Me ya sa Ghana ta sabunta takardun kuɗinta kuma mene ne bambancinsu da tsoffin?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Babban Bankin Ghana ya sanar da cewa zai fara fitar da sabbin takardun kuɗin ƙasar domin amfani da su tun daga watan Disamba mai zuwa.

A cewar babban bankin, sabbin takardun kuɗin na cedi sabunta fasali ne na takardun kuɗin da ake amfani da su a yanzu, waɗanda har yanzu za su ci gaba da kasancewa halastattun kuɗaɗen mu'amala.

An sanya wa sabbin takardun kuɗin suna "Heritage Series".

Babban bankin ya ce an shafe fiye da shekara 20 ana amfani da zane da fasalin takardun kuɗin da ake da su a yanzu, lamarin da ya sa hukumomi suka ga lokaci ya yi da za a sake fasalta su.

A halin yanzu, Ghana na da nau'o'in takardun kuɗi takwas: cedi 1, cedi 2, cedi 5, cedi 10, cedi 20, cedi 50, cedi 100 da kuma cedi 200.

Sabbin takardun kuɗin za su kasance cikin waɗannan nau'o'i ne.

Sai dai babban bankin ya bayyana cewa ba zai ƙirƙiro wani sabon nau'in takardar kuɗi ba.

Ya kuma jaddada cewa: "Darajar kuɗin cedi ba ta sauya ba."

Yaushe za a fara amfani da sabbin takardun?

Babban Bankin Ghana ya ce zai fara sanya sabbin takardun kuɗin cedi cikin harkokin kasuwanci daga ranar 1 ga watan Disamban shekarar 2026.

Bankin ya kuma bayyana cewa zai gudanar da gangamin wayar da kan jama'a a faɗin ƙasar domin taimaka wa mutane su fahimci sabbin alamomi da siffofin tsaro da ke jikin sabbin takardun kuɗin.

Da yake ƙaddamar da sabbin kuɗaɗen, Shugaban Ghana, John Mahama, ya yi kira ga 'yan ƙasar da su riƙa ɗaukar kuɗin cedi da alfahari tare da ci gaba da amincewa da shi.

"Ku riƙa ɗaukar kuɗin cedi da alfahari, kuma ku ci gaba da tabbatar da amincewar da aka gina a kansa domin ya ci gaba da yi wa Ghana hidima cikin aminci da inganci ga tsararraki masu zuwa," in ji shi.

Abubuwa da ke jikin sabbin takardun kuɗi

1. Takardar cedi 1

Takardar kuɗin cedi 1, wadda ita ce mafi ƙanƙantar daraja, na ɗauke da hoton Agnes Oforiwa Tagoe-Quarcoopome, wadda ke wakiltar mata 'yan kasuwa da gudunmawar da suke bayarwa ga tattalin arzikin ƙasar.

Agnes fitacciyar 'yar kasuwar yadi ce a Accra kuma sarauniyar kasuwa a shekarun 1940.

Ita ce mace ta farko daga cikin matan kasuwa da ta buɗe asusun banki a lokacin.

A bayan takardar kuɗin akwai hoton Kasuwar Makola da kuma goro, waɗanda ke nuna wadatuwa da haɗin kai.

2. Takardar cedi 2

Takardar cedi 2 na wakiltar bangaskiya da addini a Ghana, inda aka sanya hoton Cardinal Peter Dery, ɗaya daga cikin manyan jagororin cocin Katolika a ƙasar.

Shi ne bishop na farko na Wa, daga baya kuma ya zama Archbishop na Tamale.

A bayan takardar akwai hoton Masallacin Larabanga, wanda ake ɗauka a matsayin mafi tsohon masallaci a Ghana kuma ɗaya daga cikin tsofaffin masallatai a yammacin Afirka.

Har ila yau takardar na ɗauke da hoton Nyame Dua, wata alama mai muhimmanci a al'adu da addinan gargajiya na Afirka.

3. Takardar cedi 5

Takardar cedi 5 na nuna tarihin ilimi a Ghana.

A kanta akwai hoton malami, mishan kuma mai rajin haɗin kan Afirka, James Kwagir Aggrey, wanda aka fi sani da "uban ilimi".

Takardar ta kuma ƙunshi hoton Makarantar Achimota, ɗaya daga cikin fitattun makarantun Ghana.

Makarantar ta haifar da shugabannin ƙasa da dama da kuma manyan 'yan siyasa.

