Matsaloli biyar da ya hana Man United komawa kan ganiya

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na daga cikin kungiyoyin da suka fi shahara a tarihin kwallon kafa a duniya. A karkashin Sir Alex Ferguson United ta kwashe sama da shekaru 26 tana cin kofuna 38 tare da kafa tarihi da ya sa ta zama daya daga cikin manyan a fannin taka leda a duniya.
Ga jerin kofunan da Ferguson ya dauka a Manchester United:
- Gasar Firimiya Ingila (Premier League): Kofuna 13
- Kofin FA (FA Cup): Kofuna 5
- Kofin EFL (League Cup): Kofuna 4
- Kofin FA Community Shield: Kofuna 10
- Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League): Kofuna 2 (1999 da 2008)
- Kofin Kofunan Turai (UEFA Cup Winners' Cup): Kofi 1 (1991)
- Kofin Super Cup na Turai (UEFA Super Cup): Kofi 1 (1991)
- Kofin Intercontinental Cup: Kofi 1 (1999)
- Kofin Duniya na Kulob (FIFA Club World Cup): Kofi 1 (2008)
Amma tun bayan da Ferguson ya yi ritaya a shekarar 2013, kungiyar ta shiga wani yanayi na rashin tabbas wanda har yanzu take kokarin ganin ta koma kan ganiya.
Duk da kashe makudan kudi da daukar fitattun 'yan wasa da kuma sauya masu horarwa da dama, har yanzu United ba ta iya komawa matsayin da take a kai lokacin Ferguson ba. Wasu lokuta kungiyar tana nuna alamun murmurewa, amma daga baya abubuwa sai su sake lalacewa.
Masana da dama suna ganin cewa matsalar Manchester United ba ta ta'allaka ga koci kadai ba. A maimakon haka, matsalar tana cikin tsarin gudanarwa, dabarun daukar 'yan wasa da rashin hangen nesa na dogon lokaci.
Matsala ta 1: Rashin hakuri da koci

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da Sir Alex Ferguson ya ajiye aiki, Manchester United ta mika ragamar kungiyar ga David Moyes, wanda ake kallon zai ci gaba da aiki bisa tsarin da Ferguson ya gina.
Sai dai Moyes bai kai shekara guda ba aka sallame shi bayan sakamakon da ba su gamsar ba. Daga nan kungiyar ta dauki Louis van Gaal wanda ya lashe FA Cup amma shi ma aka sallame shi.
Daga baya Jose Mourinho ya zo ya lashe Europa League da League Cup, amma ya samu sabani da shugabanni da wasu 'yan wasa kafin a sallame shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ole Gunnar Solskjaer ya dawo da wani yanayi na fata ga magoya baya, amma rashin daukar kofuna ya hana ya ci gaba. Daga bisani aka nada Erik ten Hag wanda ya lashe League Cup da FA Cup, amma shi ma ya fuskanci suka saboda rashin samun sakamako da ake bukata a wasu manyan fafatawa.
Ruben Amorim ya karbi jan ragamar United daga wadanda aka baiwa aikin na dindindin, shima daga baya aka sallame shi aka nada Michael Carrick, wanda ya fara da aikin rikon kwarya a watan Janairu kuma karo na biyu.
Sai dai United ta fuskanci koma baya a bana a karkashin Carrick, inda take ta ukun karshen teburi da cin wasa daya daga 10 da fara kakar nan.
Babbar matsalar ita ce kowanne daga cikin wadannan kociyoyi yana da kwarewa a koyar da wasan tamaula. Lokacin Van Gaal kungiyar tana wasa a hanyar da ya dora ta, Mourinho ya zo da wata dabarar, Solskjaer ya canza tsarin, Ten Hag ma ya zo da nasa salon, Amorin ya je da nashi kwazon da Carrick da nashi dabarun.
Wannan ya sa kungiyar ke ci gaba da sake gina kanta duk bayan wasu shekaru maimakon gina tushe guda daya da za a ci gaba a kai.
Matsala ta 2: Kashe kudi ba tare da la'akari da riba ba

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan tafiyar Ferguson, Manchester United ta kashe sama da biliyoyin fama-famai wajen siyan 'yan wasa.
An sayi Angel Di Maria da tsada amma bai dade ba ya tafi. Paul Pogba ya koma kungiyar a matakin wanda aka saya mafi tsada a tarihi a lokacin, amma bai cika abin da ake tsammani ba. Romelu Lukaku, Alexis Sanchez, Jadon Sancho, Antony da wasu da dama sun je Old Trafford kan dan karen tsada, amma ba a samu irin amfanin da ake fata ba.
A wasu lokuta koci ne ke son dan wasa, bayan shekara daya ko biyu a sallame shi, sai sabon koci ya zo baya bukatar wannan dan kwallon.
Hakan ya sa kungiyar ke asarar kudi tare da tara 'yan wasan da ba su dace da sabon tsarin da kocin da yake kan aiki zai yi amfani da su ba.
Matsala ta 3: Shugabanci da tsarin gudanarwa

