Mutumin da ya tattara bidiyoyin tsiraicin mutane guda 1000 a matsayin mace

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Amarendra Yarlagadda
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Da farko, buƙatun sada zumunta daga asusun sada zumunta masu ɗauke da hotunan 'yan mata ne za su fara zuwa. Daga nan sai a fara tattaunawa, wadda daga bisani za ta rikide zuwa hirar lalata.
A cewar 'yan sanda, ana buƙatar waɗanda suke tattaunawar da su aika da hotunansu da bidiyoyinsu na tsiraici. Sai dai daga baya wani sabon mutum ya shiga cikin lamarin.
Mutumin da a baya yake tattaunawa da su kan fake da cewa shi budurwa ce da ke bayyana kansa a matsayin ɗan'uwan yarinyar, sannan ya fara neman kuɗi a wurinsu.
Rundunar 'yan sandan Hyderabad ta ce mutumin da yake yin amfani da sunan yarinyar da kuma wanda yake gabatar da kansa a matsayin ɗan'uwanta mutum ɗaya ne: Pawan Kumar mai shekaru 23.
Mutane nawa ka nema su aiko maka da hotunan tsiraicinsu?
A cewar 'yan sanda, Pawan ya yi amfani da dabarar yaudarar mutane ta hanyar soyayya wajen damfarar kusan mutum 1,000 daga sana'o'i daban-daban, ciki har da likitoci da 'yan sanda da 'yan kasuwa da jami'an gwamnati da injiniyoyin manhajojin kwamfuta da kuma malamai.
Mataimakin kwamishinan 'yan sandan Charminar, Kiran Khare, ya ce: "A cikin shekaru huɗu da suka gabata, yana yaudarar mutane ta hanyar soyayya tare da karɓar kuɗaɗe daga gare su, ta hanyar amfani da hotunan 'yan mata daban-daban, ciki har da wata mai tallan kaya daga Kolkata."
"Mutanen da ya damfara sun haɗa da mazauna jihohi daban-daban na Indiya da kuma wasu ƙasashe."
'Yan sanda sun ƙwato wayoyin hannu guda uku da kwamfutar tafi-da-gidanka guda ɗaya da kuma na'urar adana bayanai ta flash mai ƙarfin GB 16 daga hannun Pawan.
Dubarar ɗana tarko

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kondabattula Pawan Kumar mazaunin yankin Tekulpalli Mandal ne da ke gundumar Bhadradri Kothagudem a jihar Telangana.
Binciken 'yan sanda ya gano cewa Pawan ya bar karatunsa na difloma a shekara ta biyu a Cibiyar Koyar da Sana'o'in Ƙera Kayan Aiki ta Tsakiya (CITD) da ke Balanagar, Hyderabad.
A cewar mataimakin kwamishinan 'yan sanda (DCP), bayan barin karatun ne ya shaida wa iyalansa cewa yana karatun digiri na B.Tech a Kwalejin Malla Reddy.
Yana zaune a Hyderabad inda yake gudanar da ƙananan ayyuka daban-daban, sai dai a halin yanzu ba shi da aikin yi.
A cewar 'yan sanda, Pawan ya kasance yana ƙirƙirar asusun bogi a shafukan Instagram da Facebook ta hanyar amfani da hotunan 'yan mata.
Waɗannan asusun ne suke aika buƙatun sada zumunta ko bin mutane. Da zarar mutum ya amince da buƙatar, sai mutumin ya fara tattaunawa da shi, yana mai yin kamar shi yarinya ce.
DCP Kiran Khare ya ce: "A hankali yake karkatar da tattaunawar zuwa hirar lalata, sannan ya karɓi hotuna da bidiyoyin tsiraici daga hannun masu amfani da shafukan, ya kuma adana su."
'Yan sanda sun ce domin kauce wa zargin aikata laifi, Pawan ya kan aika wa waɗanda yake tattaunawa da su hotunan wasu mata masu bayyana sassan jikinsu, amma ba tsirara ba.
Baya ga yarinyar, sai 'ɗan'uwanta' ya bayyana.

Asalin hoton, HyderabadPolice
A cewar 'yan sanda, bayan samun bidiyoyi da hotunan tsiraici, Pawan ya fara karɓar kuɗi daga mutane ta hanyar yi musu barazana.
Daga baya, Pawan kan bayyana kansa a matsayin ɗan'uwan yarinyar da yake tattaunawa da mutanen a matsayinta.
Bayan haka, sai ya tuntubi mutanen da suka aika masa da hotuna da bidiyoyin tsiraici ta hanyar kiran waya da WhatsApp da kuma asusun sada zumunta.
DCP ɗin ya ce: "Yana yi musu barazanar cewa 'yar'uwarsa ta kashe kanta ko kuma zai kai ƙara ofishin 'yan sanda. Ta haka ne yake karɓar kuɗi daga gare su ta hanyar barazana."
A cewar Kiran Khare, Pawan ya fi amfani da hotunan wata mai tallan kaya daga Kolkata wajen gudanar da wannan aika-aika.
'Yan sanda sun tuntubi matar tare da sanar da ita abin da ke faruwa.
Ya fi dana tarko ga mutane 'yan tsakanin shekaru 22 da 70.
'Yan sanda sun ce Pawan ya yaudari kusan mutum 1,000 daga sana'o'i daban-daban, ciki har da 'yan sanda da malamai da ma'aikatan gwamnati da jami'ai da injiniyoyin manhajojin kwamfuta da likitoci, ta hanyar yin hirar lalata da su.
Kiran Khare ya ce: "Shekarun waɗannan mutane sun kasance tsakanin 22 zuwa 70. Mun gano hotuna da bidiyoyin tsiraicin mutane 82."
A cewar 'yan sanda, waɗanda suka faɗa tarkon sun haɗa da mazauna Telangana da Andhra Pradesh da Kerala da Tamil Nadu da Punjab, da kuma ƙasashen Saudiyya da Turkiyya da Pakistan da Kanada.
'Yan sanda sun ce ya zuwa yanzu Pawan ya damfari waɗannan mutane kuɗi har naira? Rs 25 lakh da dubu 16.
Yana da asusun bogi 27 a Instagram da Facebook.

