Abubuwa 5 da ke iza wutar rikicin manoma da makiyaya a ƙarshen damina

xxx
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A duk lokacin da damina ke gab da ƙarewa a Najeriya, ana yawan samun rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a sassa daban-daban na ƙasar.

Rikice-rikicen kan jawo asarar rayuka da dukiyoyi, tare da haddasa ƙaura da ƙarin tashin hankali a wasu yankuna.

Ƙarshen damina wani lokaci ne da manoma ke girbe amfanin gonakinsu, yayin da makiyaya kuma ke komawa arewacin ƙasar daga kudanci bayan watanni na zaman damina.

A irin wannan lokaci ne dabbobi kan shiga gonaki su lalata amfanin gona, lamarin da ke haddasa saɓani tsakanin manoma da masu kiwon dabbobi.

Sau da dama, ƙaramin saɓani kan rikiɗe zuwa rikici mai tsanani idan ba a shawo kansa cikin gaggawa ba.

Haka kuma, masana harkokin tsaro da noma na nuna cewa rashin bin tanadin hanyoyin kiwo da kuma gazawar warware rikice-rikicen cikin lokaci na daga cikin abubuwan da ke ƙara rura wutar rikicin.

Kodayake gwamnatoci a matakai daban-daban sun ɗauki matakai don rage yawan irin waɗannan rikice-rikice, har yanzu ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a wasu yankuna musamman a lokacin da damina ke ƙarewa.

Me ya sa makiyayan Najeriya ke ƙaura?

Makiyayi

Alhaji Baba Usman Ganzerma shugaban ƙungiyar makiyayan Najeriya ta MACBAN ya ce akwai abubuwa da dama da ke haddasa ƙauran makiyaya zuwa sassan Najeriya daban-daban.

  • Nema wa dabbobi abinci
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban na MACBAN ya ce abu na farko da ke janyo ƙauran makiyaya musamman daga arewaci zuwa kudanci shi ne nema wa dabbobinsu abinci.

''A arewa lokacin rani na da tsayi, don haka dabbobinsu kan rasa abincin da za su ci a arewa kan haka ne suke tafiya kudancin ƙasar, wadda damina ke sauka da wuri, domin samun ciyayi da ruwan sha ga dabbobin nasu'', in ji shi.

  • Rashin wuraren kiwo

Wani dalilin da ke sa makiyan yin ƙaura daga arewacin Najeriya zuwa kudanci shi ne rashin wuraren kiwo a arewa.

''Galibi a arewa kusan duka filayen kiwon gonaki ne, don haka idan damina ta sauka manoma suka yi shuka babu wuraren kiwo, don haka dole su tafi wuraren da babu gonaki domin sama wa dabbobinsu abinci'', in ji Baba USman Ganzerma

  • Sauyin yanayi

Batun sauyin yanayi na daga cikin abubuwan da ke janyo ƙauran makiyaya daga wasu yankunan Najeriya zuwa wasu.

''Yayin da yankin arewacin ƙasar ke ci gaba da fuskantar tasirin sauyin yanayi, an samu raguwar saukar ruwan sama a wasu yankunan, wani abu da ke tilasta wa makiyayan yin ƙaura zuwa kudanci'', in ji shi.

Baba Usman Genzarma ya ƙara da cewa sauyin yanayi ya sa wurare da yawa da ke tara ruwa a baya, yanzu sun ƙafe, lamarin da ya tilasta wa makiyayan yin ƙaura.

  • Matsalar tsaro

Wani dalilin da ke janyo ƙauran makiyaya musamman daga arewacin Najeriya zuwa kudanci a yanzu shi ne matsalar tsaro.

''Matsalar tsaro a wasu yankunan arewacin Najeriya ta tilasta wa makiyaya da dama tserewa daga garuruwansu zuwa kudancin Najeriya, wasu ma har zuwa ƙasashe maƙwabta'', in ji shi.

  • Annobar cutukan dabbobi

Shugaban ƙungiyar makiyayan ya ce wani dalilin ƙaurar makiyaya shi ne annobar wasu cutukan da ke kama dabbobi, a wasu lokutan shekara.

A arewa idan rani ya yi rani akan samu wasu tsuntsaye da ke addabar shanu, inda suke sauka a kansu suna totsar jininsu, hakan na sa makiyaya su yi ƙaura domin guje wa tsuntsayen.

''Haka idan damina ta kusan zuwa ƙarshe a yankin kudancin Najeriya a kan samu ɓullar annobar ƙudan tsando da ke yawan cizon dabbobin, wanda hakan kan tilasta wa makiyaya komawa ɓangaren arewacin ƙasar, saboda a can babu annobar'', in ji shi.

Me ke janyo rikici tsakanin manoma da makiyaya?

Galibi dai an fi samun rikicn makiyaya da manoma a lokacin da makiyayan ke komawa arewacin ƙasar daga kudanci inda suka shekara.

Wani abu da Baba Usman Usman Genzarma ya danganta da nome hanyoyin da makiyayan ke bi domin yin ƙaurar tasu.

''A lokacin da suke wucewa su kan bi labin da aka keɓe musu, domin wucewa, amma a lokacin da suka tashi komawa sai su tarar an nome, to idan suka ce za su wuce ne sai rigima ta kaure'', in ji shi.

To sai a lokuta da dama manoman kan zargi makiyayan da cinye musu amfanin gona da gangan.

''Akwai sakaci daga ɓangaren makiyayan a wasu lokuta, za ka tarar da shanu fiye da 200 amma yara uku kawai ke binsu suna kula da su, ka ga ai dole a samu matsala'', a cewar sarkin noman Wurko a jihar Taraba, ɗaya daga cikin jihohin da ake yawan samun rikicin manoma da makiyaya a Najeriya.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin matsalolin da ke haifar da rikicin shi ne babu wasu dokokin da suka iyakance wuraren kiwo a ƙasar.

Me gwamnatoci ke yi don magance matsalar?

Gwamnatoci a matakai da jihohi daban-daban kan yi iƙirarin ɗaukar matakan magance matsalar tun kafin faruwarta.

Gwamnatin jihar Taraba ta ce tana ɗaukar matakan riga-kafi tun faruwar lamarin.

Alhaji Tanko Babban Andamin, mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin noma ya ce gwamnatin jihar na shirya gangamin wayar da kai ga duka ɓangarorin.

''Gwamnati na tabbatar da cewa duka hanyoyin da makiyaya ke bi don zuwa kiwo ba a nome su ba'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar kan shirya gangamin wayar da kai na zaman tare da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyayan jihar.