biyu kan ranar tashin duniya?

Fahimtar Musulunci game da ranar tashin duniya

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Addinin Musulunci ya bayyana cewa babu wanda ya san takamaiman ranar da za a yi tashin alƙiyama sai Allah kaɗai.

Malaman addinin Musulunci sun ce akwai alamomin da sai sun bayyana ne za a gane cewa lokacin tashin duniya ya zo. Ko da yike wasu suna ruwaito wasu nassi cewa ranar Juma'a ce za a yi tashin ƙiyama.

A cikin Suratul A'araf, aya ta 187, Allah ya ce: "Sunã tambayarka game da tashin alƙiyama, yaushe ne faruwarta? Ka ce: Iliminta yana wurin Ubangijina kawai. Babu mai bayyana ta a kan lokacinta sai Shi."

Haka kuma, a Suratu Luƙman, aya ta 34, Allah ya bayyana cewa yana daga cikin abubuwan da iliminsu yake gare Shi kaɗai sanin lokacin tashin alƙiyama.

Wannan yana nufin cewa ko Annabi Muhammad (SAW) bai san takamaiman lokacin da za a yi tashin alƙiyama ba.

  • Waɗanne alamomi ne Musulunci ya bayyana?

A cikin koyarwar Musulunci, an raba alamomin tashin alƙiyama zuwa gida biyu: ƙanana da manya.

Waɗannan su ne alamomin da za su bayyana tun kafin kusantowar tashin alƙiyama. Wasu sun riga sun faru, wasu kuma suna ci gaba da bayyana, yayin da wasu ba su faru ba tukuna.

  • - Yaɗuwar jahilci da raguwar ilimi.
  • - Yawaitar fitintinu da tashe-tashen hankula.
  • - Gasar mutane wajen gina manyan gine-gine.

An kawo wasu daga cikin waɗannan alamomi a cikin hadisai ingantattu, ciki har da Sahihul Bukhari da Sahih Muslim.

Akwai kuma manyan alamomi waɗanda su ne manyan abubuwan da za su faru a lokacin da tashin alƙiyama ya kusanto sosai.

A cikin wani hadisi da Imam Muslim ya ruwaito, Annabi Muhammad (SAW) ya ambaci manyan alamomi guda goma, waɗanda suka haɗa da:

  • - Bayyanar Dujal.
  • - Saukar Annabi Isa ɗan Maryam (AS).
  • - Bayyanar Yajuj da Majuj.
  • - Fitowar hayaki.
  • - Fitowar dabba daga ƙasa.
  • - Fitowar rana daga yamma.
  • - Ruftawar ƙasa a gabas.
  • - Ruftawar ƙasa a yamma.
  • - Ruftawar ƙasa a yankin Larabawa.
  • - Wata wuta da za ta fito daga Yemen, ta kori mutane zuwa wurin taruwarsu.

Musulunci ya yi gargaɗi kan ƙoƙarin tantance takamaiman lokacin tashin alƙiyama ko kuma danganta wasu abubuwan da ke faruwa a duniya da cewa lallai su ne alamomin ƙarshe.

Duk da cewa hadisai sun bayyana alamomin da za su faru, sanin ainihin lokacin tashin alƙiyama yana ga Allah kaɗai.

Fahimtar addinin Kirista kan ranar tashin duniya

Duk da cewa addinin Kirista ya yi imani da dawowar Yesu Almasihu da kuma ƙarshen zamani, Littafi Mai Tsarki bai bayyana takamaiman ranar da za a yi hakan ba. Sai dai ya yi nuni da wasu alamomi da za su iya bayyana a lokacin ƙarshen zamani.

Reverend Ishaku Ashafa, wani malamin addinin Kirista a jihar Kaduna, ya ce za a samu sauye-sauye sosai a yadda mutane ke gudanar da rayuwarsu idan lokacin ƙarshen zamani ya zo.

Ya ce a cikin littafin Daniel, babi na 12, aya ta 4, an yi maganar yadda ilimi zai ƙaru a lokacin ƙarshen zamani. Haka kuma, ya yi nuni da cewa Littafi Mai Tsarki ya yi magana kan yadda mutane za su daina kula da juna a wannan lokaci.

