Yadda wani mutum ya haɗiye buroshi yayin da yake wanke baki

    • Marubuci, Omkar Karmbelkar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Marathi
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Akwai mamaki a ji cewa buroshi ya sulale daga hannun mutum yayin da yake wanke baki, har ya shiga cikinsa. To amma tabbas irin wannan lamari ya faru da wani mutum a India.

Lamarin da ya faru da Rajendra Malusare, mazaunin ƙauyen Sherawali da ke gundumar Raigad a jihar Maharashtra ta India, ya sa aka kwantar da shi a asibiti.

Rajendra mai shekara 50 direban motar Bajaj ne.

Binciken farko da likitoci suka yi bai gano inda buroshin yake ba. Sai dai daga baya, wani bincike da ake kira endoscopy ya nuna cewa buroshin ya makale a cikinsa.

Likitocin sun yi nasarar cire buroshin mai tsawon santimita 19 ba tare da yi masa tiyata ba.

An sallami Rajendra zuwa gida bayan wasu 'yan sa'o'i da kammala aikin.

*Endoscopy* wata hanya ce ta binciken lafiya da ake amfani da wata siririyar bututu mai sassauƙa, wadda ke da kyamara a ƙarshenta. Ana shigar da ita ta bakin mutum domin duba cikin maƙogwaro, ciki da kuma sassan hanyar narkar da abinci. Haka kuma, ana iya amfani da ita wajen cire abubuwan da suka makale a cikin waɗannan sassan jiki.

Rajendra, wanda ke da nakasa kuma mazaunin Sherawali ne, yana wanke haƙoransa kamar yadda ya saba yi a safiyar ranar da abin ya faru, sai kwatsam buroshin ya makale a maƙogwaronsa.

Nan take ya garzaya wajen wani likita a yankin.

Ba a iya ganin buroshin a hoton X-ray ba, don haka aka tura shi wani asibiti da ke Navi Mumbai domin ƙarin bincike.

Binciken endoscopy ne ya tabbatar da cewa dukkan buroshin haƙoran ya shiga cikinsa. Tawagar likitoci ƙarƙashin jagorancin Dr Raosaheb Rathod, ƙwararren likitan cututtukan ciki kuma masani kan aikin endoscopy a asibitin Medicover, ce ta yi nasarar cire shi ta hanyar wani aikin likita mai sarƙaƙiya.

Buroshin ya kai tsawon santimita 19

Bayan kimanin sa'o'i uku zuwa huɗu da haɗiye buroshin, Malusare ya fara jin ɗan ciwo a cikinsa. A lokacin da likitoci suka yi masa binciken endoscopy, sun gano buroshin mai tsawon santimita 19 a cikin cikinsa.

A cewar likitoci, akwai ƙarancin yiwuwar dogayen abubuwa masu tauri kamar buroshin haƙora su bi hanyar narkar da abinci su fita daga jiki da kansu.

Irin waɗannan abubuwa na iya makalewa a maƙogwaro ko wasu ƙunƙuntar sassan hanyar narkar da abinci, abin da zai iya haifar da matsaloli masu tsanani kamar raunata sassan ciki, toshewar hanyar narkar da abinci ko huda wasu sassan jikinsa.

An ɗauki kusan minti 30 ana aikin *endoscopy* a kan Malusare. Tun da buroshin haƙoran ya kwanta a cikin cikinsa, hakan ya ƙara wahalar da aikin cafkowa da cire shi cikin aminci ta cikin ƙunƙuntar sassan maƙogwaro.

A yayin aikin, buroshin haƙoran ya makale a mahaɗar maƙogwaro da ciki. Likitocin sun yi taka-tsantsan wajen fitar da shi ta wannan ƙunƙuntar hanyar. Bayan yunƙuri da dama, a ƙarshe sun yi nasarar fitar da buroshin haƙoran gaba ɗaya ta bakinsa ba tare da yi masa tiyata ba.

Bayan cire buroshin haƙoran, likitoci sun sake yin wani bincike domin tabbatar da cewa bai samu rauni a maƙogwaronsa ko wani sashe na hanyar narkar da abinci ba.

Bayan sun sa ido kan yanayinsa na ɗan lokaci, sun tabbatar da cewa lafiyarsa ta daidaita, inda suka sallame shi zuwa gida a ranar.

A lokuta da dama, ana samun rahotannin mutane da suka haɗiye ƙashin kifi, ƙananan yara da suka haɗiye wasu abubuwa, ko kuma tsabar kuɗi da batir da suka shiga cikin ciki. Sai dai haɗiye buroshin haƙora kai tsaye abu ne da ba kasafai ake samun irinsa ba.

BBC ta tambayi Dr Raosaheb Rathod dalilin da ya sa hotunan X-ray da aka ɗauka wa Malusare tun farko ba su nuna cewa ya haɗiye buroshin haƙoran ba.

