Me ya sa Seyi Tinubu ke 'zaƙewa' kan takarar mahaifinsa?

Asalin hoton, Seyi Tinubu News/FB
- Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Tun bayan hawan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulkin ƙasar a shekarar 2023, ɗansa Seyi Tinubu, ke ƙara fitowa fili wajen shirya goyon bayan siyasa ga mahaifinsa.
Daga kafa da jagorantar ƙungiyoyin matasa, zuwa ziyartar jihohi da ganawa da masu ruwa da tsaki, Seyi ya zama ɗaya daga cikin fitattun mutanen da ke fafutukar ganin Tinubu ya sake samun wa'adin mulki.
To sai dai ganin irin rawar da yake takawa ta zama wani baƙon abu a Najeriya a ga 'ya'yan shugabannin ƙasar dumu-dumu a cikin lamurran siyasa, hakan ya haifar da gagarumar muhawara tsakanin 'yan Najeriya da ke da tambayoyin akan me ya sa Seyi Tinubu ya dage kan wannan takara ta mahaifinsa? Wace rawa yake takawa a cikin ƙungiyoyin da ke goyon bayan mahaifinsa, kuma me ya sa yake yawan kai ziyara a jihohin Najeriya?
Matsayinsa a fafutukar sake zaɓen mahaifinsa

Duk da cewa Seyi Tinubu ba zaɓaɓɓen jami'in gwamnati ba ne, kasancewarsa ɗan shugaban ƙasa da kuma muhimmin jigo a ƙungiyoyin da ke goyon bayan gwamnatin mahaifinsa ya sanya shi cikin mutanen da ake lura da ayyukansu a siyasar Najeriya.
Ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da yake da muhimmiyar rawa a cikinta ita ce City Boy Movement, wadda kuma shi ne majiɓincinta.
Ƙungiyar ta fara bayyana ne a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023, inda ta mayar da hankali kan tattara matasa da sauran magoya bayan Bola Tinubu domin tallafa wa takararsa.
Yanzu da ake tunkarar zaɓen 2027, ƙungiyar ta sake ƙarfafa ayyukanta, inda take faɗaɗa rassanta da tsarin shugabancinta a jihohin Najeriya.
A watan Yulin 2026, Seyi Tinubu ya halarci taron ƙasa na City Boy Movement a Abuja, inda ya bayyana cewa ƙungiyar ta wuce matsayin dandali na yaƙin neman zaɓe, ta koma wata babbar hanyar haɗa matasa da sauran al'umma domin shiga harkokin ƙasa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wajen taron, Darakta Janar na ƙungiyar, Francis Shoga, ya bayyana cewa suna da burin tattara ƙuri'u miliyan 10 na matasa domin tallafa wa sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.
Masana kimiyyar siyasa sun bayyana cewa shigar Seyi lamurran siyasa dumu-dumu ba abin zargi ba ne kasancewar an ga irin haka a wasu ƙasashen duniya kamar Amurka.
Farfesa Yahaya Tanko Baba, malami ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto ya ce,"zagayen da yake yi a Najeriya zamu iya cewa baƙon abu ne, amma idan mun dubaga yadda siyasar wasu ƙasashe musamman Amurka da zamu iya cewa ita ce ta yi fice ga abin da ya shafi dimukuraɗiyya, 'ya'ya ko dangi su yi fice a siyasa a lokaci guda ba wani abu ne mai ban mamaki domin akwai fitattun 'yan siyasa a ƙasar Amurka waɗanda su da ɗiyansu sun yi shugavan ƙasa kuma 'ya'yansu sun yi shugaban ƙasa".
Farfesa Yahaya Tanko Baba ya bayar da misalin tsafaffin shugabannin Amurka da suka haɗa da "Resovelt da J.F. Kennedy da Geroge W. Bush waɗanda fitattun 'yan siyasa ne da suka yi shugabancin kuma 'ya'yansu sun yi shugaban ƙasa", in ji.
Ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Seyi

Asalin hoton, City Boy Movement
City Boy Movement ba ita ce kaɗai hanyar da ake amfani da ita wajen yaɗa saƙon siyasar Shugaba Tinubu ba.
Seyi Tinubu yana da alaƙa da wata ƙungiya mai suna Relax Tinubu Is Fixing Nigeria, wadda ke ƙoƙarin bayyana manufofin gwamnatin mahaifinsa da kare su daga suka.
Waɗannan ƙungiyoyi suna amfani da tarurruka da shirye-shiryen wayar da kan jama'a da ziyarar wurare da kafafen sada zumunta wajen isar da saƙonninsu.
Babban abin lura shi ne yadda ake ƙoƙarin mayar da matasa gimshiƙin wannan fafutuka, musamman saboda muhimmancin da ƙuri'unsu ke da shi a zaɓe.
A taron da Shugaba Tinubu ya yi da shugabannin City Boy Movement a Fadar Shugaban Ƙasa ranar 19 ga Oktoban 2026, ƙungiyar ta sake jaddada burinta na samun ƙuri'u miliyan 10 na matasa a zaɓen 2027
Me yasa yake ziyartar jihohi