4. Takardar cedi 10

Takardar cedi 10 na wakiltar adalci da daidaito.

A kanta akwai hoton Annie Ruth Jiagge, mace ta farko da ta zama alkaliya a Ghana, tare da hoton ginin Kotun Koli da wasu alamomin al'adu.

5. Takardar cedi 20

Takardar cedi 20 na wakiltar al'adu da masana'antar nishaɗi.

An sanya hoton mawaƙi, marubuci kuma masani kan kiɗa, Dr Ephraim Amu, wanda ya rubuta waƙoƙin kishin ƙasa da dama na Ghana.

Haka kuma akwai hoton National Theatre da wasu alamomin gargajiya na Adinkra.

6. Takardar cedi 50

Takardar cedi 50 na wakiltar kishin ƙasa.

A kanta akwai hoton Theodosia Okoh, matar da ta tsara tutar Ghana, tare da hoton hedikwatar gwamnati da wasu alamomin Adinkra.

7. Takardar cedi 100

Takardar cedi 100 na wakiltar zaman lafiya da haɗin kai.

An sanya hoton marigayi Kofi Annan, wanda ya taba zama Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya daga 1997 zuwa 2006.

Takardar ta kuma ƙunshi hoton Cibiyar Horar da Masu Kula da Zaman Lafiya ta Kofi Annan da wasu alamomin Adinkra.

8. Takardar cedi 200

Ita ce mafi girman darajar takardar kuɗi a Ghana.

Takardar na wakiltar 'yancin kai da ikon ƙasa, inda aka sanya hoton shugaban Ghana na farko, Dr Kwame Nkrumah, wanda ya jagoranci ƙasar zuwa samun 'yancin kai a 1957.

A bayan takardar akwai hoton Kwame Nkrumah Mausoleum da ke Accra, tare da wasu alamomin Adinkra.

  • Sabbin matakan tsaro

Gwamnan Babban Bankin Ghana, Dr Johnson Asiama, ya ce sabbin takardun kuɗin sun zo da ingantattun matakan tsaro, sun fi ɗorewa kuma fasalinsu ya dace da zamani tare da nuna al'adun Ghana.

Ya ƙara da cewa an tsara su ne domin kare kuɗaɗen daga masu jabun kuɗi tare da tabbatar da cewa za su dade suna amfani.

Shi ma daraktan kula da harkokin kuɗi na bankin, Dominic Owusu, ya ce sabbin takardun kuɗin sun dace da ƙa'idojin zamani.

Ya za a yi da tsoffin takardun kuɗin?

Babban Bankin Ghana ya ce sabbin takardun kuɗin cedi za su ci gaba da yawo tare da tsoffin takardun kuɗin da ake amfani da su a yanzu.

Bankin ya bayyana cewa duka tsofaffi da sababbin takardun kuɗin za su ci gaba da kasancewa halastattun kuɗaɗen mu'amala a ƙasar, kuma jama'a za su iya amfani da su a harkokinsu na yau da kullum.

Sai dai sabbin kuɗaɗen ba su haɗa da tsabar kuɗi, domin sauyin ya shafi takardun kuɗin ne kawai.

Gwamnan Babban Bankin Ghana, Dr Johnson Asiama, ya ce:

"Fitar da sabbin takardun kuɗin Heritage Series ba yana nufin cewa za a daina amfani da tsoffin takardun cedi ba. Tsoffin da sababbin takardun kuɗin za su ci gaba da yawo tare."

Daga baya bankin ya yi kira ga jama'a da kada su yi tururuwar canza tsoffin kuɗaɗensu ko cire kuɗi daga bankuna domin neman sabbin takardun kuɗin.

Haka kuma ya shawarci mutane da kada su murɗe ko su yi rubuce-rubuce a jikin sabbin takardun kuɗin domin su daɗe suna amfani.

Hukumomin sun kuma gargaɗi jama'a da su guji likin kuɗaɗen a bukukuwa, sannan kada a riƙa amfani da su wajen yin kwalliya.

Dr Asiama ya ce yin hakan zai taimaka wajen kare kuɗaɗen daga lalacewa tare da rage kuɗin da ake kashewa wajen maye gurbin takardun kuɗin da suka lalace.

Haɗa wannan da labarin bayaTaƙaita shi don sanarwar rediyoƘara kanun labari mai jan hankali.