Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal na harin Endrick, Newcastle da Sunderland na zawarcin Beljo
Arsenal na harin ɗan wasan Real Madrid Endrick don ganin ta ɗauko shi a watan Janairu, saboda alaƙar da ke tskanin Andrea Berta da hukumar da ke kula da ɗan wasan. (Talksport)
Arsenal na fusknatar gogayya daga Roma da Sporting wajen ɗaukar Endrick ɗin, waɗan da dukkan su na son ɗaukar ɗan wasan a mastayin aro, har zuwa ƙarshen kakar wasa, yayin da ɗan wasan bai yanke barin Real Madrid. (AS - in Spanish)
Manchester United ta ƙara ɗan wasan Brentford Nathan Collins, da takwaransa na Fulham kuma ɗan Calvin Bassey, ciki waɗan da za su iya siye a watan Janaiaru. (Mail - subscription required)
Arsenal na zawarcin ɗan wasan Atletico Madrid Alex Baena, da na RB Leipzig Antonio Nusa, sai na Bournemouth Eli Junior Kroupi. (Independent)
Jeremie Frimpong zai ci gaba da zama a LIverpool har zuwa ƙarshen kakar wasa, sai dai ana cewar ɗan wasan zai iya komawa audiya da taka leda. (Teamtalk)
Frimpong ba shi da sha'awar komawa Al-Hilal da ke Saudiyya , sai dai Liverpool za ta san ya masa kuɗi mai tsoka a kakar siyar da ƴan wasa,a mma ba a Janairu ba. (Football Insider)
Ian Maatsen, da takwaransa na Argentine Emiliano Buendia, da na Belgium Amadou Onana, da Ross Barkley, na cikin waɗan da ake sa ran za su sabunta kwantaraginsu da Aston Villa a nan gaba. (Telegraph - subscription required)
Newcastle ba zata matsa ba wajen ɗauko ɗan wasan Al-Ahl Ivan Toney ba, duk da cewar a baya ya taka leda a ƙungiyar a tsakanin 2015-18 a ƙarƙashin mai horar da ƙungiya r ayanzu a lokacin da ya ke chan Saudiyyar. (The I - subscription required)
Newcastle, da Sunderland da Leeds sun bi sahun Manchester United, da Brighton, Dion Beljo. (Teamtalk)
Chelsea na duba yiwuwar barin Jamie Gittens ya tafi a masatyin ɗan wasan aro a watan Janaiaru zuwa ƙungiyoyin d ake buga gasar Firimiya da ya ke so.. (Football Insider)
Everton na harin ɗan wasan Napoli kuma tsohon ɗan wasan Manchester City Kevin de Bruyne. (Calciomercato - in Italian)
Newcastle da Leeds na zawarcin ɗan wasan Coventry Jack Rudoni. (Teamtalk)
Fulham da Coventry na son daukar dan wasan Real Betis Rodrigo Riquelme. (4-4-2.ch - in German)
Tsohon mai tsaron ragar Manchester United David de Gea, zai bar Fiorentina idan kwantaraginsa ya ƙare a ƙarshen shekara. (Corriere dello Sport - in Italian)