Abin da muka sani kan harin da aka kai wa tawagar Pantami a Gombe

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Rundunar ƴansandan jihar Gombe ta tabbatar da hari kan tawagar motocin ɗantakarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Farfesa Ali Isa Pantami.

Lamarin na zuwa ne a lokacin da Pantami ke shirin halartar wani babban taro na yaƙin neman zaɓe da aka shirya masa a unguwar Jekada fari da ke tsakiyar birnin Gombe

Bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu matasa riƙe da makamai na fasa motocin da ke cikin tawagar, inda aka ga wasu mutanen da ke cikin motocin na fita da gudu domin tsira da rayuwarsu.

A baya-bayan nan ana samu ƙaruwar arangamar siyasa ko hari kan tawagar wata jam'iyya yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

A makon da ya gabata ma jam'iyyun ADC da NDC sun bayar da rahotannin farmakar tawagarsu yayin da suke ƙokarin halartar tarukan jam'iyyunsu a jihohin Sokoto da Cross River.

Wani abu da ke ƙara jefa fargaba a zukatan masu kaɗa ƙuri'a.

Yaya lamarin ya faru?

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Farfesa Pantami ya ce lamarin ya matuƙar tayar da hankali.

A hirarsa da BBC Abba Sani Pantami darakta hulda da kafafen yaɗa labarai na yaƙin neman zaɓen Pantami, ya ce wasu ne suka tura ƴan daba domin farmakar tawagar tasu a lokacin da suke yunƙurin halartar wani babban taron yaƙin neman zaɓe a birnin Gombe.

''Muna tsaka da tafiya, sai kawai mu ka ga ƴandaba ɗauke da makamai sun auka wa tawagarmu in da suka farfasa motoci da dukan mutane har ma da raunata wasu'', in ji shi.

Ya ce tun kafin fara taron kwamitinsu ya sanar wa da jami'an tsaro da batun gangamin nasu kuma jami'an tsaro sun je wurin.

''Amma saboda yawan ƴandabar da aka tanada, ƴansandan ba su iya kare aukuwar harin ba'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa yanzu haka sun miƙa lamarin ga jami'an tsaro waɗanda ya ce suna bincike domin kama waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Me ƴansanda suka ce?

DSP Buhari Abdullahi kakakin rundunar ƴansandan jihar Gombe ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Jeka da Fari da ke birnin Gombe, lokacin da tawagar Pantami ke kan hanyar zuwa gangami.

''A nan wurin ne wasu mahara suka riƙa kai wa tawagar hari, amma jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile harin'', in ji shi.

Ya ce yanzu haka jami'an tsaro na ci gaba da bincike domin tantance yawan waɗanda lamarin ya shafa, da kuma gano waɗanda suka kai harin'', in ji shi.

''Ba za ka iya tantance ɓangaren da ya kai harin ba, saboda wurin da lamarin ya faru, dama an saba kai hare-hare a wurin'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa kasancewa lamarin ya faru ne a tsakiyar kasuwa ya bai wa maharan damar kai hare-haren.

Ya ci gaba da cewa zuwa yanzu komai ya lafa, ana zaune lafiya, al'amura na ci gaba da wakana yadda aka saba.

Amnesty ta yi Allah wadai

Amnesty International ta yi kakkausar suka kan harin, inda ta yi zargin cewa an kai harin ne domin hana ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, shiga cikin garin Gombe.

Cikin wata sanarwa da ta fitar ta zargi jam'iyyar APC mai mulkin jihar da kitsa harin, inda kuma ta ce irin wannan hari ba abu ne da za a lamunta ba.

''Bidiyon da suka yaɗu sun nuna yadda wasu da ake zargin 'yan daban ne masu yawa kuma ɗauke da makamai suka tare hanya da tayoyi kafin daga bisani su banka musu wuta'', in Amnesty.

Ƙungiyar ta ce wannan na iya kasancewa ɗaya daga cikin munanan hare-haren siyasa mafiya muni da aka gani tun bayan fara yaƙin neman zaɓen shekarar 2027, tare da kiran ƴansandan su gudanar da bincike.

''Ya zama wajibi hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk waɗanda ake zargi da hannu a harin a gaban shari'a cikin adalci'', a cewarta.

Ta ƙara da cewa kai hare-haren tashin hankali kan jam'iyyun siyasa na iya kawo tarnaƙi wajen gudanar da ayyukansu na siyasa cikin lumana.

''Tashin hankali ba shi da gurbi a tsarin dimokuraɗiyya. Dole ne dukkan jam'iyyun siyasa su bai wa magoya bayansu umarni ƙarara da su guji shiga kowane irin tashin hankali tare da mutunta doka da ƙa'idojin dimokuraɗiyya'' in ji Amnesty.

Martanin APC

Jam'iyyar APC, wadda ɓangarori da dama ke nuna wa yatsa ta nesanta kanta daga lamarin.

Dahiru Hassan Kera mataimakin daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar APC a jihar ya ce babu ruwan jam'iyyar APC a lamarin da ya faru.

''Idan ka lura da bidiyon da aka nuna a shafukan sada zumunta za ka ga yadda ɗantakarar tasu ya shigo garin da ƴandaba ɗauke da makamai a cikin tawagar tasa, kuma babu yadda za ka tara irin wannan ƴandaban sannan ka iya sarrafa su'', in ji shi.

Ya yi zargin cewa faɗa ne ya ɓarke tsakanin mutanen da Pantami ya shiga da su garin Gombe.

''Ka san idan ka tara irin waɗannan mutane, to ko a kan raba kuɗi ma, faɗa zai iya ɓarkewa tsakaninsu kuma komai zai iya faruwa'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa jam'iyyar APC ba ta da masaniya kan abin da ya faru, hasalima ita aka yi wa laifi kasancewa ita ce ke mulki a jihar.