Asalin hoton, Getty Images
Binciken 'yan sanda ya gano cewa Pawan ya ƙirƙiri asusun bogi guda 13 a Instagram da kuma shafuka 14 na bogi a Facebook.
Ga asusun bogi 13 ɗin da ya ƙirƙira a Instagram:
1. Priyanka 11243
2. Amer 531
3. K. Chandanasri
4. K_Chandana_sri_21
5. Chandana_Princess_2021
6. Chandana_sri_445
7. Chinnu223558
8. deekshitha_princess_2021
9. moon_baby_5973
10. Kanna_ya1024
11. Misalgunjan
12. Kondabathula_Pavan_2324
13. Kondabathulasadanandam
A cewar mataimakin kwamishinan 'yan sandan, ga shafukan bogi da aka ƙirƙira a Facebook:
1. Chandana Angel
2. K. Chandana Sri
3. Chandana Sri
4. Honey Kana Potti
5. Ayesha Potti
6. Chandana Prince. S
7. Sri K Chandana
8. A. Keerthi
9. Chandana K
10. Dharawath Swati
11. Vijay Kumar
12. K. Pawan Shiva
13. Bhukya Anil
14. Divya Sri
Kiran Khare ya ce duk wanda ya samu saƙo daga waɗannan asusun ya yi taka-tsantsan tare da sanar da 'yan sanda.
Abokin nasa ya samu buƙatar sada zumunta, daga nan ne sirrin lamarin ya fara fitowa fili.
A cewar 'yan sanda, Pawan Kumar ya kuma damfari wani abokinsa tare da karɓar kuɗi har rupe 400,000 daga gare shi ta hanyar barazana. Wannan ne ya sa aka gano dukkan lamarin.
Abokinsa Ramesh (ba sunansa na gaskiya ba), wanda ya faɗa tarkon damfarar, ya shigar da ƙara a ofishin 'yan sanda.
Ramesh ya bayyana cewa ya haɗu da Pawan Kumar a lokacin da suke karatun difloma a Cibiyar Koyar da Sana'o'in Ƙera Kayan Aiki ta Tsakiya (CITD).
A watan Satumban 2021, Ramesh ya samu buƙatar sada zumunta a shafinsa na Instagram daga wani asusu mai suna 'Moon Baby 5973'.
A cikin ƙorafinsa ga 'yan sanda, Ramesh ya ce: "Na fara zargin wannan asusun. Bayan na duba shi, na fahimci cewa Pawan Kumar ne ya ƙirƙire shi."
"Nan take na tambaye shi game da lamarin, sai ya amsa cewa shi ne ya ƙirƙiri asusun bogin. Bayan haka, na yanke shawarar kawo ƙarshen abotarmu."
A cewar Ramesh, daga baya ya ƙaura zuwa wani gidan kwanan ɗalibai. Duk da haka, Pawan ya je wurin tare da neman ya zauna da shi.
A cewar ƙorafin, a wannan lokacin ne su biyun suka fara yin lalata da juna. Ramesh ya yi zargin cewa Pawan ya matsa masa lamba domin ya tilasta masa yin jima'i, sannan ya yi masa barazana.
A cikin ƙorafinsa, Ramesh ya zargi Pawan da yi masa barazanar cewa ya ɗauki bidiyonsa. Ya ce Pawan ya matsa masa lamba domin ya tilasta masa yin jima'i, sannan ya karɓi rupe 150,000 daga gare shi ta intanet da kuma rupe 250,000 kai tsaye.
Rundunar 'yan sandan Saidabad ta buɗe shari'a tare da fara binciken lamarin a ranar 17 ga Oktoba. A yayin wannan bincike ne aka gano batun yaudarar mutane ta hanyar tarkon soyayya.
'Yan sanda sun shawarci jama'a da kada su aika wa kowa da hotunansu na tsiraici.
DCP Kiran Khare ya ce: "Idan ka samu buƙatar sada zumunta daga wani asusu a shafukan sada zumunta, ya kamata ka bincika asusun. Musamman ma, ya kamata ka yi taka-tsantsan idan ka samu saƙo daga asusun da ba ka sani ba."
"Irin waɗannan mutane kan fara magana da mutum cikin sakin fuska da nuna abokantaka. Daga nan sai su fara damfarar mutane ta hanyar karɓar hotuna da bidiyoyinsu na tsiraici. Ya kamata waɗanda suka faɗa tarkonsu su gaggauta kai ƙara ofishin 'yan sanda."
BBC ta yi ƙoƙarin tattaunawa da Pawan Kumar game da lamarin, amma ba a samu damar tuntuɓarsa ba saboda yana tsare a hannun hukumomin shari'a.
Ko da lokacin da 'yan sanda suka gabatar da shi ga manema labarai, ya ƙi magana.
BBC ta kuma tuntubi 'yan gidan Pawan, amma su ma sun ƙi magana.


























