'An binne wani a cikin kabarina'

- Marubuci, Sarah-May Buccieri
- Aiko rahoto daga, Deeping St James
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Wata mata ta ce ba za ta iya kallon kabarin da ta tanada kuma ta biya kuɗinsa da irin yadda take kallonsa a da ba, bayan da aka yi kuskuren binne wani mutum a cikinsa, sannan daga baya aka tono gawar aka cire.
Marie Lane, mai shekara 69, ta ce tun da farko ta tanadi kuma ta biya kuɗin wani fili domin a binne ta a makabartar Deeping St James Cemetery da ke yankin Lincolnshire, a bayan kaburburan iyayenta da suka rasu.
Ta ce lamarin ya sa ta ji " rashin daɗi" da kuma takaici, sakamakon yadda majalisar cocin yankin ta gudanar da batun bayan da aka gano an yi kuskure binne wani daban a filin da ta tanada domin a binneta.
A farkon wannan shekarar, Ma'aikatar Shari'a ta Birtaniya ( MoJ) ta ba da izinin tono gawar mutumin da aka binne a kabarin da Marie Lane ta tanada, domin gyara kuskuren da aka tafka na binne shi a wurin da bai dace ba.
Majalisar koli ta cocin Deeping St James Parish ta ce ta amince cewa an yi kuskure a lamarin, tare da neman afuwa kan damuwar da hakan ya jawo wa iyalan biyu da abin ya shafa.
Majalisar ta kuma ce an mayar wa Marie Lane filin kabarin da ta tanada tun farko.

A shekarar 2013, Marie Lane ta ce ta sayi haƙƙin zama ita kaɗai a wurin da ta tanada a binne ta a wani fili da ke bayan kabarin mahaifiyarta. Ta ce wata takarda daga Majalisar koli ta Deeping St James Parish, wadda BBC ta gani, ta tabbatar da wannan haƙƙi nata.
"Na sayi filin kabari ne domin in kasance kusa da iyayena,"
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Babu amfanin a binne ni a nan idan ba zan kasance tare da waɗanda nake ƙauna ba." in ji ta
A farkon shekarar 2023, Marie Lane ta ce ta kai ziyara makabartar, inda ta gano cewa an binne wani mutum a filin kabarin da ta tanada tun da farko.
"Na tsaya a wurin kawai ban san abin da zan yi ba, a gaskiya," kamar yadda ta tuna.
"An binne wani mutum da ban taɓa sani ba a kabarina." in ji Marie Lane.
Marie Lane ta ce ya ɗauki sama da shekara uku tana neman a ɗauke gawar mutumin da aka binne a filin kabarinta, tana mai cewa ba ta da wani zaɓi saboda babu wani wuri a kusa da kaburburan iyayenta da za ta iya samu.
A Ingila, idan ana son tono gawa daga ƙasar da ba a keɓe domin harkokin addini ba, dole ne a nemi izini daga Ma'aikatar Shari'a ta Birtaniya ( MoJ). A mafi yawan lokuta kuma, ana buƙatar amincewar dangin mamacin na kusa kafin a bayar da izinin.
A wata wasiƙa da Ma'aikatar Shari'a ta Birtaniyata aike wa Majalisar koli ta cocin Deeping St James Parish , ma'aikatar ta ba da izinin tono gawar duk da cewa ba a samu amincewar dangin mamacin na kusa ba.
Haka kuma an bayar da izinin ne duk da kasancewar iyalan mamacin sun nuna adawa bisa dalilai na ɗabi'a da kuma na addini.
Wasiƙar da Ma'aikatar Shari'a ta Birtaniya ta aika wa majalisar koli ta cocin ta bayyana cewa babu wasu hanyoyi na daban da za su iya magance matsalar, saboda haka ta bayar da izinin tono gawar domin a gyara kuskuren da aka yi na binne mamacin a filin kabarin da bai dace ba.
BBC ta ce ta yi ƙoƙarin tuntubar iyalan mutumin da aka tono gawarsa domin jin ta bakinsu, amma ba ta samu damar hakan ba.

Mijin Marie Lane, mai shekara 77, Eric Lane, ya ce dukkanin matakan da aka bi wajen warware lamarin sun yi matuƙar tasiri ga matarsa.
Ya ce yana ganin Majalisar koli ta cocin Deeping St James Parish ba ta da ingantaccen tsarin adana bayanai da zai hana faruwar irin wannan kuskure.
Ya kuma bayyana damuwarsa cewa makamancin wannan kuskure na iya sake faruwa a nan gaba.
BBC ta tuntuɓi majalisar cocin ta Deeping St James Parish kan wannan zargi kai tsaye, tare da tambayar matakan da ta ɗauka domin hana sake faruwar irin wannan kuskure a nan gaba.
Sai dai majalisar ba ta mayar da martani ba.
Mijin Marie Lane, Eric Lane, ya ce matarsa ba ta son zuwa makabartar a yanzu.
"Akwai abubuwa masu tayar da hankali da kuma bacin rai da suka haɗu da wannan wuri har yanzu, ta yadda ban san ko za su taɓa gushewa ba," in ji shi.
Marie Lane ta ce tana tausaya wa iyalan mutumin da aka yi kuskuren binne shi a filin kabarinta, kuma ta fahimci irin damuwa da wahalar da lamarin ya jefa su.
"Ina son na haɗu da su," in ji ta.
"Na roƙi majalisar Deeping St James Parish sau da yawa a shirya mana ganawa da su, amma a kowane lokaci ana gaya min ba za a yi hakan ba."

Marie Lane ta ƙara da cewa:
"Har yanzu ina jin rashin daɗi sosai idan zan je makabartar. Yanzu ba ma zuwa can sau da yawa kamar yadda muka saba a da," in ji ta.
Ta ce har yanzu akwai tambayoyi da dama da ba ta samu amsarsu ba.
"Bai kamata a ce an ɗauki shekara uku ana warware wannan matsala ba. Ko da watanni uku ma sun yi yawa, kuma bai kamata mu shiga wannan doguwar fafutuka ba domin a gyara kuskuren da aka yi," in ji ta.


























