Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Faisal Maina da kotu ta yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai?
Faisal Maina ɗa ne ga tsohon shugaban hukumar fansho ta Najeriya, Abdulrasheed Maina, wanda aka taɓa yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari kan laifukan da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da kuma ƙarya wajen bayyana kadarorinsa.
A ranar 13 ga Nuwamban 2026, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a tura Faisal zuwa gidan gyaran hali domin ya fara zaman hukuncin ɗaurin shekaru bakwai da aka yanke masa.
Alƙalin kotun ya bayar da umarnin ne bayan amincewa da buƙatar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar.
EFCC ta nemi kotun ta bayar da izinin tura Faisal zuwa hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya domin aiwatar da hukuncin da aka yanke masa kan halatta kuɗaɗen haram da kuma rashin bayyana dukkan kadarorinsa a fom ɗin bayyana kadarori.
Jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kama Faisal a yankin Karsana da ke Abuja ranar 14 ga Oktoban 2026, bayan shafe shekaru da ya karya sharuɗɗan belinsa tare da daina halartar zaman shari'arsa.
A cikin buƙatar da ta shigar, EFCC ta kuma nemi kotun ta umarci cewa a fara ƙirga wa'adin hukuncin ɗaurin nasa daga ranar 14 ga Oktoba, lokacin da aka sake kama shi.
A watan Oktoban 2021, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa Faisal hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari.
Alƙali Okon Abang ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 7 ga Oktoban 2021, bayan samunsa da laifuka uku da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da kuma bayyana kadarori na ƙarya.
Wane ne Faisal Abdulrasheed Maina?
Faisal Maina ɗa ne ga Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban fansho a Najeriya.
Mahaifinsa, Abdulrasheed Maina, ya taɓa jan hankalin jama'a sakamakon alaƙarsa da wata shari'ar cin hanci da rashawa da ta shafi kuɗaɗen fansho.
An yanke wa mahaifinsa hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, bayan samunsa da laifin karkatar da kuɗaɗen da suka kai naira biliyan biyu, waɗanda aka danganta da kuɗaɗen ƴan fansho.
An sake shi daga gidan gyaran hali a farkon shekarar 2026, kuma tun daga lokacin ake nemansa bisa zargin karɓar kadarorin da aka sace.
Waɗanne laifuka ake tuhumar Faisal Maina da su?
A watan Oktoban 2019, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta gurfanar da Faisal a gaban Mai Shari'a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa tuhume-tuhume uku da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da kuma rashin bayyana dukkan kadarorinsa a fom ɗin bayyana kadarori.
A ranar 7 ga Oktoban 2021, Mai Shari'a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya same shi da laifin dukkan tuhume-tuhume ukun da suka shafi halatta kuɗaɗen haram.
Alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari kan tuhume-tuhume na ɗaya da na uku, sannan shekaru 14 kan tuhuma ta biyu.
Sai dai kotun ta umarci cewa a gudanar da dukkan hukuncin a lokaci guda, ma'ana mafi tsawon lokacin da zai yi a gidan yari shi ne shekaru 14.
Kotun ta same shi da taimaka wa mahaifinsa wajen halatta kuɗaɗe ta hanyar amfani da wani asusun banki na bogi mai suna "Alhaji Faisal Farm 2", wanda yake a bankin United Bank for Africa (UBA).
Kuɗin da ake magana a kai sun kai naira miliyan 58.1, waɗanda shi da mahaifinsa suka riƙa cirewa kashi-kashi tsakanin watan Oktoban 2013 da Yunin 2019.
Kotun ta ce ya kamata Faisal ya san cewa kuɗaɗen da yake hulɗa da su sun fito ne daga ayyukan cin hanci da rashawa da mahaifinsa ya aikata.
Kotun ta kuma bayar da umarnin rushe kamfanin da ake zargi da hannu a lamarin, mai suna Alhaji Faisal Farm 2, tare da ƙwace kuɗaɗen da ke cikin asusun bankin kamfanin.