Asalin hoton, City Boy Movement
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi fito da rawar Seyi Tinubu a siyasar yanzu shi ne yawan ziyartar jihohi da ganawa da sarakuna da shugabannin ƙungiyoyi da dama a ƙasar.
A farkon watan Nuwamban 2026, an ruwaito cewa ayyukan City Boy Movement sun bazu zuwa jihohin Jigawa, da Bauchi da Gombe da Adamawa da Taraba, da kuma wasu jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Ziyarce-ziyarcen da take yi na daga cikin dabarun faɗaɗa tsarin ta har zuwa ƙananan hukumomi da al'ummomin da ba sa manyan biranen jihohi.
Saboda haka, ziyarce-ziyarcen na iya zama wata hanya ta gina alaƙa da shugabannin yankuna da ƙarfafa masu goyon baya da kuma tabbatar da cewa saƙon ƙungiyar ya isa ga mutane da dama.
A ranar 10 ga Nuwamban 2026 ma, an ruwaito ziyarar Seyi Tinubu ga Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle, a gidansa da ke Abuja. Tattaunawar ta shafi ƙarfafa goyon bayan siyasa da shirye-shiryen zaɓen 2027.
Shin ko akwai alamun Tinubu na muradin ɗansa ya gaje shi?
Wani abin lura game da ziyarce-ziyarcen Seyi Tinubu a faɗin Najeriya shi ne yadda yake samun karɓuwa daga sarakunan gargajiya, inda wasu masarautu har suke ba shi sarautun gargajiya.
Waɗannan naɗe-naɗe sun ja hankalin mutane inda da dama ke ƙorafin yadda kamar sarakunan na jefa kansu ne a cikin siyasa.
Masanin ya ce, "watakila matakin ziyarce-ziyarcen ga sarakuna da Seyi ke yi, ba ya rasa alaƙa da yadda mahaifinsa ke son kimtsa shi ya gaje shi nan gaba, domin shi kansa Tinubu ya daɗe yana gina wata babbar daula ta siyasa wanda wannan ne ya yi amfani da shi a matsayin matakala har ya kai ga shugabancin ƙasa a yau".
Haka kuma masanin ya ce ga dukkan alamu shugaba Tinubu na ɗora Seyi ne bisa wannan turba inda ya ke ganin shi ya fara manyanta, shekaru suna ja kuma ba ya son wannan ginin na siyasa da ya yi ya rushe, kan haka abubuwan da Seyi ke yi a yanzu tamkar yana wakiltar mahaifin nasa sne shugaba Bola Ahmed Tinubu," in ji shi.
Wannan alaƙar kuwa ta kai ga ya samu sarautu da Alaafin na Oyo da kuma Sarakin Gwandu suka ba shi.
Sai dai abin da ke da muhimmanci a duba shi ne irin rawar da waɗannan alaƙoƙi da masarautu za su taka wajen faɗaɗa tasirin ƙungiyoyin da ke goyon bayan takarar mahaifinsa a zaɓen 2027.
1. Ɗan Zakin Gwandu – Jihar Kebbi

Asalin hoton, Seyi Tinubu News/FB
A ranar 11 ga Nuwamban 2026, Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya naɗa Seyi Tinubu sarautar Ɗan Zakin Gwandu a fadar masarautar da ke Birnin Kebbi.
Naɗin ya biyo bayan ziyarar da ya kai jihar tare da tawagar City Boy Movement domin neman albarkar sarauta ga ayyukan ƙungiyar.
Okanlomo na ƙasar Yarbawa – Jihar Oyo

Asalin hoton, Seyi Tinubu News/FB
Haka kuma a ranar 21 ga Disamban 2025, Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade I, ya naɗa shi sarautar Okanlomo na ƙasar Yarbawa a wani gagarumin bikin sarauta da aka gudanar a fadar Alaafin da ke garin Oyon jihar Oyo.
Naɗin ya jawo hankalin jama'a saboda matsayin Alaafin na Oyo a al'adun Yarbawa da kuma muhimmancin sarautar da aka bai wa Seyi Tinubu. Kalmar Okanlomo tana ɗauke da ma'anar wanda ake ganin shi a matsayin ɗan da ake ƙauna, yayin da sarautar ke da alaƙa da girmamawa da wakilcin al'adun Yarbawa.
Me ya sa ya dage kan ganin mahaifinsa ya sake takara?
Akwai dalilai da dama da za su iya bayyana irin wannan jajircewa ta Seyi Tinubu, duk da cewa bai kamata a ɗauki waɗannan a matsayin dalilan da ya bayyana da bakinsa ba sai an samu cikakken bayani daga gare shi.
Na farko, akwai alaƙar iyali da siyasa, domin mahaifinsa ne shugaban ƙasar da yake fafutukar ganin ya ci gaba da mulki.
Na biyu, Seyi yana daga cikin mutanen da suka taka rawa wajen gina ƙungiyoyin goyon bayan Tinubu tun kafin zaɓen 2023, don haka fafutukar 2027 na iya zama ci gaba da aikin da aka fara a wancan lokaci.
Na uku, ƙungiyoyin da yake da alaƙa da su suna ganin cewa yaɗa manufofin gwamnatin Tinubu da tattara matasa na da muhimmanci wajen ƙarfafa goyon bayan shugaban ƙasa.
A gefe guda kuma, fitowar ɗan shugaban ƙasa a irin wannan matsayi ta jawo tambayoyi daga masu lura da siyasa, inda Farfesa Yahaya Tanko Baba ya ce, "dukkan alamomi sun bayyana cewa shigarsa tsundum na nuna yadda nan gaba shi ma yake son taka rawar da nan gaba shi ma zai iya maye gurbin mahaifinsa ko kuma samun wani babban muƙami a wannan gwamnati, abin da kuma ba a saba da shi ba a Najeriya da sauran ma wasu ƙasashen Afirka".




























