Kareena Kapoor na shan suka kan saka sarƙa mai rubutun Qur'ani

Asalin hoton, SOCIAL
A yayin da ake shirye-shiryen bikin Diwali na Indiya, fitacciyar jarumar fina-finan Bollywood, Kareena Kapoor Khan, ba ta yi tsammanin cewa sarkar wuyar da ta sanya zai jefa ta cikin takaddamar shari'a ba.
Kareena ta sanya sarkar wuya mai darajar zinare 30 domin kece ado a bikin. Sarkar na kuma ɗauke da rubutun Ayatul Kursiyyu.
Bayan hotunan bikin sun bazu a shafukan sada zumunta, jagoran jam'iyyar Congress, Abbas Hafeez, ya aika wa jarumar takardar gargaɗi.
Ya nuna rashin jin daɗi kan yadda aka nuna rubutun al-Qur'ani a cikin hotunan da Kareena ta wallafa a shafukanta na sada zumunta.
Ba Kareena kaɗai aka aika wa sammaci ba, har ma da Rhea Kapoor, wadda ta samar da kayan da jarumar ta saka.
Takardar ta shari'a ta buƙaci a goge hotuna da bidiyoyi da kuma duk wasu rubuce-rubuce da aka wallafa kan lamarin a shafukan sada zumunta. Haka kuma ta nemi a bayar da hakuri a bainar jama'a, tare da tabbatar da cewa za a lura sosai yayin amfani da rubutun na al-Qur'ani a nan gaba.
A baya-bayan nan, Kareena Kapoor Khan ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Instagram sanye da kayan alfarma domin bikin Diwali.
An gayyaci manyan jarumai daga masana'antar fim ta Indiya zuwa taron.
Rhea Kapoor, wadda ta samar da kayan, ita ma ta wallafa hotunan a shafinta na Instagram tare da wani rubutu mai cewa:
"Haƙiƙa tauraruwar fina-finai ce, an samar da kayan adonta da azurfa mai kyau, sannan tana da irin nata salo na musamman na sanya tufafi."
Rhea Kapoor ta ƙara yin bayani kan kayan da Kareena ta sanya a wani rubutu da ta wallafa, inda ta ce:
"Kareena ta sanya sarka da aka ƙera da azurfa tsantsa, wanda Puneet Balan ya samar.
Haka kuma, ta sanya wani abin ado na kai mai shekaru 200, wanda ya kasance mallakin sarakunan Bhopal na baya, da kuma zinare mai gram 30, wanda shi ma ya kasance mallakin sarakunan Bhopal.
Sarkar na ɗauke da rubutun Ayatul Kursiyyu daga cikin Alƙur'ani mai girma a jikin."

Asalin hoton, Kareena Kapoor Khan/Instagaram
Ta kuma ce wannan kayan ado na tarihi, wani gadon sarauta ce da iyalan masarautar Bhopal suka kiyaye cikin kulawa tsawon zuri'o'i da dama.
Ta ƙara da cewa Kareena ta samu wannan kayan ado tarihi iyalan mijinta, Saif Ali Khan. Kakar Saif, Sajida Sultan, 'yar sarkin Bhopal na ƙarshe ce.
Me takardar shari'ar ta kunsa?

Asalin hoton, Rhea Kapoor/instagram
Lauyan Abbas Hafeez, Mohammed Zafar wanda kuma ke magana da yawun jam'iyyar Congress, ya shaida wa manema labarai cewa suna buƙatar a goge hotunan da ke ɗauke da rubutun al-Qur'ani da jaruma Kareena ta wallafa a shafukan sada zumunta.
Ya ce: "Ba mu adawa da jaruma Kareena Kapoor kawai don ta sanya sarkar wuya. Sai dai, muna ƙorafi ne kan rubutun da ke ɗauke a jikin sarkar."
Ya ƙara da cewa: "Sarkar na ɗauke da rubutun wata aya cikin al-Qur'ani, wanda ake ɗaukarsa a matsayin abu mai matuƙar tsarki."
"Mun sani wannan abu ya ɓata wa al'ummar Musulmai rai."
Lauya Zafar ya kuma ce: "A cewar koyarwar addinin Islama, mutum na buƙatar yin alwala kafin karanta wata aya cikin al-Qur'ani ko kuma taɓa al-Qur'ani. Babban ƙorafin mu shi ne yanda aka gabatar da ayar a kafafen sada zumunta."
Ya ce hakan ne ya janyo suka aika mata takardar shari'a, inda suke buƙatar a goge hotunan.


