Ta kuma umarci cewa idan aka samu Faisal a cikin Najeriya, a kama shi tare da tura shi gidan gyaran hali. Idan kuma aka same shi a wajen ƙasar, a fara matakan neman a dawo da shi Najeriya domin fuskantar hukunci.
A watan Nuwamban 2022, kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Faisal Maina, amma ta rage wa'adin ɗaurinsa daga shekaru 14 zuwa bakwai.
Kotun ta ce ta yi la'akari da cewa Faisal bai taɓa aikata laifi a baya ba, kuma kotun da ta saurari shari'ar tun farko bai kamata ta yanke masa hukuncin mafi tsawon lokacin da doka ta tanada ba.
A lokacin da kotun ɗaukaka ƙarar ta rage masa hukuncin zuwa shekaru bakwai, Faisal yana nan a ɓoye, don haka ba a iya aiwatar da hukuncin ɗaurin nasa nan take ba.
A watan Oktoban 2026, jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama Faisal Maina, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa ya dawo Najeriya a ɓoye.
Wane ne mahaifin Faisal Maina, kuma waɗanne laifuka aka same shi da su?
An haifi Abdulrasheed Maina a ƙauyensu da ke ƙaramar hukumar Biu a jihar Borno ta Najeriya, a kusan shekarar 1950.
Yana da mata mai suna Laila Maina, kuma suna da 'ya'ya, ciki har da Faisal Maina, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari bisa zargin halatta kuɗaɗen haram.
Kafin Abdulrasheed Maina ya zama shugaban tawagar sake fasalin tsarin fansho ta Najeriya (Pension Reform Task Team), ya shafe shekaru yana aiki a matsayin babban jami'i a ofishin kula da fansho na ma'aikatan Kwastam, Shige da Fice da Gidajen Yari (CIPPO).
A shekarar 2010, aka naɗa shi shugaban tawagar PRTT, inda ya jagoranci tawagar daga shekarar 2010 zuwa 2013.
A watan Nuwamban 2021, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari, bayan samunsa da laifukan halatta kuɗaɗen haram.
Alƙalin da ya jagoranci shari'ar, Okon Abang, ya bayyana a hukuncin da ya yanke ranar Litinin cewa Maina ya wawure sama da naira biliyan biyu daga kuɗaɗen fansho.
Kotun ta ce masu gabatar da ƙara, wato Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), sun gabatar da gamsassun shaidu da suka tabbatar ba tare da wata tantama ba cewa Maina ya aikata laifin halatta kuɗaɗen haram na naira miliyan 171 da dubu 99.
Kotun ta kuma same shi da laifin neman ma'aikatan bankin Fidelity su buɗe masa asusun banki ba tare da bin ƙa'idojin tantance wanda zai mallaki asusun ba.
Haka kuma, kotun ta ce ya ɓoye ainihin matsayinsa na mai sanya hannu kan asusun bankunan da ya buɗe a UBA da Fidelity, ta hanyar amfani da sunayen 'yan uwansa ba tare da saninsu ko amincewarsu ba.
A watan Oktoban 2019, wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin tsare tsohon shugaban hukumar kula da fansho, Abdulrasheed Maina, a gidan yari.
A lokacin, EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban tawagar sake fasalin tsarin fansho a gaban kotu, bisa tuhume-tuhume 12. Sai dai bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Maina ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su.
A ranar Talata, 22 ga Oktoban 2019, Mai Shari'a Folasade Giwa-Ogunbanjo ta umarci Maina da ya miƙa kadarori 23 da aka gano suna da alaƙa da shi.
Kadarorin sun haɗa da gidaje, filaye da kamfanoni da ke jihohin Abuja, Kaduna, Borno da Nasarawa.
A nasa ɓangaren, ɗansa Faisal Maina ya musanta tuhume-tuhume uku da suka shafi halatta kuɗaɗen haram.
Alƙalin da ke jagorantar shari'ar, Mai Shari'a Okon Abang, ya bayar da umarnin a tsare Faisal a sashen rundunar 'yan sanda ta musamman mai suna Police Tactical Squad, har zuwa lokacin da za a fara sauraron shari'arsa.
A shekarar 2020, Maina ya faɗi a cikin kotu.