Ya ce: "Abubuwan da aka ƙera da roba ba sa fitowa sarai a hoton X-ray. Ƙasusuwa da abubuwan ƙarfe kan bayyana a hoton X-ray, amma abubuwa kamar roba sau da yawa ba sa fitowa. Saboda haka, ba za a iya cewa babu wani abu a cikin jikin mutum bisa hoton X-ray kaɗai ba."

Ya ƙara da cewa: "Idan mara lafiya yana da tabbacin cewa ya haɗiye wani abu, ko kuma yana jin rashin daɗi a jikinsa bayan faruwar hakan, akwai buƙatar yin ƙarin binciken lafiya. A wannan yanayin, bayan mun yi masa binciken *endoscopy*, wato amfani da bututu mai kyamara domin duba cikin jiki, mun gano cewa buroshin haƙoran gaba ɗaya yana cikin cikinsa. Wannan ne ya sa tarihin abin da ya faru da mara lafiya da kuma alamomin da yake nunawa suke da matuƙar muhimmanci a irin waɗannan lokuta."

Matsalolin da likitoci suka fuskanta wajen cire buroshin

Tawagar likitocin ta fuskanci ƙalubale da dama yayin ƙoƙarin cire buroshin haƙoran ta bakin Malusare.

Likitocin sun haɗa wani na'ura ta musamman a ƙarshen bututun binciken endoscopy, wadda suka yi amfani da ita wajen cafko ƙarshen buroshin haƙoran. Sai dai buroshin ya makale a mahaɗar maƙogwaro da ciki.

Bayan sauya yadda mara lafiyar yake kwance da kuma yin yunƙuri sau da dama, a ƙarshe likitocin sun yi nasarar matsar da buroshin zuwa gaba.

Daga nan kuma, buroshin ya sake makalewa a wani ƙunƙuntaccen sashe na maƙogwaro. Saboda buroshin ba ya lankwasawa ko sassautawa, aikin ya buƙaci kulawa ta musamman da ƙwarewa.

Dr Rathod ya ce: "Bayan cire buroshin, mun sake yin binciken *endoscopy*. A wannan karon mun duba ɓangarorin sama da ƙasa na maƙogwaro. Mun tabbatar da cewa babu tsagewa, zubar jini ko wata illa a cikin bangon maƙogwaron, duk da ƙalubalen da muka fuskanta yayin cire buroshin. Binciken bai nuna wata babbar illa ko mummunan rauni ba."

Ya ƙara da cewa: "Bayan haka, mun ci gaba da sanya ido kan mara lafiyar na wani ɗan lokaci. Da zarar mun tabbatar da cewa yanayinsa ya daidaita, muka sallame shi zuwa gida cikin sa'o'i uku zuwa huɗu."

Sashen BBC Marathi ya kuma tattauna da Rajendra Malusare domin jin yadda abin ya faru a ranar.

Ya ce: "Bayan na gama wanke haƙorana, na saba amfani da buroshin haƙoran wajen goge harshena. A lokacin ne kwatsam buroshin ya makale, sannan ya sulale ya shiga cikina. Tun da maƙogwarona ya samu rauni, na yi zaton buroshin ya makale a cikinsa. Amma daga baya na fahimci cewa ya riga ya isa cikina."

Ya ce: "Da farko na tsorata, domin na yi tunanin idan buroshin ya makale a ciki, zan iya samun matsalar numfashi. Amma nan take na garzaya wajen likita. Tun da ba a iya yi min magani a Sherawali, sai na tafi Kharghar da ke Navi Mumbai. Na yi tunanin cewa za a yi min tiyata, amma an yi min magani ta hanyar *endoscopy*, kuma aka sallame ni zuwa gida a ranar."

Baya ga yadda lamarin ya kasance abin mamaki, BBC ta tambayi Dr Rathod wane darasi ya kamata jama'a su koya daga abin da ya faru.

Ya ce: "Abu mafi muhimmanci shi ne kada mutum ya yi gaggawa yayin wanke haƙoransa. A guji magana, dariya ko yin wani abu daban yayin da buroshin haƙora yake cikin baki. A kuma yi taka-tsantsan kada a tura buroshin haƙoran zuwa cikin baki fiye da kima. Idan mutum ya haɗiye buroshin haƙora ko wani babban abu bisa kuskure, ya kamata ya garzaya asibiti nan take."

Dr Rathod ya kuma ba da wata muhimmiyar shawara cewa: "A irin wannan yanayi, bai kamata mutum ya yi ƙoƙarin yin amai ko kuma ya ci abinci domin tura abin da ya makale zuwa ciki ba. Yin waɗannan abubuwa na iya raunata hanyar da abinci ke bi zuwa ciki (maƙogwaro), ko kuma su sa abin ya ƙara zurfafa makalewa."

Ya ƙara da cewa: "Ko da yake ciwon na iya raguwa da farko, ba za a yi watsi da yiwuwar samun rauni a cikin jiki ko wasu matsaloli ba. Saboda haka, yana da matuƙar muhimmanci a gano matsalar cikin lokaci tare da samun maganin da ya dace."