Arsenal ta shiga zawarcin Scott, Manchester United na farautar ƴan wasan baya

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta bi sahun Chelsea da Liverpool wajen tuntuɓar Bournemouth kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Ingila mai shekara 23, Alex Scott, wanda kwangilarsa za ta ƙare a lokacin bazara na shekarar 2028. (i Sport)
Manchester United ta ƙara sunayen Nathan Collins, ɗan wasan baya mai shekara 25 da ke buga wa Brentford da Jamhuriyar Ireland wasa, da kuma Calvin Bassey, ɗan wasan Najeriya mai shekara 26 da ke buga wa Fulham, a cikin jerin ƴan wasan baya da take son ɗauka. Jerin ya kuma ƙunshi Jarrad Branthwaite, ɗan wasan baya mai shekara 24 da ke buga wa Everton da Ingila wasa.(Mail)
Idan Mauricio Pochettino ya zama kocin Manchester United, hukumar ƙwallon ƙafa ta Amurka (US Soccer) na son tsohon kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya maye gurbinsa a matsayin babban kocin tawagar maza ta Amurka. (Talksport)
Chelsea da Real Madrid da Atletico Madrid na sa ido kan ɗan wasan tsakiya na Arsenal, Martin Zubimendi, mai shekara 27, da fatan kammala cinikin ɗan wasan na Spain a watan Janairu. (Independent)
Sai dai, Zubimendi ya bayyana cewa yana "farin ciki" a Landan kuma ya yi mamakin jita-jitar da ake yaɗawa game da makomarsa, kasancewar bai tuntuɓi kowa ba game da barin ƙungiyar ba. (Marca)
Liverpool na shirin miƙawa Trey Nyoni, mai shekaru 19, sabuwar kwangila a matsayin lada kan rawar da ya ke takawa a kakar wasa ta bana, ɗan wasan tsakiyar dai ya na buga wa tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekaru 20 wasa. (GiveMeSport)
Bournemouth da Everton da Nottingham Forest duk sun shiga zawarcin ɗan wasan gaba na Vasco da Gama, Andres Gomez, mai shekara 24, inda ƙungiyar ta Brazil ta sanya farashin kusan fam miliyan 17 kan ɗan wasan.(ESPN)
Brentford ta shirya ƙin amincewa da duk wani yunƙuri daga Liverpool na neman ɗaukar ɗan wasan baya, El Hadji Malick Diouf, mai shekara 21. (Football Insider)
Aston Villa na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Chelsea, Romeo Lavia, mai shekara 22, kasancewar Unai Emery yana matuƙar sha'awar ɗan wasan na Belgium. (Fussball News)
Juventus na shirin ɗaukar ɗan wasan Manchester City kuma ɗan ƙasar Algeria, Rayan Ait-Nouri, mai shekara 25, a matsayin aro a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport)
Sai dai, Barcelona ma na sha'awar Ait-Nouri, duba da cewa ɗan wasan Spain mai shekaru 23, Alejandro Balde, na iya barin ƙungiyar a lokacin kasuwar musayar ƴan wasa ta hunturu. (Sport)
Barcelona ta nuna sha'awa kan ɗan wasan baya na Chelsea da Ingila, Levi Colwill, mai shekara 23, amma Chelsea ta dage cewa ba za ta sayar da shi ba. (Football Insider)



























