Man United da Man City na hamayya kan Gusto, Liverpool na neman Vuskovic

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United da Manchester City na shirin fafatawa don ɗaukar ɗan wasan baya na Chelsea da tawagar Faransa, Malo Gusto, mai shekara 23. (Talksport)

Liverpool na sanya ɗan wasan baya na Brighton, Luka Vuskovic mai shekara 19, a cikin jerin ƴan wasan da ta ke son ɗauka a bazara mai zuwa, inda ƙungiyar ta Brighton ke kimanta ɗan wasan na Croatia a kan kusan fam miliyan 80. (Florian Plettenberg)

Fulham ce ke kan gaba wajen zawarcin ɗan wasan gefe na Real Betis kuma ɗan ƙasar Spain, Rodrigo Riquelme, mai shekara 26. (Teamtalk)

Everton na iya zawarcin ɗan wasan tsakiya na Tottenham Hotspur, Conor Gallagher mai shekara 26, idan ƙungiyar ta arewacin London ta amince da barin ɗan wasan na Ingila ya koma wata ƙungiyar a watan Janairu. (Football Insider)

Ƙungiyar PSV ta ƙasar Netherlands ta fara tattaunawa da ɗan wasan tsakiya na Napoli kuma ɗan ƙasar Belgium, Kevin de Bruyne, mai shekara 35, game da yiwuwar komawa ƙungiyar a watan Janairu. (Il Mattino)

Tottenham da Juventus na nuna sha'awar ɗaukar dan wasan tsakiya na AC Milan, ɗan ƙasar Faransa Youssouf Fofana, mai shekara 27, wanda a yanzu yake buga wasa a Sevilla a matsayin aro. (Calciomercato)

Tsohon kocin Aston Villa, Dean Smith—wanda a yanzu yake horar da ƙungiyar Charlotte FC ta gasar MLS—yana sha'awar sake yin aiki tare da tsohon dan wasansa Jack Grealish, mai shekara 31. Sai dai, albashin ɗan wasan na Ingila—wanda a yanzu yake buga wa Everton wasa a matsayin aro daga Manchester City—na iya zama babban cikas. (Football Insider)

Ɗan wasan tawagar ƙasar Amurka, Folarin Balogun—ɗan wasan gaba na Monaco mai shekaru 25, wanda ya kusan komawa Everton a ranar ƙarshe ta kasuwar saye da sayar da ƴan wasa a bazarar da ta gabata—yana ɗaya daga cikin waɗanda ake sa ran za su zama sabbin ƴan wasan farko da Mauricio Pochettino zai kawo Manchester United. (Teamtalk)

Leeds United na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke sanya ido sosai kan ɗan wasan gaba na Middlesbrough kuma ɗan tawagar Ingila ta ƴan kasa da shekara 21, Will Lankshear, mai shekara 21. Ɗan wasan ya nuna bajinta a gasar Championship tun bayan komawarsa ƙungiyar daga Tottenham Hotspur a lokacin bazara. (Football Insider)

Newcastle United da Sunderland duk suna sa ido kan ɗan wasan tsakiya na Sheffield United kuma ɗan tawagar Ingila ta ƴan ƙasa da shekara 21, Sydie Peck, mai shekara 22. (Teamtalk)

Ɗan wasan gefe na Tottenham, Mikey Moore, mai shekara 19, na iya komawa ƙungiyar Rangers, yayin da Spurs ke tunanin kawo ƙarshen yarjejeniyar aro da ɗan wasan ke yi a ƙungiyar Cologne a watan Janairu. (Teamtalk)

Barcelona ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan tsakiya na ƙasar Spain, Gavi, mai shekara 22, duk da cewa ƙungiyoyin Bayern Munich da Napoli na nuna sha'awar ɗaukar sa. (Marca)