Asalin hoton, Getty Images
Daya daga cikin manyan korafe-korafen magoya bayan United shi ne yadda kungiyar ta kasance tana tafiya ba tare da cikakken tsarin kwallon kafa ba.
A lokacin Ferguson, kocin ne ke kula da kusan komai. Amma bayan tafiyarsa, kungiyar ta kasa samar da tsarin zamani irin wanda Manchester City da Liverpool ko Arsenal suka kafa.
Manchester City tana da tsarin da zai iya aiki ko da an canza koci. Liverpool ta gina tsarinta bisa masu nazarin bayanai da masu kula da harkokin daukar 'yan wasa.
United kuwa ta dauki lokaci mai tsawo tana yanke hukunci ba tare da cikakken tsari ba. Hakan ya jawo matsaloli wajen daukar 'yan wasa, sabunta kwantiragi da kuma zabar koci.
Matsala ta 4: Tarihin da Ferguson ya kafa da matsin lambar magoya baya
Babban kalubalen duk wanda ya karbi Manchester United shi ne tarihin da Ferguson ya bari.
Magoya bayan kungiyar sun saba ganin ana lashe Premier League akai-akai. Sun saba ganin United tana fafatawa da manyan kungiyoyin Turai tana kuma yin fice.
Saboda haka duk wani koci da ya zo yana samun kansa cikin matsin lamba tun daga ranar farko. Idan sakamakon bai zo cikin sauri ba daga nan za a fara kiraye-kirayen a sallame shi.
Wannan matsin lamba ya sa wasu kociyoyi suna neman sakamakon gaggawa maimakon gina kungiya mai dorewa.
Matsala ta 5: Karuwar ingancin abokan hamayya

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da Ferguson yake mulki, Manchester United na daya daga cikin kungiyoyin da suka fi karfi a Ingila.
Amma yanzu yanayi ya canza.
Manchester City ta kafa kanta a kwallon Ingola da ba a taba gani ba karkashin tsarin zamani. Liverpool ta samu ci gaba karkashin Jurgen Klopp kafin sabon sauyi. Arsenal ta sake tasowa. Chelsea da Newcastle ma suna da karfin tattalin arziki da zai iya jawo manyan 'yan wasa.
Saboda haka ba kamar shekaru 20 da suka gabata ba ne inda United za ta iya mamaye gasar cikin sauki.
Yanzu kusan dukkan kungiyoyin saman tebur suna da tsari mai karfi, filayen atisaye na zamani da kuma manyan masu nazarin bayanai.
Me ya sa United ta bai wa Pochettino aikin?
United ta bai wa Mauricio Pochettino aikin horar da Manchester United kan kwantiragin shekara biyu da raba.
Tun a can baya a duk lokacin da kujerar kocin Manchester United ta shiga hadari, sunan Mauricio Pochettino yana daga cikin wadanda ake yawan ambata.
Yanzu dai an riga an bashi aikin, amma me ya sa United ta yi ta bibiyar Mauricio?
Dalilin farko shi ne kwarewarsa a Premier League. Ya yi aiki tare da Southampton da Tottenham, inda ya gina kungiyoyi masu karfi ba tare da samun kasafin kudin da manyan kungiyoyi ke da shi ba.
A Tottenham, ya dauki kungiyar daga matsayi na mai fafutukar shiga Turai zuwa kungiyar da ke neman kofin Premier League da Champions League.
A shekarar 2019 ya kai Tottenham wasan karshe a Champions League, abin da mutane da yawa suka dauka a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin horarwa a zamanin.
Kwarewa Wajen Gina Matasa
Pochettino ya shahara da bai wa matasa dama.
A karkashinsa ne Harry Kane ya zama daya daga cikin fitattun 'yan wasan duniya. Haka kuma ya taimaka wa Dele Alli, Son Heung-min da sauran matasa wajen bunkasa hazakarsu.
Wannan abu ne da ya dace da al'adar Manchester United wadda ta yi suna wajen renan matasa daga makarantar horas da 'yan wasan kungiyar.
Salon Wasa Da Magoya Baya Ke So
Pochettino yana amfani da salon kwallon kafa mai sauri, matsa wa abokan hamayya lamba da kuma kai hare-hare.
Irin wannan salon wasa ne magoya bayan United ke son gani saboda yana tuna musu wasu daga cikin abubuwan da suka saba gani a zamanin Ferguson.
Shin Pochettino Ne Mafita?
Duk da kyawawan siffofin da Pochettino yake da su a fannin horar da tamaula, masana suna gargadin cewa matsalar Manchester United ba ta tsaya kan koci kadai ba.
Idan kungiyar ba ta gyara tsarin daukar 'yan wasa, tsarin gudanarwa da kuma ba wa koci cikakken lokaci ba, to ko wanene aka dauka zai iya fuskantar irin matsalolin da wadanda suka gabace shi suka fuskanta.
Abin da shekaru fiye da goma bayan ritayar Sir Alex Ferguson suka nuna shi ne cewa Manchester United na bukatar cikakken sauyi a tsarin gudanarwa fiye da sauya mutum daya a kujerar koci.
Mauricio Pochettino zai yi iya kokarinsa, domin ya fito da kansa, amma nasarar da magoya bayan kungiyar ke fata za ta dogara ne a kan yadda dukkan bangarorin kungiyar za su hada kai wajen sake gina daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa ta duniya.



























