Me kalaman shugaban INEC ke nufi kan takarar Atiku a 2027?

Asalin hoton, INEC/Atiku
Kalaman da shugaban hukumar zaɓen Najeriya, INEC Joash Amupitan kan cancatar takarar jagoran adawar Najeriya Atiku Abubakar sun sake haifar da tambayoyi game da takararsa a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Da yake jawabi a cibiyar Chatham House da ke birnin Landan a ranar Alhamis, Amupitan ya amsa wasu tambayoyi da aka yi masa kan takarar Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027 la'akari da hukuncin babbar kotun tarayya na makon da ya gabata.
A makon da ya gabata ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin ADC tsagin David Mark tare da duka matakan da tsagin ya ɗauka.
Tuni kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ya ce ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin neman ta dakatar da hukuncin kotun tarayyar, wanda Amupitan ya ce idan suka gaza samun nasara wajibi kan INEC ta cire sunansa.
"Idan a ƙarshe suka gaza, wajibi ne a kaina ƙarƙashin sashe na 285 na kundin tsarin mulkin Najeriya, in bi duk wani umarnin kotu, musamman idan hukuncin ya fito daga Kotun Ƙoli," in ji shi.
Ya jaddada cewa hukumar INEC ba ta da wani zaɓi illa aiwatar da hukuncin kotu, ba tare da la'akari da tasirin da hakan zai iya yi a fagen siyasa ba.
Duk da tabbatar da aniyar INEC na mutunta bin doka da oda, shugaban hukumar ya nuna damuwa kan yawaitar shari'o'in da ake shigarwa gaban kotuna kafin zaɓe, waɗanda ke barazana ga shirye-shiryen hukumar na gudanar da zaɓen Janairun 2027.
Me kalaman ke nufi a shari'an ce?
Tun bayan yanke hukuncin ne ƴanƙasar da dama ke ta ɗora ayar tambayoyin cewa me hakan ke nufi a shari'ance.
Kan haka ne muka tuntuɓi Barista Sanusi Musa babban lauya mai muƙamin SAN, wanda kuma ya ce tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa wajibi kowace hukuma da ɗaiɗaikun ƴan Najeriya su yi biyayya ga umarnin kotu.
''Sashe na 287 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa duk wata hukuma da ɗaiɗaikun ƴan Najeriya, idan kotu ta yanke hukunci dole ne a bi shi'', in ji shi.
Babban lauyan ya kuma ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa duk wani hukuncin kotu, walau kotun tarayya ko ta ɗaukaka ƙara da ma kotun ƙoli da ma sauran kotunan jihohi, dole ne a bi su.
''Kuma duk mutumin da kotu ta ɗora wa wajibcin aiwatar da hukuncin, to wajibi ya aiwatar da hukuncin'', in ji shi.
Ɗaukaka ƙara na hana aiwatar da hukunci?

Asalin hoton, Getty Images
Wasu da dama dai na ganin kalaman na shugaban INEC da cewa ba abu ne da zai yiwu ba a yanzu kasancewa Atiku da ADC sun ɗaukaka ƙara.
To amma Barista Sanusi ya ce ɗaukaka ƙara ba ya hana aiwatar da hukuncin da kotun ƙasa ta yi.
''A duk lokacin da wata kotu ta yi hukunci, to a ƙa'ida wannan hukunci shi ne hukunci, har sai idan wanda ya ɗaukaka ƙarar ya nemi kotu ta bayar da damar dakatar da aiwatar da hukuncin, har sai abin da kotun sama ta ce'', in ji shi.
Ƙwararren lauyan ya kara da cewa idan har aka nemi kotu ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin, to galibi takan yi hakan, har zuwa lokacin da kotun sama za ta yanke hukunci.
Wane tasiri kalaman za su yi ga takarar Atiku?

Asalin hoton, Atiku Abubakar/FB
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kalaman na shugaban INEC sun sake tayar da ƙura a siyasance, inda wasu ke ganin hakan zai shafi ƙoƙarin Atiku a yaƙin neman zaɓen da yake yi.
Amma masana harkokin siyasa na ganin kalaman na shugaban INEC ba sabon abu ba ne.
Sai dai Farfesa Abubakar Kari, wanda masanin harkokin siyasa ne a Jami'ar Abuja ya ce wannan ba sabon abu ba ne, kuma dama babu abin da zai faɗa da ya wuce wannan.
''Dama sun sha faɗin cewa su suna bin umarnin kotu ne, kuma a halin da ake cikin yanzu ba abin da zai faɗa sama da hakan'', in ji masanin siyasar Najeriya.
Dangane da tasirin da kalaman za su yi ga ƙoƙarin Atiku kuwa na yaƙin neman zaɓensa, Farfesa Kari ya ce ko shakka babu kalaman na shugaban INEC za su shafi Atiku a siyasance.
''Hakan zai rage masa ƙwarin gwiwa shi da magoya bayansa da kuma jam'iyyarsa ta ADC, domin idan ka duba a baya yadda ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a Sokoto da kuma shirin da ya yi na karaɗe jihohin ƙasar'', in ji shi.
Masanin siyasar ya ƙara da cewa hukuncin babbar kotun tarayyar zai sanya wa Atiku da magoya bayansa fargaba.



























