Abubuwa uku da zan mayar a hankali a kai – Magajin Masussuka

.
Bayanan hoto, Imam Rasheed
    • Marubuci, Bashir Zubairu Ahmad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Tun bayan rasuwar Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, wanda ya yi fice wajen wa'azi da fafutukar yada fahimtarsa ta addini, an fara ɗaukar matakai domin tabbatar da ci gaba da ayyukan da ya bari.

Ɗaya daga cikin waɗannan matakan shi ne naɗin Imam Rasheed a matsayin magajinsa, a wani yunƙuri na tabbatar da cewa manufofin da marigayin ya assasa ba su tsaya sakamakon rasuwarsa ba.

Sheikh Masussuka ya shafe sama da shekaru 30 yana wa'azi, inda ya yi amfani da kafafen sadarwa da sauran hanyoyin sadarwa wajen isar da saƙonninsa ga jama'a.

Bayan an sanar da naɗin Imam Rasheed a matsayin wanda zai gaji marigayin, musamman wajen ci gaba da ayyukan da suka shafi haɗin kai da zaman lafiya, ya shaidawa BBC cewa akwai manyan abubuwa uku da zai mayar da hankali a kai domin tabbatar da cewa manufofin da marigayin ya ɗora tafiyarsu kai, ba su tsaya a nan ba. Ga abubuwa uku da ya bayyana zai mayar da hankalinsa akansu:

1. Ɗabbaƙa dawa'ar Alƙur'ani

Imam Rasheed ya ce Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka ya bar babban ƙalubalen da ke gaban sabon magajin shi ne tabbatar da cewa ayyukan da Sheikh Masussuka ya fara ba su tsaya ba.

Inda ya ce zai ci gaba da ayyukan ilimantarwa da yada saƙonnin da suka shafi fahimtar addini ta hanyar da'awa, "abinda zan fi mayar da hanakli akai shi ne ɗabbaka da'awar Alƙur'ani, ya amsa amo ya kai koi'ina a duniya a matsayin isasshe, wanda kuma ya ke gado da Annabi Muhammadu sallalahu alaihi wasallama ya bari kuma shi ne littafin Allah."

Imam Rasheed ya nunar da cewa cewa yana da burun bin tafarkin yin da'awa irin ta marigayi Sheikh Masussuka, wanda ya shahara da ita zuwa matakin ƙasa da ƙasa, ta yadda saƙon da yake yaɗawa zai kai ga mutane fiye da waɗanda suke zaune a Najeriya, a cewarsa " wannan shi ne aikin da Malam ya sa a gaba, kuma shi ya yi fatar ya bar duniya akai, mu ma shi ne muke fatar mu bar duniya akai, kuma shi babban aikin da zan mayarwa hankali a gaɓa ta farko kenan", in ji shi.

A cewar manufar wannan da'awa, Alƙur'ani ne babban tushen koyarwa da fahimtar addini, saboda haka yana son ƙara samar da hanyoyin da mutane za su samu damar karanta shi da fahimtar ma'anoninsa da kuma koyon saƙonnin da ke cikinsa.

2. Samar da haɗin kai

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Magajin na Sheikh Ibrahim Yahaya Masussuka, ya bayyana cewa zai mayar da hankali wajen samar da haɗin kai tsakanin al'umma ciki har da mabiya addinai daban-daban.

Ɗaya daga cikin manufofin da suka fito fili a ayyukan marigayi Sheikh Yahaya Masussuka shi ne ƙoƙarin ƙarfafa fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

A lokacin rayuwarsa, ya gudanar da ziyarce-ziyarce da ganawa da malamai da suke da saɓasnin fahimta da ƙungiyoyin addinai daban-daban.

Sabon magajin ya ce daga yanzu zai ci gaba da wannan manufa, domin zaman lafiya da haɗin kai su ci gaba da zama ginshiƙan ayyukan ƙungiyarsu.

Ya ƙara da cewa, "a matsayina na jakadan zaman lafiya, dama shi kansa Malam jakadan zaman lafiya ne tsakanin al'umma da Kiristoci da jama'ar Shi'a da 'Yan Tijjaniyya da ɓangaren Kadiriyya da 'yan-baruwana ma da Ahlussuna wannan shi ne abin da malam ya mayar da hankali akai, ni ma kuma wannan shi ne abin da zan mayar da hankali akai, kuma muna ma wata ziyara da muke cewa wa 'Operation Zaman Lafiya Dole', mun kai ziyara wurin Sheikh Al-Zazzaky, mun kai ziyara wurin Shekhi Nuru Khalid, mun kai ziyara wurin manyan malamanmu su Sheikh Muhammad Usman Ɗangungu Kaduna".

Imam Rasheed ya yi cikakken bayanin cewa duk inda ka ga duniya ta ci gaba to akwai zaman lafiya, kuma akwai waɗanda ke ɗaukar musulmi a matsayin masu neman faɗa da mutane alhali ba haka lamarin yake ba.

3. Yin wa'azi ba tare da fargaba ba

Wani muhimmin batu da Imam Rasheed ya bayyana cewa zai mayar da hankali a kai shi ne ci gaba da yin wa'azi ba tare da tsoro ko fargaba ba, tare da bin tafarkin Annabawa wajen isar da saƙon Allah ga al'umma.

Wannan na nufin yin kira zuwa ga addinin Allah da bayyana koyarwar Alƙur'ani da Sunnar Annabi Muhammad (SAW), ba tare da barin tsoron suka da barazana ko rashin jin daɗin wasu mutane ya hana isar da saƙon gaskiya ba.

"Ai ba fargaba akan sunnar Annabawa, kuma duk wanda ya ke addini da gaske baya fargaba a cikinta. Na farko ma mu dauki isalin yadda ake mutuwa wannan fita zai yi yayi hatsari ya mutu wani ɗan bindiga ne zai ɗauke shi ya je ya kashe sghi a daji, wannan kuma yana kwance a gida a ji an ce ya mutu, wani zai ƙone a wuta, wani yana tafiya haka kawai ya kwanta bacci a tashi babu shi", in ji shi.

Ya ce abin da wannan manufa ke nufi shi ne tabbatar da cewa wa'azi ya kasance bisa gaskiya da hujja, ba tare da tsoron matsin lamba ko ƙalubalen da ka iya tasowa ba.

Wannan ya nuna cewa sabon magajin na son ci gaba da da'awar da ba ta yin shiru ba ce wajen isar da koyarwar addini tamkar dai yadda mahaifinsa ya yi, tare da tabbatar da cewa saƙon ya isa ga al'umma ba tare da fargabar ƙalubale ba.