A cikin littafin 2 Timothawus, babi na 3, ayoyi na 1 zuwa 5, an bayyana wasu halaye da za su bayyana a ƙarshen zamani, ciki har da son kai, son kuɗi, rashin biyayya ga iyaye da rashin ƙauna.

Reverend Ashafa ya ƙara da cewa a lokacin dawowar Yesu Almasihu, zai zo domin ceton waɗanda suka yi imani da shi, ya kuma ɗauke su zuwa sama.

"Waɗanda kuma ba su yi imani da shi ba, za a barsu a nan," in ji shi.

Sai dai Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa babu wanda ya san takamaiman ranar ko lokacin da wannan lamari zai faru.

A cikin littafin Matta, babi na 24, aya ta 36, an ambato Yesu yana cewa babu wanda ya san ranar ko lokacin, har da mala'ikun sama, sai Allah kaɗai.

Reverend Ashafa ya ce wannan na nuna cewa duk da kasancewar akwai alamomin da za a iya gani, ba zai yiwu mutum ya san takamaiman lokacin da tashin duniya zai faru ba.

Daga ina wannan labarin ya samo asali?

...

Wannan bincike ya samo asali ne daga masanin kimiyyar lissafi nan haifaffen Austria, Heinz von Foerster, mazaunin Amurka.

Ya gudanar da wannan bincike tare da wasu mutum biyu, Patricia Mora da Lawrence Amiot. Dukkansu uku mambobi ne na Sashen Injiniyan Lantarki na University of Illinois da ke Amurka.

Masu binciken sun yi amfani da kimantawa ta tarihi kan yawan al'ummar duniya. Bayanansu sun kunshi kimantawa 24 da aka tattara daga farkon zamanin Miladiyya har zuwa shekarar 1958.

Sun yi amfani da wadannan bayanai domin fahimtar yadda yawan jama'ar ɗan'adam ya karu a tsawon tarihi.

Masu binciken ba su gina nazarin nasu kan hasashen cewa yawan mutanen duniya na karuwa ne da daidaitaccen kaso ba.

Maimakon haka, sun gabatar da wani tsarin lissafi da ya dogara da manufar karuwar jama'a mai tsanani, wadda aka sani da suna Hyperbolic Growth.

A cikin wannan tsarin, ba wai yawan jama'a kadai ke karuwa ba, har ma da saurin karuwar yana dada habaka yayin da lokaci ke tafiya.

Wannan tsarin lissafin ya ginu ne kan ra'ayin cewa ikon ɗa'adam na mu'amala da wasu, taimakon juna da kuma kulla hadin gwiwa yana taimaka masa wajen shawo kan wasu daga cikin kalubalen muhalli.

Hakan na kara wa dan Adam karfin rayuwa da haihuwa.

Bayan amfani da wannan ka'idar lissafi kan bayanan tarihi, masu binciken sun kammala cewa tsarin nasu zai kai wani matsayi da ake kira singularity a shekarar 2026. Wannan lokacin zai kasance a tsakiyar watan Nuwamban 2026.

Saboda haka ne ranar 13 ga watan Nuwamban 2026 ta zama wani bangare na taken binciken.

Bisa ga tsarin lissafin, a wannan ranar ne yawan mutanen duniya zai kai matakin da ba shi da iyaka a bisa ka'ida idan har aka ci gaba da amfani da irin wadannan sharudda da hasashen ba tare da wani canji ba.

A kallon farko, taken binciken na iya zama kamar wani hasashe ne game da karshen duniya, amma hakikanin ma'anarsa ta bambanta gaba daya.

Masu binciken ba su yi hasashen cewa wani babban dutse zai bugi duniya daga sararin samaniya ba, ko cewa rana za ta fashe, ko kuma girgizar kasa da aman wuta za su haddasa gagarumin bala'i.

Haka kuma ba su ayyana wata ranar da dan Adam zai bace sakamakon wata masifar halitta ba.

A hakikanin gaskiya, sun yi amfani da kalmar "doomsday" ne domin bayyana wani yanayi na lissafi da ake hasashe, inda yawan jama'a zai kai matakin da ba shi da iyaka bisa ga ka'idarsu.

Wannan kuwa ba abu ne mai yiwuwa a zahirin duniya ba.